Fitila Hausa News

Fitila Hausa News Fitila Hausa gidan Sahihan Labarai da Nishadi.
(1)

Duk da gargaɗin hukumomin tsaro a Kamaru,ɗumbin jama'a sun fito kan tituna a yau Asabar don nuna rashin gamsuwar su game...
25/10/2025

Duk da gargaɗin hukumomin tsaro a Kamaru,ɗumbin jama'a sun fito kan tituna a yau Asabar don nuna rashin gamsuwar su game da yunkurin canza sak**akon zaben shugaban kasar da ake dako.

Al'ummar sun fito ne a yankin Bafoussam dake ƙasar ta Kamaru galibin su akan babura ɗauke da allunan sanarwa wasu kuma sun liƙa ganye alamun zanga-zangar Lumana.

25/10/2025

BIDIYO:Ana cigaba da kame yan adawa a ƙasar Kamaru musamman magoya bayan Chiroma Issa Bakary.

Wani faifan Bidiyo ya nuna yadda jami'an tsaro s**ayi shigar farin kaya inda s**a k**a wani madugun adawa.

YANZU-YANZU."Ka fito kayiwa al'umma bayani,me ke faruwa haka ka tsige hafsoshin tsaron kasa da rana tsaka"Jam'iyyar ADC ...
24/10/2025

YANZU-YANZU.

"Ka fito kayiwa al'umma bayani,me ke faruwa haka ka tsige hafsoshin tsaron kasa da rana tsaka"

Jam'iyyar ADC ta ƙalubalanci Tinibu.

24/10/2025

WATA SABUWA A KAMARU !!!

BIDIYO:A wani yunkuri don tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar Kamaru, jami'an tsaron kasar na rangadin neman duk inda wasu Tsoffin tayoyin mota suke inda jami'an ke tattara su tare da ƙone su.

Wannan na zaman wata hanyar hana al'umma ƙona tayoyin mota kan tituna k**ar yadda aka saba yayin gudanar da zanga-zanga,musamman a wannan lokaci da ƙasar ke ƙara ɗaukar zafi dalilin zaɓen shugaban kasar da ake jiran sak**ako.

24/10/2025

SU WANENE SABBIN HAFSOSHIN TSARO DA TINUBU YA CANZA ?

BIDIYO:Taƙaitaccen bayanin su waye Sababbin Hafsoshin Tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a yau Juma’a.

Daga shekarar 1998 zuwa yau 24/10/2025Jami’an tsaro a najeriya sun k**a ɗan gwagwarmaya (OMOYELE SOWORE) har sau 518An k...
24/10/2025

Daga shekarar 1998 zuwa yau 24/10/2025

Jami’an tsaro a najeriya sun k**a ɗan gwagwarmaya (OMOYELE SOWORE) har sau 518

An kaishi gidan gyara hali har sau 42

Anyi shari’a dashi a kotu har sau 81

Sowore yayi shari’a da gwamnoni, sanatoci, yan majalissu, jami’an tsaro, kai har da shugaban ƙasa wannan mutumin yayi shari’a

Kuma duk domin kare haƙƙin talakawan ƙasar nan

Sowore bai taɓa zuwa kotu domin kare iyalansa ba ko yan uwansa, sai dai domin baiwa al’ummar wannan ƙasar kariya.

A halin yanzu, ɗan gwagwarmaya sowore har yana farinciki idan ank**a shi, saboda abun ya zame masa jini.

Yadda wata ƙungiyar matasan Arewa, ta gudanar da taron salla da addu’a a Masallacin Sabon Gari da ke Jihar Kano, domin t...
24/10/2025

Yadda wata ƙungiyar matasan Arewa, ta gudanar da taron salla da addu’a a Masallacin Sabon Gari da ke Jihar Kano, domin taya ɗan Shugaban Ƙasa, Seyi Tinubu, murnar cika shekaru 40.

📸: Salim Umar Ibrahim

Daga Aminiya.

Tinibu bai cire Hafsoshin tsaron kasa ba saboda sun kasa samar da tsaro a Najeriya ba.Daga Abdulkadir Nafi'u Bai cire su...
24/10/2025

Tinibu bai cire Hafsoshin tsaron kasa ba saboda sun kasa samar da tsaro a Najeriya ba.

