26/04/2023
KIN TABA TAMBAYAR SAURAYI BAYAN KA GAMA ZINA DA NI KA KAWO RUWA YA KAKE JI NA A RANKA?
To bari in amsa miki domin bazaki san komaiba injira kk shi ya amsa miki, a duk sanda namiji ya kawo ruwa da abokiyar lalarta ita tana murna tana jin dadin ta faranta masa rai, a tunaninta ai yanzu nasamu wani karin kusanci a zuciyarsa.
Ayya! Kin makara, domin shi da yakawo ruwa babu abinda yake bukata irin ki barshi yayi bacci, ko kwayan zarra na soyayyarki babu ita a zuciyansa a wannan lokaci, domin dama abinda yake nufi da yana sonki yana sha'awankine, kuma ya saukar da sha'awarshi a jikinki yanzu zai lallabeki ya daura ki a machine ki bar dakinsa a lokacinda ke bakiyi niyyan komawaba, hasalima kina son kasancewa da shi a wannan lokacin domin ke kinriga kingama yi masa mafi girman soyayya shi kuma kin gama amfani a wurinsa, zai ce dan Allah ki tafi zamu karasa a charting.
Yana fada miki cewa shi yana da ciwon sha'awa ko sha'awa ta mai yawa ko yayi azumi baya sauka? Formal tactics kenan na 99.9% na maza wurin yaudara da lalata muku rayuwa.
Babu wanda bashi da sha'awa saidai shi sha'awace abokiyar hirarsa, shi kadai ba zuciya labarin sha'awa, da abokai maganar sha'awa, da budurwa a charting maganar sha'awa, a kofar gidanku maganar sha'awa, sannan yace miki soyayya tana bukatar sirri ke kuma da shike baki da mafada kin rasa dattijai, ko kin iya yaudarar iyaye da sunan zuwa islamiyya, hadda, kitso, kawata ta kirani, an yadda da ke an baki dama kin wuce wurin dan iskanki. Tirrr
Nawa ake biyanki? Shine sadakin aurenki ko ladan iskanci? Me zaki saya da shi? Halal ko haram?
Namiji fasiki baya fatan ki gyara shi kullum gaba ta kaishi, wani ko sisi be biya ki hau machine ki biyoshi ya biya bukatarshi, ki tura mishi Kati, ki bashi kudi, kiyi mai girki, kuma ya debeki banza a matsayin banza, wallahi ba soyayya bace azabtar da ke Allah yakeyi da fasiki saboda wani na can yana son ki da aure kina nan kina ba dan iska kanki sadaka fi sabilisshaitan. Sunan dayawa Kuma wlh maza
Ya Allah ya Ubangiji ka tsaremu ka tsaremamu Yan uwan mu da Duk Kanin musulmi
Dr-Nuraddeen Katsiana
08068962793