22/03/2025
Sabuwar Jam'iyyar Maja Ta Su El-Rufai Da Atiku Yaudara Ce Ba Talakawa Ne A Gabansu Ba
Gamayya ce ta masu neman muƙami da mulki da neman takara, ba al'umma ko talakawa ne a gabansu ba.
Ya ku al’ummar Arewa, ku dubi halin da ake ciki ku tambayi kanku, shin har yanzu za mu ci gaba da bari wasu ‘yan siyasa su rika amfani da mu don biyan bukatunsu? Yanzu da aka saka dokar ta ɓaci a Jihar Rivers, sai gashi Nasiru El-Rufai da Atiku Abubakar sun hada kansu da wasu domin su caccaki gwamnatin Tinubu.
Ina s**a kasance lokacin da ake kashe al’ummar mu a Kaduna, Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto? A lokacin da aka yi ta satar mutane, garkuwa da su, da hallaka iyayenmu da ‘ya’yanmu, ina ku ke? El-Rufai, kana gwamnan Kaduna, lokacin da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a jiharka, ba ka taba yin taron manema labarai domin nuna damuwarka ba. Atiku, lokacin da kake cikin gwamnati a baya, ba ka taba kokarin kawo mafita ga Arewa ba.
Amma yau da aka cire gwamnan Rivers, sai gashi kun fito kuna ihun adalci! Shin, lokacin da kuka ke mulki Atiku yana mataimakin shugaban kasa, ba kun cire gwamnonin jihohi kamar Bayelsa da Plateau ba? El-Rufai da Atiku, lokacin da kuka ke mulki a zamanin Obasanjo, har gwamnonin jihohi uku kuka tsige! To me yasa a lokacin hakan ya zama daidai, amma yanzu da Tinubu ya yi, sai ku ce rashin adalci ne? To menene banbancinku da shi Tinubu ɗin, ko dan shi daga Kudancin Najeriya yake, ku kuma daga Arewa?
Shin me kuka yi lokacin da aka cire tallafin man fetur? Me yasa baku taba yin magana ba lokacin da aka jefa talaka a cikin wahala? Domin kun san cewa baku ne za ku sha wahalar ba, shiyasa kuka yi shiru. Amma yanzu da bukatarku ta taso, sai gashi kun fara taron manema labarai da shirye-shiryen kafa wata jam’iyyar maja.
Atiku da El-Rufai, kuna son sake hada wata jam’iyyar maja domin me? Ba ku ne kuka kafa APC ba? Ba ku ne kuka ce ita ce mafita ga Najeriya ba? Yanzu da ku ka gaza cimma burin ku, sai ku dawo kuna kokarin yaudarar mutane da wata sabuwar jam’iyyar?
Ya ku ‘yan Arewa, muna gane wasan waɗannan mutanen, ka da mu sake bari su yi amfani da mu don biyan bukatunsu karshe su watsar damu. Mun koyi darasi daga baya, kuma wannan karon, ba za mu bari su yi amfani da mu ba!
Ra'ayin Comr Haidar H Hasheem