HRtv Network

HRtv Network For Updating News and Entertainment.

Muhammad Gambo Fagada (Gambu mai waƙar ɓarayi)Muhammadu Gambu ya kasance Makadi ne mai fasahar gaske. Kuma wakokinsa cik...
14/08/2026

Muhammad Gambo Fagada (Gambu mai waƙar ɓarayi)

Muhammadu Gambu ya kasance Makadi ne mai fasahar gaske. Kuma wakokinsa cike suke da balaga da azanci da salon magana. Duk da karin harshensa ya yi matukar tasiri cikin wakokinsa, amma wannan bai hana manazarta da masu sha’awar wakokinsa fahimta tare da nazartarsu ba.

Mawaƙin ya shahara da waƙoƙin ɓarayi, a lokacin da yake waƙa, to sai dai ya tuba da waƙoƙin na ɓarayi a shekarar 2009 a yayin da aka yi wani gagarumin bikin cikarsa shekara 60 a duniya, a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato.

An haifi Alhaji muhammad Gambo wanda da akafi sani da Gambu a garin fagadan dake karamar hukumar Jega a jihar Kebbi a Najeriya. Gambu tun tasowar yarintarsa yana da rashin ji ga kuma rashin tsoro.

Asalin sunan Gambu shi ne Muhammad Gambo, tun a wancen lokacin wasu kan kirashi da Gambu kasancewar rashin iya fadin sunan Gambo din kai tsaye.

Mahaifin Gambu shahararren Malami ne, yayin da shi kuma Gambu ba ruwansa da son gadon maihaifin nasa don haka nema Gambu kan dauki kayan harbinsa a kullum ya tafi Jeji harbin Tsuntsaye da kuma sauran namun Daji.

Duk lokacin da Gambu ya samo naman dajinsa sai ya taho gari ya saidawa da masu c**a, haka kuma shi ma a nan zaiyi zamansa.

Gambu ya fara mu’amala da barayi ne a wurin yin c**a, kasancewar duk lokacin da Gambu yayiwo farauta to a gurin yake zama har zuwa dare. Wannan dalilin ne yasa Gambu ya fara sanin barayi masu tare Hanya, da masu fasa shaguna da dai sauransu.

Gambu kan ambaci Kulu a cikin wakokinsa ne saboda ita Kulu itace matarsa ta farko da mahaifiyarsa ta aura masa, don haka yake sonta tare da mutunta ta kasancewar mahaifiyarsa ce ta zaba masa ita.

Alhaji Gambu ya rasu ranar Laraba 18 ga watan agusta 2016, ya rasu yana da kimanin shekaru 67 a duniya. Yabar mata 4 da “Yaya da kuma jikoki masu yawa. Ya rasu ne a garin Maiyama na Jihar Kebbi, yayin da a ke kan hanyar kai shi asibiti.

Muhammadu Cisse

Mata ta nemi kotu ta raba auren ta bisa rashin iya soyayya daga mijinta bayan shafe shekaru 35 tareWata matar aure, Hadi...
13/08/2026

Mata ta nemi kotu ta raba auren ta bisa rashin iya soyayya daga mijinta bayan shafe shekaru 35 tare

Wata matar aure, Hadiza Abdullahi, ta garzaya gaban Kotun Shari’a da ke Magajin Gari a Kaduna, inda ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta, Isa Usman, bisa dalilin rashin soyayya.

Hadiza, ta hannun lauyanta, Abubakar Suleiman, ta shaida wa kotun cewa ba ta ƙaunar mijinta, don haka ba za ta iya ci gaba da zaman aure da shi ba.

Ta roƙi kotun da ta raba aurensu ta hanyar Khul’i, wato hanyar sakin aure da mace ke mayar da sadakinta domin samun ’yancinta daga auren.

Lauyan matar ya ce an shafe shekaru 35 da aurar da ita, inda aka biya Naira 1,000 a matsayin sadakinta, kuma ta shirya mayar da kuɗin ga mijinta.

Sai dai lauyan mijin, I.T. Sanusi, ya ce wanda yake karewa bai iya tuna ainihin adadin sadakin da ya biya ba, amma ya tabbatar cewa ya fi Naira 1,000.

Ya kuma bayyana cewa mijin yana neman a biya shi Naira 300,000, yana mai neman kotu ta ba su lokaci domin gabatar da shaidar adadin sadakin da aka biya da kuma dalilin wannan buƙata.

Alƙalin kotun, Yakubu Abdullahi, ya ɗage sauraron shari’ar zuwa 2 ga Satumba, domin bai wa matar damar gabatar da hujjojin da za su taimaka wa kotun wajen yanke hukunci.

Daily Nigeria Hausa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sansanin ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, Jami’ai 10 Sun RasuRundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce sama ...
11/08/2026

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sansanin ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, Jami’ai 10 Sun Rasu

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce sama da ‘yan bindiga 200 dauke da mak**ai sun kai hari sansanin tsaro da ke Makuku, karamar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi, a safiyar Litinin.

