02/11/2024
1. Ana samun kuɓuta daga azzaluman Shugabanni da zaluncinau ne idan aka yi haƙuri, aka bi Allah, aka nemi mafita a wajensa, da wannan haƙurin a kan bin Allah ne, Allah ya ɗaura Annabi Musa da mutanensa a kan Fir'auna da Jama'arsa.
(( قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ اسْتَعِينُوا بِاللَّهِ وَاصْبِرُوا ۖ إِنَّ الْأَرْضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ ۖ وَالْعَاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ)) ((قَالُوٓاْ أُوذِينَا مِن قَبْلِ أَن تَأْتِيَنَا وَمِنۢ بَعْدِ مَا جِئْتَنَا ۚ قَالَ عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُهْلِكَ عَدُوَّكُمْ وَيَسْتَخْلِفَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ)) A'araf 128-129
2. Cewa da wasu suke yi wai dole ne sai an fito an yaƙi zalunci ko ta wace hanya ce, wannan maganar ƙarya da gaskiya ce a cakuɗe, e, dole ne a kan kowa ya yaƙi zalunci, ya hana ɓarna gwargwadon ikonsa da damarsa, amma ta hanyar da Allah ya tsara ba ta kowace hanya ba, idan kuma mutane s**a ce ba za su bi hanyar Allah ba wajen yaƙar zalunci sai dai hanyar da zuciyarsu ta ƙawata musu, to ba za su taɓa samun mafita ba, dai a ci gaba da ruftawa cikin rami, saboda Allah zai cire hannunsa ne ya bar su da kansu a yi ta gwabzawa tsakanin zalunci da zalunci
((وكذالك نولى بعض الظالمين بعضا بما كانوا يكسبون)) An'am:129
3. Ta kowani gefe, Addinin Musulunci bai bar mu kara-zube ba, yana shar'anta mana manufofi ne tare da hanyar cim ma manufofin a haɗe, k**ar yadda ba ya halatta a sauka daga kan koyarwar shari'a cikin manufofin, k**ar faɗa da shirka da ƙoƙarin tabbatar da Tauhidi, faɗa da zalunci da tabbatar da Adalci, to haka ba ya halatta mutum ya fita daga tsarin shari'a, ya ɗakko hanyar da shari'a ba ta zo da ita ba wajen tabbatar da waɗannan manufofin, duk wanda ya yi haka shi ma ya faɗa cikin ɓarna kuma ba lallai ya samu mafita ba, ba a gyara ɓarna da ɓarna, Bahaushe ya ce kashin kare ba ya taki, jini ba ya maganin ƙishirwa, shi ya sa da Annabi (SAW) yana yi wa sahabbansa wasiyya a kan yadda za su mu'amalanci azzaluman shugawagabanni sai ya ce musu: ((أدُّوا إليهم حقَّهم، واسْأَلوا اللهَ الَّذي لكم.)), ma'ana "ku ku sauke haƙƙinsu da yake kanku, sannan ku nemi naku haƙƙin a wajen Allah" Bukhari: 7052.
4. Zaluncin shugaba ba ya halatta wa talaka zalunci, kowa zai girbi abin da ya shuka ne ranar ƙiyama, ko da kuwa na sama, ko shugaba shi ya koya wa mabiyi ko na ƙasa ɓarna, to wannan ba ya wanke mabiyin daga ɓarnarsa, tare da cewa wanda ya koyar da ɓarna, mai mulki ne shi ko Malami ko Mai gida, yana da kwatakwacin laifin duk wanda ya yi koyi da shi a kai, amma hakan ba ya nufin shi mabiyin ya sha, zububinsa yana nan daram shi ma zai je ya girba, kuma da sannu zai yi nadamar koyi da ya yi da wani a kan ba daidai ba.
