KST

KST Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from KST, News & Media Website, .

DOMIN SAMUN ARZIKI ASIRI-RUFE: KABI ALLAH, KABI IYAYE, SANNAN KAYI NESA-DA-GIDA INDA KATASO AKAFI SANINKARubutawa: Auwal...
21/07/2025

DOMIN SAMUN ARZIKI ASIRI-RUFE: KABI ALLAH, KABI IYAYE, SANNAN KAYI NESA-DA-GIDA INDA KATASO AKAFI SANINKA

Rubutawa: Auwalu El-Yobawi | 14-07-2025

Da so samu ne, babu abu mafi dadi kamar mutum ya samu arziki da wadata da rufin asiri a garinsu, cikin 'yan uwa da dangi kamar yadda Manzo Allah tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya fada cikin wani ingantaccen Hadisi. Amma salon tunani da gurbacewar zamani da dabi'u irin na mutanen da muke rayuwa a cikinsu, sun nuna gwamma mutum yasamu arziki da wadata daga can nesa, saidai aganshi da abinsa.

Tunda dai, ko cikin bayanin da fiyayyen halitta yayi, ba wajabtawa yayi cewar dole lallai ilalla sai kowa yayi arziki a garinsu ba. Jawabi ne da yake nuni da Da-So-Samu ne kasancewar Allah da Manzanninsa sunfi kowa sanin ko su waye mu.
Babban abinda akeso dakai dai shine aduk inda kake kaji tsoron mahaliccinka sannan kakare mutuncin gidanku da iyayenka. Ka tsaya cak a inda s**a doraka ta fuskar kyakkyawar tarbiyya da sanin yakamata.
Kada ka saba dokar Allah ko zubda mutuncin iyayenka saboda baka kusa dasu. Sannan kuma kada ka manta da hakkokinsu akanka, duk rintsi dun daula.

Ka lura da kyau: Mutanenmu sunfi shiri da kai da jawoka ajiki idan ka kasance a irin halin da suke na takauci. Idan ma ba talauci cancan ba dai, to ya zamana ba kafisu da komi ba. Yawwwwwwa !

Ka lura sosai: Ko abokanka da kuka taso kuna wasan-kasa tare, akasarinsu, da zarar ka samu wata daukaka ko fifiko akansu ta fannin arziki da wadata, daga sannan labari zai soma sauyawa; kiyayya da gaba da kananan maganganu su soma bayyana. Daga sadda daukaka da arziki s**a soma samunka, zakaji abubuwa iri-iri, zakaga abubuwa iri-iri musamman daga wajen wa'yanda su yakamata su baka kariya. Wasu ma daga cikin gidan da kafito.

Da farko, zasuke tayaka murna da haba-haba, namu ya samu. Can tsakiya, zasu soma gasa da kai. Daga karshe, zasu soma artabu da tataburza da kai. Wani abinda zai furta akanka, ba zaka yarda shine ya furta ba.
Wasu har zasu kaiga yimaka sihiri, ko tsubbu, ko tsafi domin ka ci baya ko kuma akalla kada ka zarta su.
Hakan bai cika faruwa ba a inda kayi arziki ba'a sanka ba, inda ba'a nan kataso ba. Inda ba'a nan 'yan uwa da dangi suke ba.

Bayan haka kuma, akwai wasu dalilai da suke kawo tsaiko ko su dakatar da cigaban wanda yasoma tasowa da arziki idan yana tareda wa'yanda aka haifeshi yataso a cikinsu, da s**a hada da:
1. Gorin asali;
2. Kunyar yin wata sana'ar;
3. Daukewar hankali irin na Abokai;
4. Dogaron 'yan uwa da dangi akanka kullum-kullum;
5. Cinikayyar sani-da-sabo;
6. Fakewa da Addini ko Al'ada a cuce ka, kayi magana ayi maka gori ko a kafirta ka;
7. Taurin bashi ko hanawa daga wa'yanda babu yadda ka iya dasu;
8. Kyautar dole;
9. Sakin jiki;
10. Barin halal domin kunya; da
11. Fama da cin dunduniya daga wa'yanda s**a san sadda kayi talauci yanzu kuma kasoma arziki.

Sannan, kasake lura dakyau: Babu wani dalili ko hujja sai a hanaka hayar wajen sana'a idan alal misali inda kake yayi kadan kanason kakara fafada kasuwarka amma a baiwa bakon da ba'a san daga ina yake ba. Ko aki sayar maka da wani muhimmin abinda kakeson kasaya kudi-hannu amma a sayarwa wa bako kasa da yadda kasaya ko ayi masa Alfarma ya biya da kadan-kadan. Sai a hanaka aure a inda kataso ko a hana yaranka amma a aura wa bako.
Ko kuma uwa-uba a soma zargin ai arzikin naka ma na TSAFI ne ko kuma DODO gareka a cikin gidanka ko gonarka ko wajen sana'arka.
Wasu haka siddan zasu dena hulda dakai, su dena amsa gaisuwarka ko sallamarka, ko kuma su amsa ciki-ciki; laifinka kawai me yasa kafisu arziki da rufin asiri?
Duk irin wa'yannan abubuwan ba zaka fuskancesu a inda ba'a san asalinka ba.

To yadda ake fifita bako a garinku hannu bibbiyu ake kakkare dukiyarsa da martabarsa, haka kaima za'ayi maka a inda ba'a sanka ba. Shima a wulakanta shi a garinsu. Haka mutanenmu suke !

