04/02/2024
KO MAIGIRMA GWAMNA DA GWAMNATI SUN SAN HALIN DA KATSINA UNITED TAKE CIKI.???
A kwanakin baya naga wata kungiya Mai rajin kare muradun Maigirma gwamna da gwamnati kan harkokin wasanni sunyi Wani rubutu Mai muhimmanci akan kungiyar kwallon kafa ta katsina united, saigashi ana gab da komawa zagaye na biyu na gasar premier league ta Nigeria shuwagabannin riko na wannan kungiya sunata daukar wasu munanan matakai na durkusar da wannan kungiya kamar haka.
À. Sanin kowane cewa shuwagabannin da aka dakatar sunyi namijin kokari wurin dauko yanwasa masu kwarewa Kuma sun biya kudin takardarsu 50% clearance. Mafi yawa daga cikinsu sunada deal kwantaragi da kasashen waje a inda gwamnati zata samu kudaden shiga masu yawa ta dalilin wannan kwantaragi. Abu Mafi muni sai gaya bisa sahihin labari shugaban riko yazagaye ta bayan fage Bada sanin gwamnatiba Yana sayar da wa'annan Yan wasa ga wasu kungiyoyi a Nan cikin kasa da wajen kasar nan kamar haka.
1. Mikel Ibe Yasayar dashi ga Enyimba int'l Aba
2. Lawrence Edward Yasayar dashi ga plateau United
3. Uzor chinedu Yasayar dashi ga Heartland F.c
4. Daniel Akambek Yasayar dashi ga Remo stars
5. Ibrahim yahaya Yasayar dashi ga kano pillars
6. Lukman Bello yanzu haka Yana kasar Tunisia yasanya hannu da, Birzerin C.A Tunisia
7. Anas Hassan yanada yarjejeniya da Wani club a Egypt Amma ansayar dashi anbada release nashi.
Duk wa'annan jerin Yan wasa mallakin gwamnati jihane sunada two years contract da KATSINA UNITED Kuma Babu Wanda ya shekara Daya a katsina an saidasu. Kuma Babu Wanda yasan nawa aka sayar dasu sai caretaker chairman ne kadai zaiyi wannan bayani.
Don sanin riba akaci ko anfadi?
Wannan na nuna tabbas management da aka dakatar sun shirya ciyar da wannan kungiya gaba sai dai aka samu rashin fahinma dasu. Don sun dauko manyan Yan wasa Kuma sun biyasu sun zama mallakin KATSINA UNITED.
A Wani sahihin labari daga NFF da NPFL na cewa, caretaker committee chairman yaje Abuja yanason abashi dama yasamu access da D.M.S code number na KATSINA UNITED abin tambaya me zaiyi dashi ? Kuma zamuso maigirma shugaban rikon kwarya yayi bayani akan kudin TV Right da kamfanin star time sukaba kungiyoyi naira million GOMA 10m.
B. Abisa sahihin bincike Kuma Babu Wani Dan wasa na fita kunya da aka dauko don maye wannan guraben da aka rasa gaya har ana gab da kulle damar yima sabbin Yan wasa register.
C. Anya wannan ba Wani mumunan tanadi bane wannan kwamitin riko yake shiryama wa'anda za'aba wannan club dinba? Ganin haka yakamata gwamnati ta duba wannan lamarin Kuma duk Wanda zai hau wannan shugabanci yasani anshirya mashi cikakken makircin yanada kalubale da Allah ne kadai zai iya fiddashi.
Shawara tarage ga mai shiga rijiya don wannan babban kalubalene ga jihar mu Mai albarka da maigirma gwamna maison cigaban jiha da matasa da wasanni gaba Daya.
nagode, naku Maison cigaban jihar katsina Dan gwagwarmaya.
Daga Comrd. Muhammad Isah Funtua.
0700 399 4680