
19/07/2025
Ƙungiyar Gidauniyar Uwar gidan kwamishinan muhallin jihar Katsina Hajiya Barista Naja'atu Hamza Sulaiman ta shirya wani babban gangamin wayar wa mata kai game da cutar kyanda, kamar yadda Hajiya Zulaihatu Dikko Radda ta bayar da umurni
A yau Asabar 19 July 2025, ƙungiyar Gidauniyar Uwar Gidan Sadaukin Kasar Hausa Hajiya Barista Naja'atu, daga kungiyoyin mata da matasa masu son faɗaɗa tafiyar gidan Wambai, sun shirya wani babban taro na tara dumbin mata don wayar masu da kai game da sha'anin lafiya, musamman rigakafin cutar kyanda.
A lokacin gabatar da jawabin nata, shugabar kungiyar Malama Ladidi Umar ta bayyana cewa sun kira wannan taron ne bisa kiran da Uwar gidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihatu Dikko Radda ta yi na a wayar wa mata kai game da cututtukan ƙananan yara, musamman kan rigakafin da za a yi nan da wata biyu na cutar kyanda ga ƙananan yara
Ita ma a nata jawabin Uwar gigan shugaban karamar hukumar Faskari, ta bayyana muhimmancin rigakafi ga ƙananan yara, inda ta shawarci mata da cewa da zarar an fara gudanar da wannan allura kowace ta tabbatar an yi wa yayanta
Ita kuwa jawabin nata shugabar Gidauniyar Hajiya Barista Naja'atu da Hajiya Rukayya Sani ta wakilta, ta ce ta tara wannan babban gangamin ne domin isar da sakon H.E Hajiya Zulaihatu Dikko Radda da ta umurci a wayar ma mata kai game da amfani da kuma illar rashin yi wa yara rigakafin cutar kyanda
Masana harkar lafiya sun kuma yi wa matan jawabai da s**a shafi ingancin lafiyar ƙananan yara a lokacin gudanar da taron
A lokacin gudanar da taron an kuma shirya yar kwarya-kwaryar addu'a ta nema wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari gafara da rahamar Allah, sannan kuma an shirya wa mahalarta taron dirama mai ƙunshe da darasin illar rashin yi wa yara rigakafin cutar kyanda, wanda hakan na sa su da ƴaƴan nasu su zama abin ƙyama a cikin al'umma
Ibrahim M Bawa CEO Katsina Daily News