A cewar rundunar, jami’an ‘yan sanda tare da goyon bayan sojoji da rundunar sojin sama daga Kebbi da Katsina sun dakile harin bayan artabu mai tsanani na sama da sa’o’i biyu.

Jami’an ‘yan sanda 10, ɗan kungiyar sa-kai guda daya da fararen hula biyu sun rasa rayukansu yayin harin. Rundunar ta kuma ce akalla ‘yan bindiga 17 aka kashe tare da lalata wasu daga cikin baburansu kafin sauran s**a tsere.

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya yaba da jarumtakar jami’an da s**a yi fada da maharan tare da ba da umarnin kara tsaurara matakan tsaro a Sakaba da yankunan da ke makwabtaka da ita.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya Ta K**a Mutane Uku Bisa Zargin Garkuwa Da wani FarfesaHukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun ...
08/08/2026

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya Ta K**a Mutane Uku Bisa Zargin Garkuwa Da wani Farfesa

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun k**a wasu mutane uku da ake zargi da hannu a garkuwar da aka yi da Shugaban Sashen Noma na Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Samuel Avengbe Okunsebor.

An k**a su ne a daren Juma’a a Mararraban Akunza da ke kan hanyar Lafia zuwa Makurdi.

Kamen nasu ya zo ne kwanaki biyu bayan DSS ta ceto Farfesa Okunsebor, wanda aka yi garkuwa da shi a Mile3, tsakanin Lafia da Nasarawa-Eggon.

A lokacin ceto shi, an kuma k**a wasu mutane biyu, ciki har da wata mata.

Sabbin waɗanda aka k**a sun haɗa da Yakubu Abubakar mai shekaru 25, Usman Abubakar Mairiga mai shekaru 37, da Sale Babauro Abubakar mai shekaru 27.

Majiyar tsaro ta ce ana tsare da mutanen ukun a hannun DSS domin ci gaba da bincike.

Daga shafin Dimokuraɗiyya

Kwastam ta k**a bindigogi 140 da tabar wiwi ta N373.8m a tashar TinCanHukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta ce ta k**a bi...
07/08/2026

Kwastam ta k**a bindigogi 140 da tabar wiwi ta N373.8m a tashar TinCan

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta ce ta k**a bindigogi kirar pump-action guda 140 da kuma kayan abinci da aka gauraya da tabar wiwi da darajarsu ta kai Naira miliyan 373.8 a Tashar Jiragen Ruwa ta TinCan da ke Legas.

Babban Kwanturolan hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana cewa an gano sassan bindigogin ne a cikin wani kwantena da aka ɓoye su, inda aka riga aka haɗa bindigogi 140 daga cikinsu, yayin da ake ci gaba da haɗa sauran sassan.

Ya ce an k**a manyan mutane biyu da ake zargi, yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da farautar wani da ake nema ruwa a jallo.

Adeniyi ya kuma ce jami'an kwastam sun k**a kwantena biyu ɗauke da biskit, alewa da sauran kayan ciye-ciye da aka gauraya da tabar wiwi, waɗanda aka ɓoye a cikin motocin da aka shigo da su, janareto, batura da yadudduka.

Ya gargadi cewa an shirya kayan ne cikin salo mai k**a da kayan ciye-ciye na yau da kullum domin jan hankalin yara da matasa, lamarin da ka iya sa mutane su ci su ba tare da sun san suna ɗauke da miyagun ƙwayoyi ba.

Hukumar NDLEA ta karɓi kayayyakin da aka k**a tare da bayyana cewa irin waɗannan kayan na zama sabon barazana ga lafiyar al'umma, tana mai kira ga iyaye da makarantu su ƙara sanya ido kan irin waɗannan kayayyaki.

Gwamnatin Kaduna ta bada tallafin gida ga mijin matar da aka kona da ran ta a jiharGwamnatin Jihar Kaduna ta bai wa iyal...
05/08/2026

Gwamnatin Kaduna ta bada tallafin gida ga mijin matar da aka kona da ran ta a jihar

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bai wa iyalan Aliyu, wanda matarsa ta mutu bayan wasu fusatattun mutane sun ƙone ta da ranta a Marabar Jos, kyautar gida, tallafin kuɗi da kuma guraben karatu kyauta.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ne ya miƙa mukullin gidan ga Aliyu a ranar Talata a Fadar Gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa gwamnati na da alhakin tallafa wa iyalan da s**a faɗa cikin irin waɗannan munanan hare-hare.

Tallafin ya biyo bayan mummunan lamarin da ya faru a Marabar Jos, inda wasu fusatattun mutane s**a kashe matar Aliyu bisa zargin satar yara. Sai dai mijinta ya musanta zargin, yana mai cewa matarsa ba ta aikata laifin da ake tuhumarta da shi ba.

Hakazalika, Gwamna Uba Sani ya miƙa kyautar gida ga Sarah Achi, matar marigayi Ven. Edwin Achi, wanda masu garkuwa da mutane s**a kashe bayan sun yi garkuwa da shi tare da matarsa a Jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa.

