15/07/2024
Kai da kake ikirarin cika dalibin ilimi, maiye ka sani dangane da iftilain da al'umma suke ciki? Abun ya shafeka ne kai tsaye ko kuwa sai an buga a labarai kake sani? In banda tsabagen son zuciya, rashin imani da raina mutane, ka kalli wanda aka sacewa mata, aka yiwa diyarsa fade, da wanda aka mayar mabaraci kace wai kada su nunawa gomnati fushinsu saboda kawai kai din kanada alaka da gomnatin ta kusa ko ta nesa. Ko shakka babu kaso mafi tsoka na malaman da s**ace kada ayi zanga zanga da wadanda ke goya masu baya, babu ko daya a cikinsu wanda matsalar tsaro ta shafa kai tsaye, kaje ka saurari malaman kauyukan da matsalolin s**a shafa kaji idan zasu haramta zanga zangar, ko su din ba malamai bane, ko kuwa dan su din basu da ko sisi kuma basu da alaka ta kai tsaye da gomnati shi yasa basu cancanchi biyayya ba. Haka kawai sai kaga mutumin da ko malamin unguwarsu bai taba gaishewa ba wai yau shine yake cewa kada a taba kimar malamai don kawai ya burge wasu tsiraru daga mabiyanshi.
Haqqun zagin malamai da yi masu rashin kunya sakacci ne, rashin ilimi ne ko kuma rashin yin aiki dashi amman haba, ka kalli mutumin da yafi karfin ci da sha a kauyensu yanzu yayi hijira ya koma mabaraci kace wai kada yayiwa gomnati bore dan kawai kana marar imani, dan neman suna, kuma dan aike. Bamu goyon bayan cin fuska da yima malamai rashin kunya amman muna tur da Allah wadai da halinsu da halinku na zaben abinda kuke yin magana akai da wanda kuke yin gum da bakinku don kawai bai shafeku ba.
Kunce wai in anyi zanga zanga matsala za'a shiga, daman kune baku cikin matsala shi yasa kuke tsoran a shigeta, ku tambayi mutanen kauye matsala kuji idan sunada suaran kwallan da zasuyi kuka ma idan an kone duka nigeriyar baki daya. daga karshe muna addu'a, duk mutumin daya bada fatawa ko ya goyi bayan fatawar da akayi abisa son zuciya, allah ya hadashi da irin iftila'in da mutanenmu na kauye suke ciki a matsayin jarabawar karshe kafin ya koma ga ubangijinmu mu duka mai adalci.