25/10/2022
Hon. Sani Aliyu Danlami ya dauki nauyin karatun yara (35) a makarantar koyon aikin kiwon lafiya mai suna "Gial Health Technology" dake Katsina.
A ranar talata 25/10/2022, Hon. Sani Aliyu Danlami, Dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina, ya mika takardar shedar shiga makaranta (Admission) ga yaran wadanda yan asalin karamar hukumar Katsina ne.
Da yake gabatar da jawabinsa, yayin da yake mika takardun karatun ga yaran, Hon. Sani Danlami ya bayyana cewa" wannan ba shi bane karon farko da ya dauki nauyin karatun yara, musamman masu karamin karfi, a karamar hukumar Katsina.
Hon. Danlami ya ci gaba da bayyana wuraren da ya dauki nauyin tura yara karatu ciki da wajen Najeriya, tun kafin yaje majalisa, inda yace" ya dauki nauyin tura yara biyar karatu a wata makaranta dake birnin Cairo dake kasar Masar.
Sai wasu muhimman makarantu a cikin gida Najeriya, wanda su ka hada da makarantar koyon harkokin mulki dake Funtua, Jami'ar Alkalam dake Katsina, sai Jami'ar Ummaru Musa Yaradua dake Katsina. Da dai sauransu.
Daga karshe ya jawo hankalin yaran dasu tashi tsaye su jajirce suyi karatu duba da mahim mancin karatun da zasuyi, karatu bangaren lafiya yana da matukar alfanu ga Al'umma. Hon. Danlami ya bayyana cewa" ya biya dukkan kudaden karatun yaran har su gama.
Tunda farko da yake gabatar da jawabin maraba, daya daga cikin 'yan kwamitin shirya wannan shiri na Hon. Sani Danlami Malam Mustapha kofar bai ya bayyana cewa" aikin alheri ga Hon. Sani Danlami ba sabon abu bane, musamman ma wannan bangare na ilmi.
Da yake gabatar da jawabin godiya amadadin sauran yaran maza da su ka samu takardar shedar shiga makarantar watau Abbas Sabo ya godema Hon. Danlami akan wannan taimakon rayuwarsu da ta Al'umma da ya yi.
Ya kara da cewa" tun 2009, yakeson ya yi karatun aikin lafiya, amma Allah bai ba shi iko ba, amma ga shi yanzu ya samu kyauta daga Hon. Sani Aliyu Danlami, Allah ya saka da ma shi da alheri ya kuma ba shi abinda yake nema.