Wanda kuke katanga daya dashi, sai yaki sayen kaya ko ciniki a wajenka yatafi can nesa inda baikai arahar naka ba ko inganci ya saya kudi-hannu; idan kaga yazo wajenka, to bashi yakeson ka bashi. Yasan hakan wancan bakon ba zai bashi ba.

Idan haya kake a shagon wanda yasanka, da zarar kafara samun daukaka maimakon yaji dadi dakai aka raya wajen, a'a. Ko dai yayi maka kora-da-hali tafuskar kara maka kudin-haya ko kuma yabaka "Notis" yace zaiyi gyara ko kuma 'ya'yansa sun girma zasu soma sana'a a wajen. Kana barin wajen, kwanaki kadan zakaga shi da yaran nasa sun zuba sak irin kayan da kake sayarwa acikin shagon.

Akwai hikimomi masu yawa tattare da hakan da ba zasu kirgu ba. Cikakken gamsasshen bayani yana tafe zuwa anjima In Sha Allah.

Amma kafin anjima din, mu lura da wa'yannan ababe ⬇️

👉 Masu arzikin garinku ko a inda kataso, asalinsu 'yan garine ko baki ne?

👉 Tsakanin 'yan asalin garinku da s**a fita da wa'yanda suke zaune s**aki fita suwa s**afi rufin asiri idan wani taro ko biki yasa aka hadu?

👉 Idan katashi neman bashi daga wajen dan kasuwa, wajen wanda kasani kake zuwa ko bako?

👉 Kudi ko bashin wa akafi cinyewa tsakanin Dangari da Bako?

👉 Idan ka bibiyi tarihi, shahararrun attajirai, Annabawa da Salihan bayi, ya s**a kare da mutanen asalin garuruwansu?
A ina akafi karbarsu s**afi shahara?

👉 Ko ka lura hatta yaran da ake kawowa almajiranci ake yiwa kallon banza daga karshe su suke kudancewa a garuruwan da aka kawosu su danne 'yanbokon gari, da wa'yanda aka kawosu almajirancin aka idanunsu?
Wasu ma sunyi musu yaran gida ko almajiran gida?

👉 Ko kalura da yadda dan Nijar zai tsallako yakafa rumfar shayi yagina gida a unguwa, asalin wa'yanda yatarar s**arbi haya daga hannunsa?

👉 Ka taba tambayar me yasa Inyamuri ko Bayerabe zai baro Kudu yazo garinku ya bude shagon Kemis, ko Fakanaizae, ko kayan gwangwan, ko Sifiyan kayan ababen hawa cikin kankanin lokaci ya shahara agaban matasan garin masu zaginsa suna ce dashi "Arne"?

Da sauransu, da sauransu.

Masu hikimar magana sunyi gaskiya da suke ce ⬇️

A. An tambayi "Ido" aka ce "Wa ka raina?"
Yace, "Wanda nake gani kullum."

B. Naka shi yake ba da kai;

C. Makashinka yana tare dakai !

Duk wanda bai fahimci wannan ba, ya cancanci a taya shi jaje.

Shirye-shiryen Ƙaddamar Da Sabuwar Tafiya Ranar Lahadi dai dai da 13/7/2025 A Katsina Ya Fara Kankama, Inda Aka Fara Kaf...
12/07/2025

Shirye-shiryen Ƙaddamar Da Sabuwar Tafiya Ranar Lahadi dai dai da 13/7/2025 A Katsina Ya Fara Kankama, Inda Aka Fara Kafa Manyan Alluna masu dauke da Jiga jigan hadaka. Na kasa da Kuma na jaha.

18/06/2025
Kafin ka ɗora wa ƙaddara,Kafin ka zargi kowa kan damuwarka,Ka fara duba aiyukanka na jiya, Ka fara duba aiyukanka na sat...
13/12/2024

Kafin ka ɗora wa ƙaddara,
Kafin ka zargi kowa kan damuwarka,

Ka fara duba aiyukanka na jiya,
Ka fara duba aiyukanka na satin da ya wuce,
Ka fara duba aiyukanka na wancan wata,
Waccar shekara da taa wuce,
Shekaru 2, 3, 4, 5... da s**a wuce.

Duk suna da alaƙa da halin da ka tsinci kanka a yau.

Cewa ƙaddara ce,
A'a, laifin wasu mutane ne,

Duk kanka kake nemawa uzuri,
Na kasalarka,
Wawan zaɓinka,
Biye wa son zuciyarka.

Yanzu kuma kake girbe shukar da ka yi.

Sunnar rayuwa ce,
Ba Musulmi ko waninsa,
Ba mutum kirki, ko na banza,
Ba babba ko yaro,
Ba mace ko namiji.

Duk abin da kake aikatawa a yau, shi ka tarar gobe, ko shekaru masu zuwa, har a lahira.

Kana da damar sauƙa a wani layi na kuskure don ka gyara gobenka, ka RAGEWA kanka ƙalubale da matsaloli. Ubangiji ﷻ na taimakon wanda ya yi kataɓus ne, ba malalaci ko mai bin son zuciya ba.

07/10/2024

اللهم صل على سيدنا محمد الفاتح لما أغلق والخاتم لما سبق ناصر الحق بالحق والهادي إلى صراطك المستقيم وعلى آله حق قدره ومقداره العظيم.

Amazing picture
29/09/2022

Amazing picture

29/09/2022

KA SOMA DAN UWANKA ABUN DA KASO MA KANKA

Address


Telephone

07037828247

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KST posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share