19/07/2025
Sanata Henry Seriake Dickson yace; A jiya na bi sahun takwarorina wajen halartar wani taron bita na kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dokoki kan Ilimi, inda muka tattauna kan kalubalen da ke tattare da ilimin firamare, musamman kan batun gyara da aka yi wa dokar karatun UBE.
Kamar yadda kowa ya sani, na sha bayyana ra’ayi na a zauren majalisar dattijai so da dama kan bukatar karfafa ilimin boko da rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar nan.
Har ila yau, na jaddada bukatar tattaunawa kan hanyoyin karfafawa da bunkasa iyawa ta fuskar neman ilimin harsuna, al'adu, da wayewar da ke da muhimmanci wajen fadada tunanin 'yan Nijeriya.
Saboda haka, na yi magana ne na goyon bayan ilimin Larabci ko Addinin Musulunci ga Musulmi, wadanda su ne babban tushen albarkatun kasa, da kuma ilimin Faransanci, a matsayinsa na guda daga cikin harsunan da ake koyarwa a kasa, ya kamata a karfafa, inganta su kamar yadda ake yiwa karatun Boko.
Zai kasance cikin maslahar ƙasarmu mu wadata yaran ƙasar nan da ilimin harsuna, al'adu, da wayewa gwargwadon iko don shirya su don yin gogayya da takwarorinsu na duniya.
Kamar yadda nake fada a kowane dandali, saka hannun jari a fannin ilimi ya kamata ya zama babban fifiko ga kowa a cikin gwamnati - shugaban kasa ko gwamna, kamar yadda na yi a matsayin Gwamna na tsawon shekaru takwas, ko da a lokacin koma bayan tattalin arziki, ba'a dakatar da tsare-tsaren ilimi, fannin ilimi yana bukatar a kara karfafa shi, tare da mai da hankali kan inganta cibiyoyi da tsari mai kyau na ilmantar da malamai, da kuma samar da manufofi masu kyau wajen zuba kudade domin tallafawa ilimin.