Katsina Newsline

  • Home
  • Katsina Newsline

Katsina Newsline Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Katsina Newsline, Media/News Company, Yahaya Madawaki Way Opposite Albustan Hotel, .

Katsina Newsline — Jarida daya tamkar dubu.
• Tsantsar gaskiya a kowanne rahoto
• Labarai da dumi-dumi cikin gaggawa
• Adalci da sahihanci wajen yada Labari daga Ko'ina a Fadin Duniya.
- Domin tallata Hajarku:
📞 Kira/SMS/WhatsApp: 0708 736 6220

YANZU YANZU Yadda ƴar marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari, Zahra Buhari ta wallafa sabbin hotunanta a yau.Wane fata za ...
24/08/2026

YANZU YANZU
Yadda ƴar marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari, Zahra Buhari ta wallafa sabbin hotunanta a yau.

Wane fata za ku mata ?

Da Dumi-Dumi: Ndume Ya Buƙaci ’Yan Adawa Su Yi Wa Tinubu Hukunci Bisa Ayyukansa, Ba Takardun Karatunsa BaSanata Ali Ndum...
24/08/2026

Da Dumi-Dumi: Ndume Ya Buƙaci ’Yan Adawa Su Yi Wa Tinubu Hukunci Bisa Ayyukansa, Ba Takardun Karatunsa Ba

Sanata Ali Ndume ya buƙaci jam’iyyun adawa da su mayar da hankali kan ayyuka, manufofi da nasarorin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, maimakon takardun karatunsa, yayin da zaɓen shekarar 2027 ke ƙaratowa.

Ndume ya jaddada cewa ya kamata ’yan siyasa su tattauna abin da gwamnatin Tinubu ta cimma da kuma manufofinta, domin bai wa ’yan Najeriya damar yanke hukunci bisa abin da aka aikata.

Karanta cikakken labarin a sashin sharhi.

Ya Allah, a wannan lokacin da rauni ya mamaye jikinsa, Ka zuba masa lafiyar da babu ciwo a cikinta. Ka sauƙaƙa masa, Ka ...
24/08/2026

Ya Allah, a wannan lokacin da rauni ya mamaye jikinsa, Ka zuba masa lafiyar da babu ciwo a cikinta. Ka sauƙaƙa masa, Ka ɗaga masa wannan jarrabawa, Ka mayar da hawaye farin ciki, Ka kuma dawo da shi cikin iyalansa cikin cikakkiyar lafiya. 🤲🏻

GODIYA TA MUSAMMAN ZUWA GA SANATA MUNTARI MUHAMMAD DANDUTSEDaga: Hon. Ibrahim Babangida Ibrahim Mailayu FuntuaIna mika s...
18/08/2026

GODIYA TA MUSAMMAN ZUWA GA SANATA MUNTARI MUHAMMAD DANDUTSE

Daga: Hon. Ibrahim Babangida Ibrahim Mailayu Funtua

Ina mika saƙon godiya da matuƙar farin ciki da jin daɗi ga mai girma Sanata Muntari Muhammad Dandutse, bisa gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen taya mu murnar haihuwar jaririnmu da aka yi wa suna Yau Talata 18th August 2026, Wanda aka radawa Suna da Aliyu Babangida Ibrahim Mailayu Funtua (Haidar)

Mai girma Sanata Muntari Muhammad Dandutse ya nuna ƙauna, kulawa da kishin zumunci ta hanyar bayar da gudunmawar kuɗi Naira 400,000, tare da buhunan shinkafa guda uku (3) da kuma katunan taliya guda biyar (5) domin taya mu murnar wannan babbar ni’ima da Allah Maɗaukakin Sarki Ya azurta mu da ita.

Hakika, wannan kyakkyawan aiki ba ƙaramin abin yabawa ba ne. Ya nuna irin girman zuciya, karamci, dattako da kishin zumunci da mai girma Sanata Muntari Muhammad Dandutse yake da shi. Irin wannan taimako yana ƙara ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin al’umma, tare da nuna cewa farin cikin ɗan’uwa ko aboki shi ne farin cikin kowa.

Muna matuƙar godiya da wannan kyakkyawar niyya da gagarumar gudunmawa da ka bayar. Ba za mu manta da wannan karamci da ka nuna mana ba, kuma muna addu’ar Allah Ya saka maka da mafificin alheri, Ya ƙara maka lafiya, arziki, matsayi da ɗaukaka, Ya albarkaci dukiyarka da ayyukanka, Ya kuma sa wannan gudunmawa ta zama sadaka mai ci gaba da samun lada a gare ka.

A madadin kaina da iyalina, ina sake miƙa godiya ta musamman ga mai girma Sanata Muntari Muhammad Dandutse bisa wannan karamci da kulawa.

Allah Ya saka da mafificin alheri, Ya ƙara zumunci da ƙauna tsakaninmu. Amin.

