02/08/2026
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Allah Ya Yi Wa Fitaccen Mawaki Kosan Waka Rasuwa
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar fitaccen mawakin Kosan Waka Abokinsa kuma amininsa, Hassan Danja, ne ya tabbatar wa DCL Hausa da labarin rasuwar tasa Allah Ya gafarta masa, Ya yalwata masa rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya ba iyalansa, abokansa da masoya juriyar wannan babban rashi. Amin. Muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalansa da masoya. Allah Ya jikansa da rahama. Amin.