02/03/2026
Yadda jigo a tafiyar matasa ya canza sheƙa zuwa jam’iyyar adawa ta ADC a jihar Katsina
Wani jigo a cikin tafiyar matasa a jihar Katsina ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.
Usman Alasan Ruwan Godiya wanda ya kasance mai magana da yawun tafiyar matasa a jihar Katsina, ya wallafa a shafinsa na Facebook katin mambarship na jam’iyyar ADC, tare da bayyana wasu dalilai da s**a sa ya bar tafiyar matasa ya koma jam’iyyar haɗakar adawa ta ADC a jihar.
Tsohon mai magana da yawun tafiyar matasan ya tabbatar da sauyin ne ta hanyar wallafar bayanin nasa, inda ya ce matakin ya zo ne bayan nazari da tunani kan makomar siyasa da burinsa na ci gaba da hidimtawa al’ummar ƙaramar hukumar faskari da jahar katsina baki daya