05/07/2026
Kuɗi da Kadarorin da Aka Ce Alhaji Aminu Dantata Ya Bari a Duniya
An ce ya bar kuɗi har naira tiriliyan 61 a bankunan Najeriya da na ƙasashen waje.
Haka kuma, an ce ya mallaki gidajen mai 800 a ciki da wajen Najeriya, waɗanda ba sa ɗauke da sunansa amma mallakinsa ne.
A jihar Kano kaɗai, an ce ya bar gidaje 500, tare da filaye 1,200 masu katanga ko ginin farko kawai, ba tare da cikakken gini ba.
An kuma ce ya bar gidaje 320 a sauran garuruwan Najeriya da ƙasashen waje.
An ce ya mallaki motoci 280 da ake amfani da su, sannan akwai motoci 120 da ba a amfani da su, suna ajiye kawai.
Haka kuma, an ce ya mallaki hannayen jari da darajarsu ta haura naira tiriliyan 30 a kamfanoni na cikin gida da na ƙasashen waje.
A wata hira da ya bayar a shekarar 2022, ya ce ya fara sayen jirgin sama na kansa tun 1967, lokacin da farashin jirgi ya kasance dala 120,000. An ce ya mallaki jiragen sama na kansa guda 10, kuma kowanne bai gaza darajar naira biliyan 1 ba.
Ya rayu tare da mata huɗu, ya bar 'ya'ya sama da 45, da kuma jikoki fiye da 150.
An binne shi a Madina, ƙasar Saudiyya, bisa ga wasiyyarsa.
Allahu Akbar!
Copied