Hausa Daily Report

Hausa Daily Report Hausa Daily Report na kawo muku sahihan labarai na yau da kullum a Hausa.

28/04/2026

VIDEO: ABIN MAMAKI: Wani abin mamaki a ƙasar Indiya. Wani mutum ya tono gawar ’yar’uwarsa daga kabari domin kai ta banki ya tabbatar da mutuwarta.

A wani lamari da ba a saba gani ba, wani mutum mai shekaru sama da 50 daga jihar Odisha ta ƙasar Indiya ya tono ragowar gawar ’yar’uwarsa daga kabarinta ya kai ta banki domin ƙoƙarin tabbatar da mutuwarta.

Mutumin ya yi ƙoƙarin cire kuɗi rupee dubu 20 (kimanin dala 200) daga asusun ’yar’uwarsa, amma hakan ya ci tura duk da bankin ya riga ya sanar masa cewa ta mutu.

A cewar mutumin da ya shaida wa ’yan sanda, bankin bai yarda da maganganunsa kan mutuwar ’yar’uwarsa ba, lamarin da ya sa ya aikata wannan abin mamaki.

Rahotanni sun nuna cewa ’yar’uwar tasa ta rasu ne a watan Janairun wannan shekara.

28/04/2026

Yadda CCTV Camera ta tona asirin masu kwacen waya a cikin unguwanni.

Allah ya kara tona musu Asiri...

Najeriya na bukatar tsari da ingantattun manufofi kan fasahar zamani - Sarki Sanusi Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi ...
28/04/2026

Najeriya na bukatar tsari da ingantattun manufofi kan fasahar zamani - Sarki Sanusi

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa Najeriya na bukatar gaggawar samar da ingantaccen tsari da tsarin manufofi na ƙasa domin amfani da sabbin fasahohi, musamman fasahar AI, wajen ci gaban ƙasa mai dorewa.

Sanusi ya bayyana haka ne a wajen taron karo na 8 na Committee of Pro-Chancellors of State-Owned Universities in Nigeria da aka gudanar a Kano, mai taken: “Unlocking the Potentials of Artificial Intelligence: University Governance, Internationalization and Rankings."

Ya ce ya zama dole jami’o’in Najeriya su jagoranci samar da tsarin AI na ƙasa, yana mai jaddada cewa bai k**ata makarantu su tsaya kawai ga koyarwa da bincike ba, ya k**ata su shiga gaba wajen tsara manufofin da za su taimaka wa ci gaban ƙasa.

Sarkin ya kuma yi gargadin cewa Najeriya na iya yin baya idan ba ta tashi da wuri ba, yayin da wasu ƙasashe k**ar Ghana s**a riga sun fara aiwatar da cikakken tsarin AI da ke mayar da hankali kan horar da matasa, tattara bayanai da sauya tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa jami’o’i suna da muhimmiyar rawa a matsayin ginshiƙan al’umma, yana mai cewa ya k**ata su shiga cikin tattaunawar ƙasa kan shugabanci, tattalin arziki da fasaha.

A nasa jawabin, shugaban COPSUN, Ayodeji Omole, ya ce taron ya mayar da hankali kan bukatar haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin magance kalubalen da jami’o’in jihohi ke fuskanta.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ta ba ilimi muhimmanci a matsayin ginshiƙin ci gaba, tare da zuba jari a kayan aiki, koyon zamani da bincike domin inganta jami’o’in jihar.

Majalisar Wakilai ta amince da bukatar Tinubu ta ciyo bashin dala miliyan 516 Majalisar Wakilai ta ƙasa ta amince da buk...
28/04/2026

Majalisar Wakilai ta amince da bukatar Tinubu ta ciyo bashin dala miliyan 516

Majalisar Wakilai ta ƙasa ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓo bashin waje na dala miliyan 516,333,007 domin tallafa wa aikin gina wasu sassan titin Sokoto zuwa Badagry.

Majalisar ta amince da bukatar ne a zaman ta na ranar Talata, bayan gabatar da rahoto daga Abdullahi Rasheed, mataimakin shugaban kwamitin kula da tallafi, basuss**a da harkokin bashi.

An bayyana cewa wannan bashi zai taimaka wajen inganta aikin babban titin Sokoto–Badagry, wanda ake sa ran zai haɗa yankuna da dama tare da bunƙasa harkokin sufuri da tattalin arziki.

