
04/09/2024
'Yan sanda sun cafke wata budurwa da ta yi wa saurayi dan shekara 20 fyade
Yan sanda sun cafke wata budurwa yar shekara 18 da ta yi wa wani matashin dan saurayi mai shekaru 20 da haihuwa fyade.
Matashin ya ce budurwa ta yi sha'awarsa ta ja shi ta kai shi wani kangon gida alokacin baya cikin hankalinsa, inda ta yi amfani da wannan damar ta aikata masha'a da shi, ba tare da amincewarsa.
Na san masu karatu sun zaku su ji a ina wannan lamarin ya afku?
Tsauni Global Media ta ruwaito ta cewa lamarin ya afku a birnin Thessaloniki, wanda shi ne babban birni na biyu a kasar Greece.
Tuni yan sandan na Greece din s**a cika hannu da wannan nudurwar inda suke ci gaba da gudanar da bincike domin gano gaskiya su mika ta zuwa ga kuliya manta sabo don ta yanke mata hukunci daidai da abin da ta aikata na yi wa namiji fyade ba tare da amincewarsa kamar yadda majiyarmu ta Mail Online ta rawaito