07/07/2026
JANA’IZAR AS-SAYYID KHAMENE'I (Q.S) TA ISO IRAQ, NAJAF.
Da yammacin yau Talata ne jirgin da ya ɗauko Janazar Ayatullah Asshahid Assayyid Khamene'i (Q.S) ya sauka a filin jirgi na birnin Najaf, Iraq.
Tun shekarar 1957 dai ne Assayyid Khamene’i ya ziyarci Iraq, sannan yana Matashi ɗan shekaru 18, inda ya samu albarkar ziyarar Haramomi masu albarka ciki har da Najaful Ashraf inda Amirul Mumineen Imamu Ali (A.S) yake, da kuma Karbala mai tsarki inda Imam Hussain (A.S) yake.
A wancan karon Asshahid ya zo ne da ƙafafunsa a harkar neman ilimi da kuma ziyarori, amma yau Talata 07/07/2026 an iso da shi ɗauke a kafaɗu da hannaye a matsayin Shahidi, inda zai sake gabatar da ziyararsa a karo na biyu, ya Allah!
Kenan daga waccan shekara ta 1957 zuwa 2026 ɗin da muke ciki shekaru 69 rabonsa da Iraq.
Sayyid Khamene’i (Q.S) a duk shekara idan Arba’eena ya zo ana jiyo shi yana kewa da kwaɗayin zuwa ziyaratul Arba'een, sai dai kash!! Yanayi ba ya ba shi shi dama saboda mas'uliyar da ke kansa da kuma halin tsaro.
Amincin Allah ya tabbata a gare ka Jagora kuma baya goya marayu jikan Abul Yatama Ali (A.S).
#العزاء
ASEEL
07072026