An sako Sarah Achi bayan ta shafe watanni uku a hannun masu garkuwa da mutanen, yayin da mijinta ya rasa ransa a lokacin da yake tsare. Gwamnan ya ce tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar na rage raɗaɗin da iyalan waɗanda rikice-rikice da ayyukan ta'addanci s**a shafa ke ciki.

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJI'UN: Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Kwamishiniyar Lafiya Ta Jihar Katsina A Lokacin Sojoji, Haj...
03/08/2026

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJI'UN: Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Kwamishiniyar Lafiya Ta Jihar Katsina A Lokacin Sojoji, Hajia Rabi Kumasi Rasuwa, Yau Litinin A Katsina.

An Yi Jana'izar Ta K**ar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Masallacin Banu Kumasi Dake Cikin Garin Katsina Da Yammacin Yau Litinin.

Allah Ya Jiƙan Ta Da Rahama!

01/08/2026
Ana Zargin Mahaifi Da Kashe Ƴarsa Kan Auren Dole A KatsinaWani magidanci ya shiga hannun hukuma kan zargin kashe ’yarsa ...
31/07/2026

Ana Zargin Mahaifi Da Kashe Ƴarsa Kan Auren Dole A Katsina

Wani magidanci ya shiga hannun hukuma kan zargin kashe ’yarsa a sak**akon yi mata duka saboda ta ƙi amincewa da auren dole a Jihar Katsina.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce ta fara bincike kan mutuwar matashiyar mai suna Ummul Khair, wadda ake zargin ta rasu bayan nata mahaifinta ya yi mata duka saboda ƙin amincewa ta auri wani mutum da ya zaɓa mata.

Jim kaɗan bayan faruwar lamarin, ’yan sanda daga caji ofis na Babbar Kasuwar Katsina s**a k**a magidancin mai suna Kabir Sani, wanda direban motar haya ne kuma mazaunin unguwar Shagari Low-Cost da ke cikin birnin Katsina.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilanmu cewa marigayiyar, wadda aka kiyasta shekarunta tsakanin 16 zuwa 18, ta daɗe tana adawa da yunƙurin mahaifinta na aurar da ita ga mutumin da ya zaɓa mata, lamarin da s**a ce ya janyo saɓanin a cikin iyalinsu.

A cewar shaidu, ana zargin mahaifin ya fara dukan ta tun ranar Laraba. Maƙwabta sun ce sun ji kukanta, kuma sun yi ta buga ƙofar gidan domin su shiga su ƙwace ta, amma mahaifin ya ki buɗe musu ƙofa.

Rahotanni sun ce dukan ya ci gaba har zuwa safiyar Alhamis, inda daga bisani yarinyar ta suma.

An gano faruwar lamarin ne lokacin da wasu ƙawayen marigayiyar s**a je gidansu a safiyar Alhamis domin su tafi makaranta tare.

A cewar rahotanni, sun tarar da ita babu rai, yayin da mahaifinta ke shirya jana’izarta, lamarin da ya sa s**a sanar da maƙwabta, waɗanda daga bisani s**a kai rahoto ga ’yan sanda.

Wani mazaunin unguwar ya ce, “Mun ji tana kuka tsawon dare, kuma mun yi ƙoƙarin shiga domin ceto ta, amma mahaifinta ya ƙi buɗe mana kofa. Da safe muka ji cewa ta rasu. Lamarin ya girgiza ɗaukacin mutanen unguwar.”

Wani mazaunin yankin ya ce marigayiyar ta dage cewa ita ce za ta yanke shawarar wanda za ta aura, yayin da mahaifinta ya nace sai ta auri mutumin da ya zaɓa mata.

An yi jana’izar marigayiyar a safiyar Alhamis, tare da binne ta a maƙabartar Abbatuwa da ke birnin Katsina, bisa koyarwar addinin Musulunci.

Majiyoyin ’yan sanda sun tabbatar da cewa wanda ake zargin na ci gaba da kasancewa a tsare a ofishin ’yan sanda na Babbar Kasuwar Katsina, yayin da jami’an bincike ke ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar yarinyar.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya ce yana da masaniya kan lamarin, amma zai yi ƙarin bayani ne bayan kammala binciken da ake yi.

Majiya: Aminiya

INA MAFITA: Tsadar rayuwa da gidaje sun hana matasan Nijeriya yin aure - UNFPAAsusun kula da yawan jama'a ta majalisar d...
29/07/2026

INA MAFITA: Tsadar rayuwa da gidaje sun hana matasan Nijeriya yin aure - UNFPA

Asusun kula da yawan jama'a ta majalisar dinkin duniya (UNFPA) ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa tsadar rayuwa, rashin aikin yi da matsalar gidaje na daga cikin manyan dalilan da ke hana matasan Nijeriya yin aure.

Yayin bikin Ranar Yawan Jama'a ta Duniya ta 2026, Wakiliyar UNFPA a Nijeriya, Muriel Mafiko, ta ce yawancin matasa na son yin aure da kafa iyali, amma matsin tattalin arziki da rashin tabbas kan makomarsu na hana su cimma wannan buri.

Address

IBB Way
Katsina
820231

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HRtv Network posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HRtv Network:

Shortcuts

Share