05/11/2025
DCP ABBA KYARI YA MUSANTA MALLAKAR KADARORIN DA NDLEA TA DANGANTA DA SHI
Dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, ya musanta mallakar wata kaddara da Hukumar NDLEA ta alakanta da shi a shari’ar da ake yi masa kan zargin kin bayyana dukiyoyi.
A zaman kotu na ranar Talata a gaban Mai Shari’a James Omotoso na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Kyari ya ce wasu daga cikin kadarorin da ake gardama mallakar mahaifinsa ne marigayi, wanda yake da “’ya’ya kusan 30”.
Tsohon shugaban rundunar IRT ya ce ya yi mamakin zargin da ake yi masa, yana mai cewa takardun kadarorin suna hannun Ma’aikatar Kasa ta Jihar Borno.
Ya kuma musanta mallakar filin wasan polo da aka danganta da shi a Borno, yana mai cewa ba shi da ikon mallakar irin wannan fili mai girma.
“A dukiya irin wacce ake magana a kanta, ma Aliko Dangote, attajirin Najeriya, ba shi da ita; b***e ni,” in ji shi a gaban kotu.
Kyari ya kara da cewa filin polo tun yana yaro yake wanzuwa, “mu kan je mu buga wasa a can tun can.”
Sai dai ya amsa mallakar wani filin gona da ke kan hanyar Abuja–Kaduna, yana mai cewa ya shafe kusan shekaru goma yana kula da gonar.