Gkhn gidan kwallo hausa news

Gkhn gidan kwallo hausa news Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gkhn gidan kwallo hausa news, Media/News Company, Katsina.

labaran wasanni bbc hausa news
16/10/2023

labaran wasanni bbc hausa news

Sa'o'i 3 da s**a wuceLiverpool da Newcastle United na sa ido a kan dan gaban Ingila Jarrod Bowen mai shekara 26 yayin da...
06/10/2023

Sa'o'i 3 da s**a wuce

Liverpool da Newcastle United na sa ido a kan dan gaban Ingila Jarrod Bowen mai shekara 26 yayin da maganar sabunta kwantiraginsa da West Ham ke ci gaba da tafiyar hawainiya. (Talksport)

Manchester City na shirin fara tattaunawa da Erling Haaland, a kan sabon kwantiragi domin hana Real Madrid, zawarcinsa.(Telegraph)

Manchester City za ta yi gogayya da Barcelona wajen zawarcin matashin dan wasan tsakiya dan Netherlands Xavi Simons daga Paris St-Germain a bazara mai zuwa. (Fichajes)

Dan gaban Manchester United da Ingila Jadon Sancho, yana son sake komawa Borussia Dortmund a watan Janairu. (90min)

Dan wasan tsakiya na Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21, ya tafi Chelsea maimakon Liverpool saboda tuni ya riga ya yi wa kungiyar alkawarin zuwa can a lokacin yana Brighton. (Standard)

Chelsea na shirin tattaunawa da dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher yayin da yake tunkarar wata 18 na karshen kwantiraginsa. (Mail)

Andre Onana, ba ya nuna sha'awar barin Manchester United domin zuwa ya yi wa kasarsa Kamaru wasan gasar cin Kofin Afirka. (ESPN)

Saudiyya za ta nemi shirya gasar cin kofin duniya ta 20345 Oktoba 2023

Southgate ya gayyaci Harry Maguire tawagar Ingila5 Oktoba 2023

Rashin Messi ya jefa Inter Miami a tsaka mai wuya5 Oktoba 2023

West Ham na sa ido a kan matashin dan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Emile Smith Rowe. (Teamtalk)

Dan wasan gaba na gefe na Japan Kaoru Mitoma, na dab da sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar shekara biyar da Brighton duk da danganta shi da ake yi da kungiyoyin Premier da dama.(Talksport)

Newcastle ta fara tattaunawa domin tsawaita kwantiragin dan wasan tsakiya na Ingila Sean Longstaff har zuwa 2028. (Nicolo Schira)

'Ƴan Qatar da ke son sayen Manchester United ba za su kara tayin da s**a yi na sayen kungiyar ba zuwa fam miliyan biyar duk da barazanar sabon cinikin da ake neman yi da Sir Jim Ratcliffe. (Times)

Everton na dab da cimma yarjejeniya ta tsawon lokaci da dan bayan Ingila Jarrad Branthwa

A halin da ake ciki bukatar hadin gwiwa tsakanin Birtaniya da Ireland ne kadai bukatar da ake da ita ta neman shirya gas...
05/10/2023

A halin da ake ciki bukatar hadin gwiwa tsakanin Birtaniya da Ireland ne kadai bukatar da ake da ita ta neman shirya gasar Euro 2028 ba tare da hamayya ba bayan da Turkiyya ta janye yunkurinta na haɗa hannu da Italiya wurin neman shirya gasar Euro 2032.

A watan Yuli ne Turkiyya ta amince ta haɗa hannu da Italiya wurin shirya gasar Euro 2032 kuma hukumar kwallon kafa ta Turai (Uefa ) ta amince da hakan.

Yayin da Italiya ta nemi shirya gasar ta Euro 2032 ita kaɗai, Turkiyya ta nemi karɓar baƙuncin gasar Euro 2028 da kuma Euro 2032.

Yanzu ƙasashen biyu na jiran amincewar hukumar ta Uefa a taron kwamitin zartarwata.

Turkiyya ta karbi bakuncin wasan karshe na gasar zakarun Turai a watan Yuni tsakanin Manchester City da Inter Milan a filin wasa na Ataturk da ke Istanbul, amma ba a taba gudanar da wata babbar gasa a kasar ba.

a'o'i 3 da s**a wuceTsohon kocin Chelsea da Everton, Frank Lampard ya na sha'awar maye gurbin Michael Beale a ƙungiyar R...
05/10/2023

a'o'i 3 da s**a wuce

Tsohon kocin Chelsea da Everton, Frank Lampard ya na sha'awar maye gurbin Michael Beale a ƙungiyar Rangers.

Lampard, mai shekaru 45, ya nuna cewa a shirye yake domin tattaunawa da kungiyar da ta rabu da Beale ranar Lahadin da ta gabata bayan rashin nasara a wasanni uku cikin bakwai na gasar Premier na Scotland a kakar wasa ta bana.

Kwanan nan Lampard ya kasance kocin riko a Chelsea daga Afrilu zuwa Mayu.

Duk da haka, zamansa na biyu a Stamford Bridge bai yi kyau ba, inda ya samu nasara sau ɗaya kacal a wasanni 11.

Ya kuma jagoranci Everton daga watan Janairun 2022 kafin aka sallame shi a watan Janairun wannan shekaran bayan rashin nasara sau tara a wasanni 12 da ya ja ragamar kungiyar.

