Flash News.Ng

Flash News.Ng INGANTATTUN LABARAI...
Jaridar Flash-newsNg Tana Gabatar Da Shirye-shiryenta Cikin Harshen Hausa Da Turanci. Call/WhatsApp 08036411514 Media news company

NEMAN ILIMI: Kullum sai ta shafe tsawon kilomita 3 zuwa 4 a kasa kafin take isa Makarantar Firamarensu, kuma duk da haka...
09/07/2025

NEMAN ILIMI: Kullum sai ta shafe tsawon kilomita 3 zuwa 4 a kasa kafin take isa Makarantar Firamarensu, kuma duk da haka ita take riga kowa zuwa Makarantar

An gano dalibar da take riga kowa zuwa makarantar firamaren Irshadul Ibadi Sani Mashall dake karamar hukumar Kura a jihar Kano.

Tana isa makaranta tun kafin karfe bakwai na safe.

Wannann Malamin mai suna Mai Unguwa Sunusi Sikifa Malami Makarantar Firamare ne kuma shugaban makaranta ne a karamar hukumar Garun-Malam, ya fito kan hanyar zuwa tasa makarantar sai ya riske ta a kofar makarantar Firamaren su yarinyar waro Irshadul Ibadi Sani tana dakon a zo a bude kofar shiga makarantar ta su domin daukar darasi.

Daga Dantala Uba Nuhu Kura

RASHIN TSARO: Kaso 90% na yan ta'addan dake kai hari a jihar Katsina suna zaune ne a cikinmu - Inji Gwamnan Katsina Dikk...
09/07/2025

RASHIN TSARO: Kaso 90% na yan ta'addan dake kai hari a jihar Katsina suna zaune ne a cikinmu - Inji Gwamnan Katsina Dikko Radda

Mi za ku ce game da haka?

KAJI KO: Makarantar Firamare Ɗaya Tilo Da Ke Garin Gulbin Boka A Jihar Neja Ta Zama KangoHarkar ilimi a matakin firamare...
09/07/2025

KAJI KO: Makarantar Firamare Ɗaya Tilo Da Ke Garin Gulbin Boka A Jihar Neja Ta Zama Kango

Harkar ilimi a matakin firamare na fuskantar barazanar durƙushewa a garin Gulbin Boka, karamar hukumar Mariga, Jihar Neja, idan har mahukunta ba su ɗauki mataki ba.

Mutanen garin sun yi korafi kan halin da Makarantar Firamarin ta Gulbin Boka ke ciki, inda s**a bayyana cewa ginin makarantar ya lalace matuƙa, kuma hakan na barazana ga makomar ilimin ’ya’yansu.

An ruwaito cewa makarantar ta kusan kai shekara huɗu a rufe, sakamakon rashin tsaro da ya addabi yankin a shekarun baya, wanda ya sa aka girke jami’an tsaro a cikin makarantar.

Kafin a rufe makarantar, dalibai 976 ne ke halartar karatu. Amma a halin yanzu, dalibai 150 kaɗai ke zuwa wani wuri na wucin gadi da jama’ar garin s**a tanada don ci gaba da karatu.

Yanzu haka, mutanen garin sun yi yunkurin haɗa taro da sisi don gyaran makarantar, amma gyaran yafi karfi su. Don haka, sun roƙi hukumomi da masu ruwa da tsaki da su duba halin da wannan makaranta ke ciki domin ɗaukar mataki cikin gaggawa kafin lokaci ya ƙure.

RASHIN TSARO: Labarin dake fitowa daga yankin Garin Mangoro dake Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja na nuni da cewar y...
08/07/2025

RASHIN TSARO: Labarin dake fitowa daga yankin Garin Mangoro dake Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja na nuni da cewar yanzun haka Yan bindiga na cikin garin kamar yadda wasu mazauna garin s**a shaida mana.

Muna fatan ku saka su cikin Addu'ar ku!

