08/03/2025
Bamu Taba Yin Sanatan Da Ya Kula Da Rayuwar Mu Ba Kamar Audu Soja - Cewar Laftanal Hudu Usman
Mataimaki na Musamman ga Gwamna Dikko Radda akan masu bukata ta musamman Laftanal Hudu Usman(Rtd) ya bayyana cewa basu taba samun sanatan da ya kula da rayuwar su ba kamar Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua.
Laftanal Hudu Usman mai ritaya ya furta hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin sana'oi da kekunan guragu da sanatan ya samar ga masu bukata ta musamman.
Wadanda s**a amfana da tallafin su sama da 50 an zabo su ne daga Kananan Hukumomi 11 na Shiyyar Katsina ta Tsakiya.
Kayayyakin da sanatan ya samar a matsayin tallafin sana'oin sun hada da Kekunan Dinki da Injinan Murza Taliya da Kekunan Guragu gami da tallafin kudi ga dukannin wadanda s**a amfana.
Laftanal Hudu Usman wanda ya wakilci Gwamna Dikko Radda a wurin taron,ya bukaci wadanda s**a amfana akan su yi kyakkyawan amfani da tallafin.
Accuracy News Hausa ta tsinkaye shi yana mai kira garesu akan su sakawa karamcin ta hanyar yin addu'a ga samun nasarar Sanatan da sauran shuwagabanni.
Tunda farko wakilin Sanatan wanda kuma shine Shugaban Hukumar KASSAROTA Major Yahaya Rimi mai ritaya ya ce,tallafin na daga cikin cikon alkawarin yakin neman zaben Sanatan na inganta rayuwar masu bukata ta musamman.
Major Yahaya Rimi mai ritaya ya ce tunda farko sai da aka horas da wadanda s**a amfana akan sana'ar dinki da sabulun ruwa da sarka da kiwon kaji da sauran sana'oi.
Daga nan sai ya nanata kudirin Sanatan na cigaba da bullo da shirye-shirye da zasu inganta rayuwar al-ummar Mazabar tashi.
Sauran wadanda s**a maganta a lokacin taron sun hada da wakilin Ma'aikatar Jin Kan Al'umma da mataimaki na Musamman ga Sanatan.
Wasu daga cikin wadanda s**a amfana sun yabawa Sanatan akan kula da rayuwar su,sai s**a yi mashi addu'ar fatan nasara.