22/02/2024
GWAMNA DIKKO GASKIYA A SAKE LALE
Rubutawah, AbdulHadi Ashamed Bawa✍️
Yanzu nike kallon wani rahoto a TRUST TV a kan harin 'yan bindiga a kauyen lamba, Wurma B, ta karamar hukumar Kurfi.
Abinda ya dauki hankalina shi ne yadda dan jaridar, daga nan cikin garin Katsina, ya sami labari har ya isa kauyen ya sami janazar mutane takwas din da aka kashe, amma kuma babu wakili ko daya, walau na karamar hukumar Kurfin ko na gwamnatin jiha.
A yadda ya fadi a rahoton shi, a duk jami'an gwamnati da ya nemi yaji ta bakin su, babu ɗaya da ya bashi wani bayani kan wannan lamari. Daga wanda yace ba hakkin shi bane bada bayanin, sai kuma wadanda basu daga wayarsu ba kuma sakon (SMS) da ya tura masu har ya zuwa bada rahoton babu amsa daga gare su.
Wannan rahoto ya nuna k**ar gwamnatoci basu damu da halin da al'umma suke ciki ba, ko suke shiga ba idan irin haka ta faru. Bahaushe ke cewa "sannu ba ta warkar da ciwo, amma tana da dadi".
Ya k**ata gwamnati ta sani cewa, bada bayanai sahihai a kan irin wadannan hare haren ba shi ke nuna gazawarta ba, hasali ma, badawar za ta hana yada nakasassun bayanai ga duniya, su kuma al'ummar da abin ya shafa za su san cewa gwamnati ta damu tare da nuna kulawa ga halin da suke ciki.
A wasu jihohin, gwamnatocin su ke fara fitar da bayani idan aka sami irin haka; bayanin yana kumsar sunan garin da abin ya afku tare da bayyana yawan mutanen da abin ya shafa har da sunayen su (wadanda s**a rasa rayuka da kuma wadanda aka jikkata), tare da sakon jajantawa tare da alhini gami da matakin da gwamnati ta dauka ko za ta dauka.
A cikin kwanaki hudu da s**a gabata, Allah kadai Ya san iyakar rayuka da dukiyar da aka rasa ta sanadiyyar wadannan hare hare, amma dai har yanzu banji gwamnatin jiha ta ce komai ba (kila kuma nine ban ji ba). Ko jiya an kashe kwamandan CWC na karamar hukumar Kankara, amma dai ni ban ga inda aka ce ita rundunar ko kuma gwamnati ta bada sakon jaje ga al'umma ba, musamman iyalan mamacin.
Ita kanta rundunar ta CWC, ban taba jin ta bada sanarwa ba, walau ta samun nasara ko akasi, duk kuwa da cewa a wurare da dama ta rasa jami'anta ta hannun wadannan 'yan ta'adda, a wasu lokutta kuma tana samun masu s**ar matakan da take dauka wajen gudanar da aikin ta.
Ya k**ata yadda sauran hukumomin tsaro suke da bangarorin hulda da jama'a, ita ma wannan runduna ya k**ata a sama mata nata, don ta rika bayar da sahihan rahotanni kan wannan aiki nata mai muhimmancin gaske.
Ina rokon gwamnati ta kalli wannan batu da idon basira, matsin da ake ciki yanzu, duk ya matso da zukatan mutane kusa. Ma'ana, ba wuya sai kaga abu kalilan amma mutum sai hassala, ka rasa kasa gane kan shi.
Ya Allah Ka ƙara tausaya mana, Kayi maganin abinda ya ishe mu.
Allahumma Aamiiin Ya Hayyu Ya Qayyum.