Yadda aka gudanar da Addu'o'in roƙon ruwa a yau Talata, a unguwar Samaru da ke garin Zaria jihar Kaduna.Allah ya bamu ru...
08/07/2025

Yadda aka gudanar da Addu'o'in roƙon ruwa a yau Talata, a unguwar Samaru da ke garin Zaria jihar Kaduna.

Allah ya bamu ruwa ya bamu damuna mai albarka

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Barr. Abba Hikima ya maka hukumar kiyaye haɗura FRSC KotuBabban Lauya Barr. Abba Hikima ya maka hukumar...
08/07/2025

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Barr. Abba Hikima ya maka hukumar kiyaye haɗura FRSC Kotu

Babban Lauya Barr. Abba Hikima ya maka hukumar kiyaye afkuwar haɗura FRSC Kotu, bisa zargin tauye hakkin da Adam. Wannan ya faru biyo bayan tare lauyan da s**a yi a jihar Kano, tare da sauran masu ababen hawa suna yi masu tambayoyi takardu.

TUN-TU6EN HARSHE: Jarumar TikTok Babiana ta bawa Musulmi da duk 'yan Arewacin Nijeriya hakuri, akan wani bidiyo da ta sa...
07/07/2025

TUN-TU6EN HARSHE: Jarumar TikTok Babiana ta bawa Musulmi da duk 'yan Arewacin Nijeriya hakuri, akan wani bidiyo da ta saki na neman ɗaukin 'yan kudancin Nijeriya, bisa zargin ana yaɗa bidiyon tsirarcinta, a arewacin Nijeriya.

KAJI KO: Najeriya Magance Talauci Ne Gabanta Ba Gwajin Makamin Nukiliya Ba – ShettimaMataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Sh...
07/07/2025

KAJI KO: Najeriya Magance Talauci Ne Gabanta Ba Gwajin Makamin Nukiliya Ba – Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya sake jaddada kudirin Najeriya na ci gaba da bin dokar haramcin gwajin makamin nukiliya ta hanyar haɗin gwiwa da Hukumar Yarjejeniyar Hana Gwajin Makamin Nukiliya (CTBTO).

Ya ce abin da ya fi dacewa a nahiyar Afirka a halin yanzu shi ne magance manyan ƙalubalen rayuwa da ke fuskantar al’umma kamar talauci da sauyin yanayi, ba neman mallakar makaman nukiliya ba.

Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana haka ne a ranar Litinin, lokacin da ya karɓi baƙuncin Sakataren Zartarwa na Hukumar CTBTO, Dr. Robert Floyd, a wata ziyarar girmamawa da ya kai fadar shugaban ƙasa.

NOMA TUSHEN ARZIKI: Sheik Imam Junaidu Bauchi kenan ya yin da ya ziyarci gonarsa.
07/07/2025

NOMA TUSHEN ARZIKI: Sheik Imam Junaidu Bauchi kenan ya yin da ya ziyarci gonarsa.

TIRKASHI: Duk cikin waɗanda za su tsaya takara shugaban ƙasa a Jam'iyyar haɗaka ta ADC sai sun yi da ƙyar za su iya kara...
07/07/2025

TIRKASHI: Duk cikin waɗanda za su tsaya takara shugaban ƙasa a Jam'iyyar haɗaka ta ADC sai sun yi da ƙyar za su iya karawa da Ni ma ba wai shugaba Tinubu ba - Mawaƙi Rarara.

HOTUNA: Yadda mabiya mazhabar Shi'a s**a gudanar da zagayen muzaharar Ashura a Garin katsina Yau Lahadi.
06/07/2025

HOTUNA: Yadda mabiya mazhabar Shi'a s**a gudanar da zagayen muzaharar Ashura a Garin katsina Yau Lahadi.

Yadda aka gudanar da jana'izar fitaccen mai yabon Annabi Muhammadu SAW Abdullahi Shehu Ɗan Gano, yau a Gano jihar Kano.A...
06/07/2025

Yadda aka gudanar da jana'izar fitaccen mai yabon Annabi Muhammadu SAW Abdullahi Shehu Ɗan Gano, yau a Gano jihar Kano.

Allah ya jikanshi da Rahma

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Flash News.Ng posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share