
06/06/2025
Tinawa da malamanmu na boko ' nasan idan nace duk dalibansa mu daga hannu β za'a samu dayawa
A lokacinsa: mukasan idan dalibi baije makaranta ba kwana biyu ' za'a tura yan ajinsa suje su kamosa duk inda yake ' abiyo cikin gari anata wake wake
A lokacinsa : idan anyi suna gidan su dalibi yakanyi kwalliya yazo makaranta domin kawo goron suna wajen malam
A lokacinsa : yake shiryawa dalibai wasan makaranta duk shekara inda ba karamin murna dalibai keyiba ' kuma dalibi zaikara kokari acikin aji domin kada ayi babu sunansa acikin masu yin wasa na musamman wanda sai masu kokari sukeyi
A lokacinsa : mafi yawanmu muka fara daukan hoto ' domin har kofar yamma muke zuwa muzauna domin ganin tafiyarsa birni da dawowarsa idan ankai wankin hotoπ
A ranar da'aka bamu hotuna ranar murnace ba k**a hannun yaro ' kuma irin ajiyar dazamuyiwa hoton ko kudi sai haka
A lokacinsa : aka sami babbar alaka tsakanin malaman makaranta da iyayen 'yara' domin iyayen yara suna ziyartar makaranta lokaci zuwa lokaci ' idan dalibi yaga mahaifinsa yazo makaranta yakan tsorata kuma yanajin dadi ' wannan zaisa gobe bazaiyi kokarin rashin zuwa ba
A lokacinsa: muka fara ganin manya manyan mutane suna kai mana ziyara a wannan makarantar primary
A lokacinsa: munyi kwalliya muna jiran ziyarar shugaban kasa shagari ' bayan malam baballe ya dauki tsawon lokaci yana koya mana yadda zamu tΓ‘rbeshi idan yazo makaranta
Kash: sai shagari yayi kwanar shagari yakoma birni saboda wasu dalilai marasa tushe da'aka gayamisa daga wannan ziyarar tashar mota tasamo asalin wannan suna ' bazamu taba mantawa ba had yanzu
A lokacinsa: yakawo martabawa tsakanin malamai dz dalibai ' malamin ko da wasa bazaiyi wani abu marar kyau acikin gari ba don kada dalibinsa yagani
Mukuma dalibai ko wajen kida zamuje idan munsan unguwar akwai malaminmu a unguwar to ta haramta muje kallo don kada a ganmu
Dasauran abubuwa dayawa da wannan bawan Allah headmaster nawa yakawo mana a wannan makaranta kuma har yanzu yana cikin rayuwarmu
Ya Allah π kajikan wannan bawan Allah da gafara ' yakuma albarkaci zuri'arsa amin π
βοΈYau Ibrahim Dank**a
06-JUNE-2023