21/05/2026
🛑 Budurci: Ilimi Maimakon Zargi"
💡 A yau za mu duba wasu daga cikin abubuwan da mutane suke dauka game da budurci alhali ba gaskiya ba ne a ilimin lafiyaa
🛑 1. “Dole Sai Jini Ya Fito a Daren Farko”
❌ Wannan ba gaskiya ba ce.
💥 Wasu matan ba sa zubar da jini saboda:
👉 Yanayin halittarsu.
👉 Fatar “Hymen” tana da laushi sosai.
👉 Wasanni ko wasu abubuwa sun taba fatar tun farko.
👉 Rashin jini ba hujja ba ce cewa mace ta taba namiji.
🛑 2. “Likita Zai Iya Gane Kowace Mace Mai Budurci”
❌ Ba koyaushe hakan yake yiwuwa ba.
💥 Kwararrun likitoci sun bayyana cewa:
Yanayin “Hymen” ya bambanta daga mace zuwa mace.
Ba a iya tabbatar da tarihin saduwar mace ta hanyar dubawa kawai.
🛑 3. “Budurci Shi Ne Kadarar Darajar Mace”
❌ Darajar mace ta fi tsaya wa:
💥 Tarbiyya
💥 Mutunci
💥 Addini
💥 Halayya mai kyau
💥 Budurci kadai ba shi ne ma’aunin kimar mace ba.
🛑 4. “Duk Mace Mai Wasanni Ta Rasa Budurci”
❌ Wannan ma kuskure ne.
💥 Wasanni na iya shafar fata a wasu mata, amma hakan ba yana nufin mace ta san namiji ba
💥 Sako ga Iyaye da Ma’aurata
🗨️ Mu rungumi ilimi maimakon zargi.
🗨️ Mu kare mutuncin mata da kalamai masu kyau.
🗨️ Fahimta tsakanin ma’aurata tana gina zaman lafiya da amana.
👉 Ilimi mai inganci yana hana yanke hukunci cikin kuskure.
—