((ومن دعا إلى ضلالة كان عليه من الإثم مثل آثام من تبعه لا ينقص ذلك من آثامهم شيئاً".))Muslim:2648
(( إِذْ تَبَرَّأَ الَّذِينَ اتُّبِعُوا مِنَ الَّذِينَ اتَّبَعُوا وَرَأَوُا الْعَذَابَ وَتَقَطَّعَتْ بِهِمُ الْأَسْبَابُ))((وَقَالَ الَّذِينَ اتَّبَعُوا لَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَتَبَرَّأَ مِنْهُمْ كَمَا تَبَرَّءُوا مِنَّا ۗ كَذَٰلِكَ يُرِيهِمُ اللَّهُ أَعْمَالَهُمْ حَسَرَاتٍ عَلَيْهِمْ ۖ وَمَا هُم بِخَارِجِينَ مِنَ النَّارِ)) Baƙara: 166-167
5. Abin da zaluncin kowane mai zalunci, shugaba ne shi ko talaka, yake wajabta mana shi ne komawa ga Allah, da riƙo da hanyar shari'a wajen hana shi zaluncin da neman haƙƙin waɗanda ya cuta, ba wai mu ma mu narke mu zama maha'inta macuta masu yin yadda s**a ga dama ba idan muka yi haka mu ma mun zama irinsu, shi ya sa idan wani maɓarnaci ya zo ya yi zina da matarka ko ƴarka, kai ma ba zuwa za ka yi ka yi zina da matarsa ko ƴarsa ba don ka huce ko ka rama, haka wanda ya maka sata kai ma ba zuwa za ka yi ka masa sata ko ka sa a masa ba, ko ka yi wa wani da sunan kai ma an ma, akwai hanyoyin da shari'a ta gindaya na yadda za a mu'amalanci waɗannan abubuwan wanda idan aka kauce musu sai dai a ƙara wa ɓarnar faɗi memakon a rage ta, haka idan shugabanni sun yi zalunci, ba ya halatta ma duk wani nau'in ɓarna da fitina, da sunan ai su ma manyan haka suke, a'a, kowa kabarinsa daban hisabinsa daban.
((ألا تزر وازرة وزر أخرى)) ((وأن ليس للإنسان إلا ما سعى)) ((وأن سعيه سوف يرى)) Najmi:38-40
6. Ana haƙuri da zaluncin shugabanni ne saboda Allah, kuma saboda haka shari'a ta tsara don neman mafita, kuma a kansa ne Allah yake wa al'uma sak**ako mai daɗi, Allah da kansa yake ɗaukar nauyin kawo wa mutane canji na ƙwarai ta hanyar da s**a yi tsammani ko wadda ba su yi ba, idan s**a koma gare shi, s**a yi biyayya, da haƙuri da Jarabawar da s**a samu kansu a ciki. Allah (SWT) ya ce dangane da da'awar Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa:
(( وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِي الْأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضَىٰ لَهُمْ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّن بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْنًا ۚ يَعْبُدُونَنِي لَا يُشْرِكُونَ بِي شَيْئًا ۚ وَمَن كَفَرَ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ)) (55) Nur:55
Imamuɗɗabari ya Ambata a ƙarƙashin wannan ayar cewa ta sauka ne a wani lokaci da sahabbai s**a kai kuka zuwa ga Annabi (SAW) a kan tsananin matsi da tsoro da danniya da suke ciki, suna ji k**ar ba za a fita daga wannan yanayin ba. Cikin wannan ayar sai Allah yake musu alƙawarin in dai s**a riƙe imani da Allah s**a yi aiki na ƙwarai to zai ba su nasara ya Mallaka musu daula su samu amincin yin addininsu, kuma ya maye musu tsoro da aminci. Kamar dai yadda ta ce dangane da sha'anin banu Isra'ila:
(( وَأَوْرَثْنَا الْقَوْمَ الَّذِينَ كَانُوا يُسْتَضْعَفُونَ مَشَارِقَ الْأَرْضِ وَمَغَارِبَهَا الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا ۖ وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ الْحُسْنَىٰ عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ بِمَا صَبَرُوا ۖ وَدَمَّرْنَا مَا كَانَ يَصْنَعُ فِرْعَوْنُوَقَوْمُهُ وَمَا كَانُوا يَعْرِشُونَ)) A'araf:137
Saboda haka, ba wai wannan cewa a yi haƙurin yana nufin an yarda da abin da suke yi na zalunci ba ne, jifan duk wanda ya ce mutane su yi haƙuri su koma ga Allah da cewa yana kare azzalumai ko ya yarda da abin da suke yi, ita wannan maganar ita ce babbar zalunci, saboda babu adalcin da ya wuce a nusar da mutane a kan tsayawa kan hanyar Allah don da ita kaɗai ne ake iya samun mafita mai ɗorewa.
