20/08/2025
Hukumar Kwastam ta k**a Miyagun Kwayoyi da darajarsu ta kai Naira Miliyan 690 a Katsina
Hukumar Kwastam ta Najeriya, shiyyar Katsina, ta cafke miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai Naira miliyan 690 a lokacin sintiri a iyakokin jihar.
Kwamptroller Idriss Abba-Aji, kwamandan hukumar a Katsina, ya bayyana wa manema labarai cewa jami’an kwastam sun gano kartani 14 na tramadol da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 650, tare da kwayoyin Fragbaline da s**a kai kusan Naira miliyan 28, da kuma tabar wiwi (cannabis sativa) da aka kiyasta darajarsu a kan Naira miliyan 15.
Wannan kamun, in ji shi, ya kasance mafi girma a tarihin shiyyar.
Ya ce masu safarar miyagun kwayoyin suna ɓoye su ne cikin motoci da ba a yi zaton haka ba.
"Wasu lokutan ma har a cikin mota da alama k**ar na manyan mutane suke ɓoyewa. Amma dukkan abin dole sai an tsayar, an bincika, sannan ake gano su,” in ji shi.
Hukumar ta ce an k**a mutum ɗaya da ke tuƙa ɗaya daga cikin motocin, amma daga bisani aka ba shi beli na wucin gadi.
Kwamptroller Abba-Aji ya kuma jaddada cewa yawancin matsalolin tsaro musamman ta’addanci da fashi a arewacin ƙasar na da alaƙa da shan miyagun kwayoyi. Ya ce hukumar za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro tare da kira ga jama’a da su taimaka wajen dakile safarar miyagun kwayoyi a iyakokin jihar Katsina.
Daga : SANI UMAR BUZU