01/09/2024
YAKI DA MATSALAR TSARO A DUNIYAR CYBER SECURITY (1)
Datti Assalafiy ✍️
Mutanen mu da basu san tsaro ba dauka suke cewa karfin Soji, bakin bindiga, tankokin yaki, jiragen yaki, labarin an kashe dubban 'yan ta'adda shine tsaro, sam wannan ba shine tsaro ba, Intelligence da Cyber Security shine tsaro jama'a
Ku zo na shiga daku cikin duniyar cyber security, wannan hoton CDR ne wato "Call Details Record" ko "Call Data Record" nake yin analysis akan wani mutum da aka masa kisan gilla aka gudu da dukiyarsa, duk wani bincike na bin diddigin motsin kowani irin mutum a duniya ya kare anan, sai dai matsalar da zaka hadu da jami'an tsaro da suke binciken laifuka mutum 100 da kyar ka samu guda 1 da ya iya CDR analysis a cikinsu
Anan wajen ina iya kallon mutum har cikin gidansa, har inda yake kwantawa a cikin dakinsa ina gani, idan yana falo ko yana daki zan banbance, b***e kuma ace wanda yake zaune a cikin dazuka, kuma ba siddabaru bane, codinate na latitude da longitude yake nuna min a google map a cikin CDR
Anan CDR ina iya ganin duk abokan mu'amalar mutum, har ma nayi KYC akan wata software app na kalli fuskokinsu, duk wanda ya taba yin waya da wani ko ya kai shekara biyu da wanda s**a taba haduwa da inda suke haduwa, da inda mutum yake wuni da safe, rana da yammaci duk zan iya ganewa na je har daidai gurin ba tare da an samu kuskure ba
Bincike ba wai kawai ace ga phone number na suspect ayi tracking a samu soft target da location din su ba, wannan tsohon yayi ne, bari na takaita muku zance idan na samu layin wayar mutum na masa CDR abinda ke cikin hanjin cikinsa ne kawai ba zan iya gani ba
Matarka tana cin amanarka?, budurwanka tana cin amanarka?, suna zuwa hotel?, wani hotel suke zuwa tare da waye?, na rantse da Allah duk ina iya ganowa anan ba tare da an samu kuskure ba
Idan ina son sanin mutum da halayensa ba sai na tambayi wani ba, anan zan gano komai, kuma yahudawa ne s**a koya min wannan analysis din ta dalilin wani Maigidana, kudin aljihuna na biya na zauna a aji aka koya min aka bani shahada na zama certified CDR analyst
Kamar yadda zaku ji Professor Isa Ali Pantami ya fada, yace data base kawai za'a gina wa hukumomin tsaro su dinga bin diddigin 'yan ta'adda, ina kyautata zaton cewa IMSI Catcher device da take fitar da CDR yake nufi a sayo a ginawa cibiyoyin bincike, kudin da za'a sayo na'urar da training duk ba zai wuce Naira Miliyan dari biyar ba, amma abin takaici duk jihohin Arewa bamu da wannan data base din ko guda daya
Na taba zuwa bincike wata jiha a inda suke fama da matsalar ta'adda, muna tare da jami'an tsaron da suke bincike wani babban case, duk cikinsu babu wanda ya san CDR ma b***e a samu wanda ya iya analysis na CDR din, to wannan babban kalubale ne wa Gwamnati, kuma babban cikas ne a harkan binciken manyan laifuka
Ni Datti Assalafiy Allah Ya sani zuciyata a cikin kuna da takaici take saboda wahalan da 'yan Arewa muke sha a hannun 'yan ta'adda, kuma ga hanyar da za'a samu mafita amma wadanda suke da iko sun ki yin abinda ya dace, sun mayar da tsaron Arewa ya koma harka na siyasa da neman kudi
A rubutu na gaba zan kawo muku yadda za'a yi amfani da wannan tsari na bincike a kawar da matsalar kidnapping da ya addabi Arewa, ku biyoni bashin rubutun zuwa dare idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya
Yaa Allah Ka mana maganin wadanda suke da hannu a cin amanar tsaron Arewa