Steven Davis da Alex Rae ke rike da ragamar Rangers na wucin-gadi, wadanda za su ziyarci Aris Limassol a gasar Europa league ranar Alhamis kafin su ziyarci St Mirren ranar Lahadi mai zuwa.

Sa'o'i 3 da s**a wuceKungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke buga gasar MLS a Amurka ta samu koma baya a yunkurinta n...
05/10/2023

Sa'o'i 3 da s**a wuce

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke buga gasar MLS a Amurka ta samu koma baya a yunkurinta na taka rawar gani a kakar wasa ta bana, inda Chicago Fire ta doke ta da ci 4-1, wasan da Lionel Messi bai samu bugawa ba saboda rauni.

Tsohon dan wasan Liverpool, Xherdan Shaqiri ne ya zura kwallo biyu a ragar Miami sannan Maren Haile-Selassie shi ma ya jefa kwallaye biyu.

'Yan kallo 62,124 ne s**a halarci wasan a filin wasan Soldier Field da ke Chicago inda s**a yi fatan ganin kyaftin din Argentina Lionel Messi.

Amma dan wasan mai shekaru 36 ya buga wasa sau daya ne kacal a wasanni bakwai tun ranar 3 ga watan Satumba.

Messi, wanda ya kulla yarjejeniya da Miami a watan Yuli bayan kwantiraginsa da Paris St-Germain ta kare, ya kalli wasan karshe da Houston Dynamo ta doke sabuwar kungiyarsa da ci 2-1 a wasan karshe na gasar cin kofin US Open a makon da ya gabata.

Inter Miami ita ce ta 14 a gasar MLS da ta kunshi kungiyoyi 15 kuma tana bukatar lashe dukkan wasanninta guda uku na gaba kafin ta iya tsallakawa zuwa mataki na gaba.

Mintuna 29 da s**a wuceKocin Ingila Gareth Southgate ya gayyaci tsohon kyaftin din Manchester united Harry Maguire tawag...
05/10/2023

Mintuna 29 da s**a wuce

Kocin Ingila Gareth Southgate ya gayyaci tsohon kyaftin din Manchester united Harry Maguire tawagar Ingila don fafatawa a wasannin da za ta buga da Australia da kuma Italiya a watan Oktoba a filin wasan Wembley.

Wasa ɗaya ne tal aka fara da Maguire a United a kakar wasan bana inda ya buga wasan gasar Carabao cup da s**a doke Crystal Palace da ci 3-0 a ranar 26 ga Satumba.

Kocin na ingila ya kuma sake kiran dan wasan Aston Villa Ollie Watkins wanda ya buga wa Ingila wasan karshe a watan Maris na 2022.

Amma dan wasan gaban Chelsea Raheem Sterling bai sami shiga cikin jerin 'yan wasan kasar ba a karo na hudu a jere.

Jarrod Bowen na West Ham, wanda aka kira zuwa tawagar Ingila a karon farko a watan Mayun 2022, ya dawo bayan ya rasa gurbi a tawagar a watan Satumba.

Har ila yau an gayyaci dan wasan gaban Arsenal Bukayo Saka, duk da cewa dan wasan na fama da raunin da ya tilasta masa fita daga wasan Arsenal da Lens bayan mintuna 34 ranar Talata.

Ingila za ta kara da Australia a wasan sada zumunci a ranar 13 ga watan Oktoba kafin ta fafata da Italiya a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2024 a ranar 17 ga Oktoba.

Oktoba 2023Za a gudanar da gasar cin kofin duniya a 2030 a kasahe shida kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa...
05/10/2023

Oktoba 2023

Za a gudanar da gasar cin kofin duniya a 2030 a kasahe shida kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta sanar.

An bayyana Sifaniya da Portugal da Morocco cikin masu hadaka, yayin da za a fara wasa uku a Uruguay da Argentina da kuma Paraguay.

Wasan da za a fara a Kudancin Amurka a gasar zai zama na bikin shekara 100 da Fifa ta fara gabatar da gasar a Montevideo.

A shekara mai zuwa hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta tabbatar da wannan tsarin a babban taron da za ta gudanar.

Fifa ta kara da cewar za ta duba damar bayar da karbar bakuncin gasar kofin duniya a 2034, tsakanin nahiyar Asia da yankin Oceania.

Ana sa ran Saudi Arabia za ta karbi bakuncin wasannin da za a yi a 2034 a karon farko a tarihi.

Birnin Montevideo a Uruguay shi ne ya karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 1930, a nan za a buga wasan farko a 2030 daga nan a yi fafatawa a Argentina da kuma Paraguay.

Sauran wasannin daga fafatawa 48 za a raba tsakanin Afirka da Turai, wato Morocco da Portugal da Sifaniya.

Idan har an amince da wannan shirin, Morocco za ta zama ta biyu a Afrika da za ta karbi bakuncin gasar kofin duniya, bayan Afirka ta Kudu a 2010.

Portugal ba ta taba karbar bakuncin gasar kofin duniya ba, amma ta gudanar da wasannin cin kofin nahiyar Turai a 2004.

Sifaniya ta karbi bakuncin gasar 1982, inda Italiya ta lashe kofin na uku jimilla.

Qatar ce ta gudanar da gasar kofin duniya da aka yi a 2022, wadda Argentina ta dauka na uku a tarihi.

The performance of the Arsenal
28/09/2023

The performance of the Arsenal

Address

Katsina

Telephone

+2348063862252

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gkhn gidan kwallo hausa news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gkhn gidan kwallo hausa news:

Share