
15/04/2023
*HABA HARRIS YAUSHE KA MANTA DA KANKA?*
*KASHI NA DAYA (1)*
Bismihi Ta'ala, Wasallallahu Ala Muhammad Wa Ahli Muhammad Wa'ajjil Farjahum Wansur Maulana Zakzaky (H).
Kamar Yanda Taken Rubutun Yake " Haba Haris Yaushe Kamanta Da Kanka" Harda da Za'a Rudeka Da Propaganda? Eh Mana Propaganda ne Kawai, Yaushe Mujaddadi Zai Assasa Abu Kuma Yazo Ya Rusa Saboda Da Matsala?
Akwai Wani Lokaci Da Malam Haruna Abbas Yasamu Su Jagora (H) Akan Cewa Za'a Rusa Yan Jaishi Mahadi Sai Su Sayyed (H) S**ace Mai Yasa Sai Malam Haruna Abbas Yace Matsaloli Sunyi Yawa Sai Su Allama Zakzaky (H) S**ace "Indai Hakane Ai Gwagwarmayan ma Sai a Rusheta Saboda Itama Akwai Matsaloli acikinta", S**a Kara Dacewa Ai Ita Matsala Ba'a Rabuwa Da Ita Ana Magance Wanda Za'a Iya Magancewa ne Saura Kuma a Koyi Tafiya Da Ita Domin Matsala kam ba'a Rabuda da Matsala."
To Yaushe Kuma Wani Zaice Maka Wai Don Matsalolin Dake Cikin Aikin Harisanci Sai Jagora (H) Su Rusheta?
Ga Abinda Su Sayyed (H) S**a Fadin Irin Makircin Jahiliyya Akan Aikin Harisanci Da Bakinsu Mai Albarka Wanda Kowa yasani, Suke Cewa " To Yanzu Yaya Za'ayi a Rusa Aikin Harisancin Nan Ne? Ayi Penetrating ne A Kutsa Cikinsu Saboda Haka akwai Jami'an Tsaro acikiku dayawa, Suna Dayawan Gaske.
Wani Abunda Shi Jami'in Tsaro Bai Saniba Shine a lokacin Da aka Daukeshi aiki ana daukanshi a Hoto (ID Card) Akwai ID Card dinshi kuma ana sawa a Computer, Saboda Haka Zamu iya Samu, Munama dawasu.
To Yaushe Wani Dan Bani Na Iya Zaice Maka Wai Don Akwai Jami'an Tsaro Cikin Aikin Harisanci Jagora (H) Sun Rushe Aikin Kuma Ka Yarda? Wani Irin Tarbiyyane Hurras Bamu Samu A Wajen Allama Zakzaky (H) Ba A Wannan Tafiyar? Meyene Yarage Sayyed Zakzaky Bai koya Manaba Ko Kuma Bai Fada Mana Ba Wanda Zaisa Propaganda Makiya Yayi Tasiri Har Mu Fitinu Muyi Sanyi Da Aikin Da Aka Sanmu Dashi?
Duk Wayanda Sayyed Zakzaky (H) s**a Gana Dasu Suwaye ne S**a Yiwa Su Malam (H) Dole Kafin Aka Ganadasu? Duk Wayanda Aka Gana Dasu Lokacin Daya Dace A Gana Dasu Ne .