Sa hannu:
Hon. Ibrahim Babangida Ibrahim Mailayu Funtua S.A Information and Public Enlightenment Funtua Local Government Council.

Tsohon gwamnan Katsina Masari ya ce, mai munafunci a zuciyarsa ne kadai zai iya buda baki ya ce Tinubu da Dikko Radda ba...
17/08/2026

Tsohon gwamnan Katsina Masari ya ce, mai munafunci a zuciyarsa ne kadai zai iya buda baki ya ce Tinubu da Dikko Radda ba wani ci gaban da s**a kawo

Me zakuce

Allah ya Ji kansu da Rahama🙏Allah ya basu Gidan Aljanna🙏🏻Allah ya yafe musu kuskurensu🙏
14/08/2026

Allah ya Ji kansu da Rahama🙏
Allah ya basu Gidan Aljanna🙏🏻
Allah ya yafe musu kuskurensu🙏

Atiku ya maka Tinubu kotu kan takardar NYSC, yana son a hana shi takara a 2027Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma d...
14/08/2026

Atiku ya maka Tinubu kotu kan takardar NYSC, yana son a hana shi takara a 2027

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin kalubalantar cancantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu shiga zaben shugaban kasa na 2027.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mataimakin na musamman ga Atiku kan kafafen yada labarai Phrank Shaibu.

A karar, Atiku da ADC sun yi zargin cewa Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC da takardar shaidar kammala bautar kasa ta NYSC mai dauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle”, maimakon “Bola Ahmed Tinubu”. Masu karar suna neman kotu ta tantance sahihancin takardar tare da umartar INEC ta gabatar da bayanan Form CF001 da Tinubu ya mika mata dangane da zabukan 2023 da 2027. Sun kafa hujjarsu ne kan sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, wanda ya tanadi rashin cancantar mutumin da aka tabbatar ya gabatar da takardar shaida ta bogi ga INEC.

Atiku Abubakar ya ce manufar karar ita ce a bai wa kotu damar tantance hujjojin da aka gabatar, ba wai yanke hukunci ta kafafen sada zumunta ba. Ya kuma bukaci INEC ta nuna rashin son kai ta hanyar gabatar da takardun da ake bukata a gaban kotu. Daga cikin bukatun Atiku da ADC akwai neman kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaben shugaban kasa na 2027 idan aka tabbatar da zarge-zargen da s**a gabatar, yana mai jaddada cewa babu wani dan Nijeriya da ya fi karfin Kundin Tsarin Mulki.

Bandir ɗaya zai maka full tank din mota a shekarar 2002, idan babur gareka takarda shida kawai za ka bayar a cika maka ɗ...
14/08/2026

Bandir ɗaya zai maka full tank din mota a shekarar 2002, idan babur gareka takarda shida kawai za ka bayar a cika maka ɗan Jincheng ɗinka. Hakazalika idan ka fasa bandir ɗaya za ka ɗauki katon buhun masara da carton ɗin taliya har ka samu canjin 20 na hawa mashin.

14/08/2026

Duk wani Dan Apc na katsina kodan Gwagwarmaya dan wahala ne.

Inji Asiya Smaida

Zaben Osun: PDP Tsagin Turaki Ta Goyi Bayan AdelekeBangaren ya umurci magoya bayansa su kaɗa kuri’a tare da kare ƙuri’un...
14/08/2026

Zaben Osun: PDP Tsagin Turaki Ta Goyi Bayan Adeleke

Bangaren ya umurci magoya bayansa su kaɗa kuri’a tare da kare ƙuri’unsu a zaɓen ranar Asabar

Bangaren jam’iyyar PDP da tsohon Ministan Sufuri, Tanimu Turaki, ke jagoranta ya bayyana goyon bayansa ga Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, wanda ke neman sake zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar Accord a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Kwamitin Rikon Kwarya na PDP na Ƙasa, Ini Ememobong, ne ya bayyana matakin a wata sanarwa, yana mai cewa an yanke shawarar ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki. Wannan na zuwa ne bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Adebayo Adedamola a matsayin ɗan takarar bangaren Turaki, tare da umartar INEC ta saka tambarin PDP a takardun zaɓe.

Sai dai Ememobong ya ce jinkirin da aka samu wajen kammala batun takarar ya hana ɗan takarar PDP gudanar da yaƙin neman zaɓe yadda ya kamata. Saboda haka, bangaren ya umarci mambobinsa su goyi bayan Adeleke, su kaɗa kuri’a tare da kare ƙuri’unsu har zuwa lokacin ƙirga su.

Bangaren Turaki ya kuma yi kira ga ’yan takara da magoya bayansu da su guji tashin hankali, yana mai cewa nasarar zaɓe ya kamata ta kasance sakamakon zaɓin jama’a cikin ’yanci da adalci.

Address

Yahaya Madawaki Way Opposite Albustan Hotel

Telephone

+2348065223687

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina Newsline posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share