7. Haka kuma haƙuri ba ya nufin ba za a yi wa shugabanni nasiha ba, ko ba za a yi umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna ba, saboda hakan yana kishiyantar zama na ƙwarai da bin Allah, kuma Allah ya game Al'uma da uƙuba idan s**a kasance masu shiru a kan ɓarna, saboda haka wajibi ne musamman ga Malamai su tsaya da wa'azi da karantarwa da umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, gwargwadon yadda shari'a ta tanadar, Annabi (SAW) ya ce:
(( الدِّينُ النَّصِيحَةُ. قُلْنا: لِمَنْ؟ قالَ: لِلَّهِ ولِكِتابِهِ ولِرَسولِهِ ولأَئِمَّةِ المُسْلِمِينَ وعامَّتِهِمْ)) Muslim:55
(( والذي نفسي بيدِه لتَأمرُنَّ بالمعروفِ ولتَنهوُنَّ عن المنكرِ أوليُوشِكَنَّ اللهُ أن يَبعثَ عليكمْ عقابًا منهُ فتدعونهُ فلا يَستجيبُ لكمْ)) Tirmizi:2169
Wanda idan Allah ya zo saukar wa da al'uma uƙuba dalilin shiru a kan ɓarna, ana tseratar da masu hani ne kawai, a azabtar masu zaluncin da masu goya musu baya kai tsaye da masu shiru da miƙa zuciya ga zaluncin.
((فَلَمَّا نَسُوا مَا ذُكِّرُوا بِهِ أَنجَيْنَا الَّذِينَ يَنْهَوْنَ عَنِ السُّوءِ وَأَخَذْنَا الَّذِينَ ظَلَمُوا بِعَذَابٍ بَئِيسٍ بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ)) A'araf:165
((إنَّه يُسْتَعْمَلُ علَيْكُم أُمَراءُ، فَتَعْرِفُونَ وتُنْكِرُونَ، فمَن كَرِهَ فقَدْ بَرِئَ، ومَن أنْكَرَ فقَدْ سَلِمَ، ولَكِنْ مَن رَضِيَ وتابَعَ)) Muslim:1854
8. A gefe guda kuma, wa'azi da hani a kan ɓarna ba ya wajabta fito na fito da azzaluman da ingiza al'uma a ce su fita su ɗaga musu yatsa ko su ƙwaci haƙƙinsu ƙarfi da yaji, ko a hargitsa al'amura a yi uwar watsi, duk Malami ko mai da'awa ko wani ɗan gwagwarmaya da ya ɗaura al'uma a kan irin wannan hanyar ba shakka zai samu sak**akonsa wajen Allah, kuma zai girbi abin da ya shuka, don shi ma idan fitina ta zo ba za ta ƙyale shi ba. Babban abin da ake buƙata daga Malamai a irin wannan yanayin shi ne su kasance masu kira izuwa ga hanyar Allah, su guji raɓar azzaluman masu mulki da ba su kariya ko neman tuwo a wajensu, su koma gefe su kafa da'awarsu, su gina ta a kan haɗa al'uma da Allah, su karantar da su haƙuri da komawa ga Allah da neman mafita a wajensa, su jira har izuwa lokacin da Allah zai yi ikonsa, wannan ita ce hanyar Annabawan Allah. Shi ya sa Annabi Musa (A.S) bai ingiza mutanensa cewa su fita su gwabza da Fir'auna da mutanensa ba, sai dai ya yi tausar mutanensa da cewa idan sun tabbata a kan hanyar Allah zai kawo musu mafita a ƙarshen lamari, haka Annabi Muhammad (SAW), duk da matsin lambar da ya samu a Makka, har ta kai an kore shi daga garin, ya yi ta ba su haƙuri har ya tarbiyyantar da al'uma ta kafu a kan tauhidi da bin Allah, sannan aka umarce shi da Jihadi. To in dai an kyautata zuciyoyi an bi Allah komai daga baya mai sauƙi ne, wannan kuma yana buƙatar jagorancin Malamai na Allah, wanda shi ne abin da alumarmu ta fi tsananin buƙatuwa gare shi sama da komai, in dai har mafitan muke son samu. Ba wata hanya da za ta iya tseratar mana da Addininmu da duniyarmu idan ba cikakken komawa ga Allah muka samu ba bisa jagorancin Malamai na ƙwarai.
Allah ya ba wa ƙasarmu lafiya da zama lafiya.
Mallam Bahaushe
03/08/2024