03/11/2025
Shahararren mawakin Najeriya, Damini Ogulu wanda aka fi sani da Burna Boy, ya bayyana cewa ya bar addinin Kiristanci ya karɓi Musulunci ne bayan dogon tunani da bincike kan neman gaskiya.
A cewar Burna Boy, matakin da ya ɗauka ba wai saboda matsin lamba ba ne, sai don ƙwarewar da ya samu ta tunani da nazari game da manufar rayuwa da ma’anar addini.
“Na dade ina bincike da tambayar kaina meye gaskiya game da rayuwa da addini. Daga ƙarshe, na ji zuciyata ta natsu da Musulunci. Wannan shi ne dalilin da ya sa na rungumi wannan hanya,” in ji shi.
Mawakin ya bayyana cewa, duk da wannan sauyi, yana girmama sauran addinai, tare da kira ga mutane su zauna lafiya da juna ba tare da bambancin addini ko ƙabila ba.
Burna Boy, wanda ya shahara da wakokinsa na duniya kamar “Last Last” da “City Boys”, ya ce burinsa shi ne ya zama mutum mai gaskiya da mutunci, komai bambancin fahimta.