
02/08/2025
Sarkin Katsina ya naɗa sabbin hakimai 6 a masarautar sa
Masarautar Katsina ta tabbatar da nadin sabbin Hakimai shida, ciki har da Muhammad Dikko Umar Radda, ɗan Gwamnan Jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda, wanda aka nada da sarautar Hakimin Radda.
Sanarwar nadin ta fito ne daga sakataren masarautar Katsina, Alhaji Bello M. Ifo (Sarkin Yakin Katsina), inda ya bayyana cewa an amince da nadin sabbin hakiman a ranar 2 ga watan Agusta, 2025.
Ga jerin sabbin Hakiman da aka tabbatar kamar haka:
1. Alhaji Sanusi Kabir Usman – Hakimin Shinkafi
2. Alhaji Ahmad Abdulmumini Kabir Usman Dan-Majen Katsina (Hakimin Dankama)
3. Sanata Hadi Sirika – Marusan Katsina (Hakimin Shargalle)
4. Alhaji Abubakar Dardisu, FCNA, Mni – Hakimin Muduru
5. Alhaji Gambo Abdullahi Dabai – Dausayin Katsina (Hakimin Dabai)
6. Alhaji Muhammad Dikko Umar Radda (Gwagwaren) Katsina (Hakimin Yadda)
Sanarwar ta ƙare da fatan alheri da zaman lafiya ga sabbin masu sarautar, tare da addu’ar Allah ya ba su nasara a jagorancin al’umma.
“Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, amin,” inji Alhaji Bello M. Ifo.