Katsina Media Online

Katsina Media Online Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Katsina Media Online, Media/News Company, Yahaya Madawaki Way Katsina, Katsina.

15/05/2024

Assalamu Alaikum 👋

31/03/2024
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ɗauki Malaman Makaranta 7,325Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko ...
12/09/2023

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ɗauki Malaman Makaranta 7,325

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Raɗda, ta ɗauki malaman makaranta guda dubu bakwai da dari uku da ashirin da biyar (7,325) domin haɓaka harkar ilimi a jihar.

Malaman makaranta da aka ɗauka, sun fito ne daga cikin tsarin S-power, da kuma masu aikin kyauta wanda ake kira "Valunteer".

Kafin daukar Malaman makarantar an yi musu jarabawar gwaji, inda aka fitar da wadanda s**a samu nasarar samun makin da ake buƙata.

Shugaban kwamitin daukar ma'aikatan ne, Dr Sabiru Dahiru ya fitar da sanarwar ɗaukar ma'aikatan. Inda ya ce Gwamnan jihar Malam Dikko Umar Raɗda ya bada umarnin a basu horo na musamman, sannan sai a basu takardar k**a aiki, tare da tura kowa inda ya fito domin bayar da gudummawa.

Daga Jamilu Sama'ila Dandana

MUTUNA DA MTUMIN DAYA KARE MARTABAR ANNABI S.A.W A GABAN MAKIYANSA.Shine Shugaban Qasar Da Yaje Majalisar ‘Dinkin Duniya...
04/08/2023

MUTUNA DA MTUMIN DAYA KARE MARTABAR ANNABI S.A.W A GABAN MAKIYANSA.

Shine Shugaban Qasar Da Yaje Majalisar ‘Dinkin Duniya Agaban Yahudawa Yabaiwa Annabi (S.A.W) Kariya.

Shine Shugaban Qasa Na Farko Acikin Shugabannin Qasar Egypt Da Yaja Sallah A Masallacin Annabi (S.A.W) Madina.

Shine Shugaban Qasar Da Ya Bud’ewa Falatsinawa Iyakar Qasar Egypt Domin Zalincin Da Yahudawa Keyi Musu.

Shine Shugaban Qasar Da A Lokacinsa Malamin Addini, Hafizin Qur’ani, Kuma Qwararran Engr A Fannin Boko.

Shine Shugaban Qasar Da Yafito Da Malamai Da Duk Wanda Aka ‘Daure Bisa Zalinci A Mulkin Husnul Mubarak.

Shine Yayi Qoqarin Tsarin Qasar Egypt Ya Tafi Daidai Da Tsarin Musulunci.

Shine Wanda Larabawa Masu Qawance Da America S**a Had’a Baki Da Isra’el Wajen Kifar Da Gwamnatinsa.

Shine Shugaban Qasar Da Yayi Shahada A Prison A Hannun Maqiya Addinin Allah,

Shine Shugaban Qasar Da Aka Hana Y’an Uwansa, Da Masoyansa Su Sallaci Gawarsa.

An Haifeshi 20/8/1951,

Yazama Shugaban Qasa 30/6/2012,

Anyi Masa Juyin Mulki 3/7/2013,

Ya Rasu A Prison 17/6/2019.

Shaheed Mursi Rahimahullah😭💚

Tarihin Musulunci Na Wannan Qarnin Bazai Manta Da Kaiba Har Abada.✌🏻

Allah Ya Jadada Rahama Gareshi Yasa Aljarnar Firdausi ce Makomarsa.

Zafafan Hotunan Sarauníyar Kyawawan Matan Nájeriya A'isha Garko, waccé tafì kowacé ƴa Macé Kyau a faɗín N@eriya. Bíncíke...
25/09/2022

Zafafan Hotunan Sarauníyar Kyawawan Matan Nájeriya A'isha Garko, waccé tafì kowacé ƴa Macé Kyau a faɗín N@eriya. Bíncíke ya núna akwaí yíwar ta saké samún Matsayín a shékara maí zuwa domìn har yanzu ba'a samu wacce tafí ta Kyaú ba.

Menene Ra'ayín Ku?

"A gwamnatinmu zamu buɗe bankunan abinci a ko wace jiha da ƙaramar hukuma don baiwa talakawa abinci sau uku kyauta, zamu...
20/09/2022

"A gwamnatinmu zamu buɗe bankunan abinci a ko wace jiha da ƙaramar hukuma don baiwa talakawa abinci sau uku kyauta, zamu ƙulla yarjejeniya da kamfanin Pop Cola saboda kowa ya more rayuwa."
~A cewar Kwamaret Ruma

Sarauniya Elizabeth ta rasu!Masarautar Birtaniya ta sanar da rasuwar Sarauniya Elizabeth. Ta Rasu tana da shekara 96; ta...
08/09/2022

Sarauniya Elizabeth ta rasu!

