SUBEB Chairman Media Crew

SUBEB Chairman Media Crew Executive Chairman SUBEB

A yanzu haka Gwamnatin Jihar Katsina ta fara aikin fadada sabuwar Makarantar Firamaren Kabir Magaji Kambarawa dake cikin...
28/07/2025

A yanzu haka Gwamnatin Jihar Katsina ta fara aikin fadada sabuwar Makarantar Firamaren Kabir Magaji Kambarawa dake cikin Garin Katsina.

Idan za'a tuna, kwanakin baya Gwamnatin Dr. Dikko Umaru Radda ta samar da sabuwar Makarantar, domin rage cinkoson Ɗalibai a wasu Makarantun Firamaren dake yankin, a Karamar Hukumar Katsina.

27/07/2025
16/07/2025

Sakon ta'aziya....

A madadin Shugaban Hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar Katsina (SUBEB) Dr. Kabir Magaji Gafiya ke miƙa sakon ta'aziya ga iyalai da yan'uwa, da sauran al'ummar Jihar Katsina, bisa ga rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Dr. Kabir Magaji ya bayyana rashin Marigayin a matsayin Babban rashi, ga al'ummar Nijeriya, dama Duniya baki ɗaya.

Kazalika, ya miƙa sakon ta'aziya ga Gwamna Malam Dikko Radda na Jihar Katsina, da sauran al'ummar Jihar Katsina baki ɗaya, yana mai addu'ar neman rahamar Ubangiji ga Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

A Safiyar Yau Lahadi, Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Gafiya ya ziyarci Garin Dank**a, domin yin ta'aziya ga Dir...
06/07/2025

A Safiyar Yau Lahadi, Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Gafiya ya ziyarci Garin Dank**a, domin yin ta'aziya ga Diraktan Sashen kula da horas da Malamai na Hukumar Alh. Ma'aruf Musa Dank**a, bisa ga rasuwar ɗaya daga cikin Ya'yan sa.

An gudanar da Karatun Alqur'ani Maigirma, da addu'oi na musamman, domin ta ya Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Ga...
05/07/2025

An gudanar da Karatun Alqur'ani Maigirma, da addu'oi na musamman, domin ta ya Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Gafiya murnar cika Shekaru biyu, da fara jagorancin Hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar Katsina.

Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Gafiya ya hannanta takardar k**a aiki, ga sabbin sakatarorin ilimin Karamar Huku...
03/07/2025

Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Gafiya ya hannanta takardar k**a aiki, ga sabbin sakatarorin ilimin Karamar Hukumar Kurfi Malam Bawa Magaji, da kuma Hajiya Maryam Babajo a Karamar Hukumar Funtua.

Wannan abokin zama na ne. Malamin Firamare ne, amma zai yi matuƙar wahala son zuciya ya hana shi zuwa wurin aiki. Ba zan...
27/06/2025

Wannan abokin zama na ne. Malamin Firamare ne, amma zai yi matuƙar wahala son zuciya ya hana shi zuwa wurin aiki. Ba zan ce baya fashi ba, amma zai yi wahala ka same shi ya ƙi zuwa makaranta. Tafiyar ta kai kusan kilomita 20 da inda yake koyarwar, amma kullum a haka yake zuwa baya fashi (sai dai idan da wani dalili). Da wannan nake kafa maka hujja cewa: ƙarancin albashi ba shi da wata alaƙa da ƙin zuwan ka wurin aiki. Agreement aka yi da kai sannan ka sa hannu. Idan ba zaka je ba kawai ka ajiye aikin kowa ya huta. Allah ya yawaita mana irin waɗannan malaman a makarantun mu. Mu kuma Allah ya shiryar damu mu chanza ɗabi'un mu.

Daga Shafin Salisu Yakubu

Domin inganta jin dadi da walwalar Ma'aikatan sa, Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Gafiya ya samar da Motar hawa,...
26/06/2025

Domin inganta jin dadi da walwalar Ma'aikatan sa, Shugaban Hukumar SUBEB Dr. Kabir Magaji Gafiya ya samar da Motar hawa, ga sabon Daraktan Sashen kula da harkokin koyarwa wato Alhaji Habibu Yusuf Daura.

Barka da Sallah..
06/06/2025

Barka da Sallah..

05/06/2025

Na daga Sunna ta Allah duk lokacin ka gode sai ya ƙara maka, amma irin halin mu ya sanya Shekarar bana ji kake shiru, domin mu koyi darasi...

29/05/2025

Sakon taya murnar cika Shekaru biyu, daga Shugaban Hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar Katsina (SUBEB) Dr. Kabir Magaji Gafiya.

Congratulatory Message!On behalf of the Katsina State Universal Basic Education Board (SUBEB), I extend heartfelt congra...
28/05/2025

Congratulatory Message!

On behalf of the Katsina State Universal Basic Education Board (SUBEB), I extend heartfelt congratulations to His Excellency, Governor Malam Dikko Umar Radda, and His Excellency, Deputy Governor Malam Faruk Lawal Jobe, on reaching the mid-term of their administration.

In just two years, our state has witnessed remarkable and lasting achievements across all sectors under your exemplary leadership.

Your visionary governance and steadfast commitment to the development of Katsina State continue to inspire progress and optimism. At SUBEB, we remain fully committed to supporting your administration’s efforts in transforming basic education for the benefit of our children and future generations.

Congratulations once again on this significant milestone.

Signed;
Kabir Magaji Gafiya,
Executive Chairman,
Katsina State Universal Basic Education Board (SUBEB)

29 May, 2025.

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SUBEB Chairman Media Crew posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share