25/08/2025
Shugaban Karamar Hukumar Katsina Ya Jagoranci Ziyarar Gani-da-Ido a Yankunan da ke Fama da Barazanar Zaizayewar Ƙasa
Da yammacin ranar Lahadi, 24-08-2025, Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin gudanar da ziyarar gani-da-ido a wasu yankuna da ake hasashen ambaliyar ruwa da zaizayewar ƙasa ka iya shafa.
Ziyarar ta kasance wani mataki na gaggawa da nufin tantance halin da ake ciki kai tsaye, tare da gano hanyoyin da s**a dace na ɗaukar matakan kariya na nan take da na dogon lokaci domin kare rayuka, dukiyoyi da kuma bunƙasa tattalin arzikin al’ummomin da abin ya shafa.
Unguwannin da aka ziyarta sun haɗa da Masoya Annabi Quarters da ke kan hanyar Batsari a cikin mazabar Wakilin Yamma II, Rahamawa ‘Yar Yara a Wakilin Kudu III, Mani House a Wakilin Kudu II, Shinkafi da Gezawa a Shinkafi A, Kwado a Shinkafi B, da kuma yankin bayan Sakatariyar ƙaramar hukumar Katsina da ke cikin mazabar Wakilin Gabas I.
A cikin tawagar da ta raka shugaban akwai Sakataren ƙaramar hukumar Katsina, Daraktan Sashen Ayyuka, Shugaban Majalisar Kansiloli wanda shi ma Kansila ne na Shinkafi B, tare da kansilolin Wakilin Yamma II, Wakilin Gabas I da Wakilin Kudu III. Haka kuma, ‘yan jarida da wasu daga cikin masu taimaka wa shugaban sun halarta.
Yayin tattaunawa da al’ummar yankunan, Hon. Miqdad ya tabbatar da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar za ta ɗauki matakan da s**a dace tare da isar da rahoton ƙorafe-ƙorafen jama’a zuwa ga hukumomin da abin ya shafa. Ya jaddada cewa ba za su yi kasa a guiwa ba wajen fuskantar ƙalubalen muhalli, domin kare lafiyar al’umma, tsaron dukiyoyinsu da kuma tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a cikin ƙaramar hukumar.
Zaharaddeen Muazu Rafindadi
Sakataren Yada Labarai na Shugaban Karamar Hukumar Katsina
25/08/25