DA ƊUMI-ƊUMI: Rundunar Sojin ƙasar Mali, tare da takwarorinsu na Burkina Faso da Nijar a ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwar...
28/04/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Rundunar Sojin ƙasar Mali, tare da takwarorinsu na Burkina Faso da Nijar a ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwar AES, sun ƙaddamar da wani zazzafan farmaki domin mayar da martani ga ƴan ta’ad-da. Inda s**a ka$he masu yawa s**a k**a wasu kuma s**a kwace karfin ikon yankunan k**ar yadda rahotanni s**a bayyana.

Matatar Man Dangote Na Bada Tallafin Mai a Najeriya — Jami’in KamfaninWani babban jami’i a kamfanin Dangote Group ya bay...
28/04/2026

Matatar Man Dangote Na Bada Tallafin Mai a Najeriya — Jami’in Kamfanin

Wani babban jami’i a kamfanin Dangote Group ya bayyana cewa Matatar Man Dangote na rage farashin man fetur da dizel da yake sayarwa a kasuwar Najeriya, k**ar wata hanya ta tallafi.

Jami’in ya ce wannan mataki na taimakawa wajen rage nauyin farashi ga masu amfani da mai, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tashin farashin mak**ashi.

Ya ƙara da cewa matatar na ƙoƙarin tabbatar da wadatar mai a cikin gida, tare da rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Sai dai wasu masana na ganin cewa irin wannan tsarin rage farashi na iya zama na ɗan lokaci ne, dangane da yadda kasuwar mai ke tafiya da kuma tsadar samarwa.

RASUWAR MATASHI A IBADAN: ANA ZARGIN ‘YAN SANDA DA HALLAKA SHI A AKINYALEInnalillahi wa inna ilaihi raji’un.Wani matashi...
28/04/2026

RASUWAR MATASHI A IBADAN: ANA ZARGIN ‘YAN SANDA DA HALLAKA SHI A AKINYALE

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.
Wani matashi mai suna Sani Salisu Basaura ya rasa ransa a wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a yankin Akinyale da ke jihar Oyo, a birnin Ibadan.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin yana kan hanyarsa ta neman abinci ne a ranar Juma’a da ta gabata, sai wasu jami’an ‘yan sanda s**a k**a shi. Shaidu sun ce an ci gaba da dukansa har sai da ya suma, lamarin da daga bisani ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
An ce jami’an da ake zargi suna aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Kara Police Station da ke yankin Akinyale.

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda ake kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da daukar matakin da ya dace kan wadanda aka samu da laifi.

Haka kuma, an bukaci a tabbatar an ba iyalan mamacin hakkinsu da kuma samar da adalci.
A karshe, an yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Rahoto daga: Ayuba Aliyu Basaura
Ranar: 27/04/2026

Gwamnatin Najeriya ta jinjinawa Saudiyya bisa samar da gurbin karatu ga daliban Najeriya 50 a fannin man feturGwamnatin ...
28/04/2026

Gwamnatin Najeriya ta jinjinawa Saudiyya bisa samar da gurbin karatu ga daliban Najeriya 50 a fannin man fetur

Gwamnatin Tarayya ta jinjina wa Masarautar Saudiyya bisa samar da gurbin karatu na kyauta ga daliban Najeriya su 50 domin karantar fannin man fetur da ma’adanan kasa.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Bin Mohammed Al-Balawi, wanda ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026.

Ministan ya bayyana cewa wannan tallafin karatu ya zo daidai da burin gwamnati na bunkasa ilimi da kwarewa a fannonin da s**a shafi tattalin arzikin kasa. Ya ce wannan ba gurbin karatu ba ne kawai, a’a, wani babban jari ne da za a zuba wa matasan Najeriya.

"Wannan mataki zai samar da kwararrun da Najeriya ke bukata a masana’antun man fetur da ma’adanan kasa," in ji Ministan.

Ya kuma kara da cewa an tsara shirin ta yadda dalibai 50 za su rika amfana a duk shekara, wanda hakan zai tabbatar da dorewar shirin na dogon lokaci.

A nasa bangaren, Jakada Al-Balawi ya sanar da cewa gurbin karatun ya fito ne daga Jami’ar Man Fetur da Ma’adanai ta King Fahd (KFUPM). Ya bayyana cewa tallafin ya hada da Biyan kudin makaranta (Tuition), Tikitin jirgin sama na zuwa da dawowa, Wajen kwana kyauta, da Alawus din dake shiga hannu a kowane wata.

Jakadan ya jaddada cewa wannan kokari na nuna kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa Saudiyya da Najeriya ginshikan tattalin arziki ne a yankunansu wadanda ke da damar bunkasa huldar kasuwanci a tsakaninsu.