Daga Abdulkadir Nafi'u

Bai cire su ba don sun kasa Kawo karshen Boko Hamar a Arewa maso Gabas.

Tinibu bai cire Hafsoshin tsaron kasar nan ba don sun kasa kamo ko halaka Bello Turji da ire-iren sa ba dake Arewa maso yamma.

Tinibu bai cire Hafsoshin tsaron kasar nan ba don sun kasa ladabtar da masu tada kayar baya a Arewa ta Tsakiya ba musamman a Taraba,Neja da jihar Filato.

Tinubu ya tsige manyan Hafsoshin tsaron kasar nan don sakacin su na kasa tsare ƙimar gwamnatin sa inda wasu daga jami'an tsaro har suke yunkurin juyin mulki wa gwamnatin sa.

Buƙatar kansa ce tasa ya Tumɓuke manyan Hafsoshin tsaron kasar ba don maslaha da neman zaman lafiya ga miliyoyin al'ummar Najeriya ba.

"KU FITO DON NUNAWA DUNIYA BAMU YADDA DA MURƊE ZAƁEN KAMARU BA"Madugun adawa na kasar Kamaru Chiroma Issa Bakary yayi ki...
24/10/2025

"KU FITO DON NUNAWA DUNIYA BAMU YADDA DA MURƊE ZAƁEN KAMARU BA"

Madugun adawa na kasar Kamaru Chiroma Issa Bakary yayi kira ga kafutanin al'ummar kasar Kamaru da su fito zanga-zanga a Ranar Lahadi Mai zuwa don nunawa duniya rashin gamsuwar su ga yunkurin murɗe zaɓen shugaban kasar da gwamnatin kasar ke neman yi bayan q zahiri al'umma sunyi zaɓen cikin lumana sun kuma zaɓi ra'ayin su.

shugaban kasar Kamaru PAUL BIYA ya kwashe shekaru 43 matsayin shugaban kasar,ya kuma nemi wa'adi na 7 a shugabancin kasar wato wasu ƙarin shekara 8 yana shugabancin kasar.

Paul Biya mai shekaru 92 a duniya ga dukkan alama yana fatan cika shekaru 100 a karagar mulkin kasar.

Shugaba Tinubu ya sauya manyan hafsoshin tsaron NajeriyaShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauye a manyan...
24/10/2025

Shugaba Tinubu ya sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauye a manyan muk**an rundunonin tsaron ƙasar, a wani yunkuri na ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.

A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya fitar a yau Juma’a, 24 ga Oktoba 2025, an bayyana cewa an nada Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Hafsoshin Tsaron Najeriya (Chief of Defence Staff) domin ya maye gurbin Janar Christopher Musa.

Haka kuma, an nada Manjo Janar W. Shaibu a matsayin sabon Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, yayin da Air Vice Marshall S.K. Aneke ya zama sabon Shugaban Rundunar Sojin Sama, da kuma Rear Admiral I. Abbas a matsayin sabon Shugaban Rundunar Sojin Ruwa.

Shugaban Sashen Tsaro na Leƙen Asiri (Chief of Defence Intelligence), Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, zai ci gaba da rike mukaminsa.

Shugaba Tinubu ya jinjinawa tsofaffin hafsoshin tsaron, musamman Janar Christopher Musa, bisa jajircewarsu da kishin ƙasa a lokacin da s**a yi wa ƙasar hidima.

Ya kuma umarci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun nuna kwarewa, tsantseni da haɗin kai domin ƙarfafa rundunonin tsaron Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a fadin ƙasar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa sabbin nade-naden sun fara aiki nan take.

YANZU-YANZU: Tinubu ya sauke Janar Christopher Musa daga mukamin babban hafsan tsaron Najeriya, ya maye gurbinsa da Jana...
24/10/2025

YANZU-YANZU: Tinubu ya sauke Janar Christopher Musa daga mukamin babban hafsan tsaron Najeriya, ya maye gurbinsa da Janar Olufemi Oluyede.

Shin ko me kuke zargin ya kawo wannan sauye-sauyen da rana tsaka ??

LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima da sauran al'umma s**a...
24/10/2025

LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima da sauran al'umma s**a gabatar da sallar Juma'a yau a masallacin Fadar Shugaban Ƙasa dake A*o Rock. Limamin masallacin Sheikh Abdulwaheed Suleiman ne ya jagoranci sallar.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fitila Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share