Masarautar Birtaniya ta sanar da rasuwar Sarauniya Elizabeth. Ta Rasu tana da shekara 96; ta kuma kwashe shekaru 70 kan gadon sarauta.

Dalilin da ya sa al'ummar jihar Katsina za su maida biki don zabar Tinubu a 2023 - Inji Gwamna MasariDaga, Ibrahim M Baw...
27/08/2022

Dalilin da ya sa al'ummar jihar Katsina za su maida biki don zabar Tinubu a 2023 - Inji Gwamna Masari

Daga, Ibrahim M Bawa

Gwamnan jihar Katsina Rt Hon Aminu Bello Masari ya bayyana cewa al'ummar jihar Katsina ba butulai bane, don haka za su maida biki domin zabar Ahmed Bola Tunibu a matsayin shugaban kasar Nijeriya a zaɓe mai zuwa na 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin na TVC News da Katsina Media Post News ta kalli firar.

A firar Masari bayan da ɗan jaridar ya tambaye shi ko al'ummar arewacin Nijeriya za su karbi Tinubu a zaben 2023 kuwa sai Masari ya kada baki ya ce " Ai sun riga ma sun karbe shi, da farko dai sunan Tinubu ba sabon suna bane a harkar siyasar Nijeriya, kuma mu al'ummar jihar Katsina mun san irin halacci da rawar da Tinubu ya taka wajen lashe zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, da tazarcen da ya yi a 2019, don haka mu al'ummar jihar Katsina ba butulai bane" Inji Gwamna Masari

Ku Kasance da Hazikin Matashi Haifaffen Cikin Garin Katsina Hamza Abdulhadi Yantaba A Gidan Radion Vision FM A Kan Tatta...
23/08/2022

Ku Kasance da Hazikin Matashi Haifaffen Cikin Garin Katsina Hamza Abdulhadi Yantaba A Gidan Radion Vision FM A Kan Tattaunawa da Zasuyi kan Manya Manyan Matsalolin dake damun Katsina Local Government Tare da Hanyoyin da Zaa bi A Magance Matsalolin.

A Karkashin Gidauniyar dake Tallafawa Mabukata Wato AFF FAMILY.

Ku Kasance dashi.
Ranar Talata Da Karfe 10:30 na Dare.

Ku Kasance da Matashi Hamza Abdulhadi Yantaba A Gidan Radion Vision FM A Kan Tattaunawa da Zasuyi kan Manya Manyan Matsa...
17/08/2022

Ku Kasance da Matashi Hamza Abdulhadi Yantaba A Gidan Radion Vision FM A Kan Tattaunawa da Zasuyi kan Manya Manyan Matsalolin dake damun Katsina Local Government Tare da Hanyoyin da Zaa bi A Magance Matsalolin.

A Karkashin Gidauniyar dake Tallafawa Mabukata Wato AFF FAMILY.

Ku Kasance dashi.
Ranar Talata Da Karfe 9:00 na Dare.

"Shekararsa 15, ya cewa Mahaifiyarsa idan ya kai shekara 18 wace kyauta zata yi masa? Ta ce, Ɗana ai da sauran lokaci ma...
28/07/2022

"Shekararsa 15, ya cewa Mahaifiyarsa idan ya kai shekara 18 wace kyauta zata yi masa? Ta ce, Ɗana ai da sauran lokaci mai tsawo, kar ka damu...!

Lokacin d ya cika shekara 17, sai ya kwanta ba shi da lafiya. Mahaifiyarsa ta kai shi Asibiti.

Bayan likita ya gama yi mata bayanin abin da ya samu ɗanta. Yaro ya ce, ta gaya masa abin da likita ya ce..! Mahaifiyar ta yi ta Kuka ta kasa magana...!! Yaro ya ce, na san abin da likita ya ce.... Cewa ya yi ciwon ajali ne, ba zan warke ba....!!

Bayan kwanaki kaɗan yaro ya warke ras, aka mayar da shi gida.... A katifar da aka kwantar da shi sai ya ga takarda an rubuta.... Ɗana zaka tuna lokacin da ka tambaye ni wacce kyauta zan baka in ka kai 18?

Ban manta ba.....

Likita ya ce, kana da matasalar Zuciya, ba zaka iya rayuwa ba har sai an samu wanda zai sadaukar da tasa zuciyar a yi maka "Heart Transplant" don haka, n baka tawa a matsayin kyautar cika shekara 18.....!!!"

S**airaj Hafiz Imam

Address

Yahaya Madawaki Way Katsina
Katsina

Telephone

+2348064962841

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina Media Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Katsina Media Online:

Share