Ministan ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana jimamin Najeriya game da takaddamar dake faruwa a yankin tekun Gulf, inda ya mika sakon goyon bayan Najeriya ga kasar Saudiyya. Ya bayyana fatan samun zaman lafiya da kuma daidaita duk wata matsala ta hanyar diflomasiyya.

A karshen zaman, Ministan ya tabbatar wa jakadan cewa Najeriya za ta gaggauta aiwatar da sauran yarjeneniyoyin da aka kulla da Saudiyya, ciki har da wadanda s**a shafi fannin yada labarai da sauran sassa.

Ziyarar ta samu halartar Babban Sakataren ma'aikatar, Dr. Binyerem C. Ukaire, da wasu manyan daraktoci na ma'aikatar yada labaran.

Harin daba na Farm Centre: Take-taken APC shi ne amfani da daba don razana masu zabe kuma sai mun kare ƙuri'ar mu - Arza...
28/04/2026

Harin daba na Farm Centre: Take-taken APC shi ne amfani da daba don razana masu zabe kuma sai mun kare ƙuri'ar mu - Arzai

Hon. Abba Arzai Dala, dan takarar Majalisar Tarayya a karkashin jam’iyyar ADC a ƙaramar hukumar Dala, ya nuna damuwa kan ƙaruwar amfani da ƴan daba da ya zargi ƴan jam'iyyar APC da yi a jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya Litinin ne wasu ƴan daba da ake zargin sun zo wucewa a tawogar wani ɗan siyasa su ka daka wawa akan kayan ƴan kasuwar waya ta Farm Centre a jihar Kano, inda s**a Farfesa teburin tare da kwashe wayoyin ƴan kasuwa.

Sai dai a wata sanarwa da ya aike wa Daily Nigerian Hausa, Arzai ya zargi dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, A. A. Zaura da yawo da yan daban da har su ka kai farmaki a kasuwar ta Farm Centre.

Arzai, wanda shine shugaban Kwankwasiyya Amanar Talaka Movement, ya kuma sake buga misali da ɗan majalisar wakilai na mazaɓar ƙaramar hukumar Dala, Ali Sani Madaki da amfani da yan daba a wajen kaddamar da wasu aiyuka a mazaɓar, inda yayi zargin cewa duk hakan wata barazana ce da yan APC din ke yi ga ƴan adawa.

Ya kara da cewa duk da wannan barazana, to al'umma na za su bari a musu sakiyar da ba ruwa ba a ranar zaɓe, inda ya tabbatar da cewa za su yi iya ƙoƙarin su na tabbatar da kare ƙuri'un su.

"A cikin ‘yan kwanakin nan, al’ummar Jihar Kano musamman a karamar hukumar Dala sun fara fuskantar wasu al’amura masu tayar da hankali da ke nuna yadda harkokin daba ke kara samun gindin zama a harkokin siyasa. Wadannan abubuwa sun janyo damuwa matuka, domin suna barazana ga zaman lafiya da kuma makomar dimokuradiyya a jihar.

" A jiya, Hon. Aliyu Sani Madaki, mamba a Majalisar Tarayya kuma dan takarar jam’iyyar APC, ya gudanar da kaddamar da wasu ayyuka. Sai dai wannan taro ya rikide zuwa tashin hankali, inda yan daba dauke da mak**ai s**a jikkata wadanda basu ji ba basu gani ba, hakan ya jawo fargaba a tsakanin jama’a.

" Haka zalika, a yau ma, Dan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar APC, A.A. Zaura, ya kaddamar da yakin neman zabensa inda yan daban dake tare dashi s**a afkawa yan kasuwar waya ta farm centre har s**a kwashe musu wayoyi da kudade Sannan s**a sa sara kan mai uwa da wabi.

"Wadannan abubuwa guda biyu suna nuni da wata barazana mai girma, wadda ke nuna yiwuwar amfani da irin wadannan matasa wajen tsoratar da masu zabe, da kuma lalata kayan zabe," in ji shi.

Arzai ya kuma yi kira ga al'ummar jihar da su tabbata sun karbi katin zaɓe don gudanar da ƴancin su na yan kasa, inda ya kuma yi kira da yan jam'iyyar su ta ADC da su tabbata sun yanki katin jam'iyyar da na zaɓe.

Me za ku ce?

Yusuf Buhari ya nuna satifiket din da ya amsa na kammala yi wa kasa hidima a Nijeriya
27/04/2026

Yusuf Buhari ya nuna satifiket din da ya amsa na kammala yi wa kasa hidima a Nijeriya

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Daily Report posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share