22/08/2025
π MURYAN TALAKA β Kashi na 1
Assalamu alaikum βyan uwa masu sauraro.
A yau mun fara sabon shiri mai suna MURYAN TALAKA, shiri da zai riΖa zuwa muku a duk ranar Jumaβa, inda za mu tattauna kan abubuwan da s**a shafi rayuwar talaka, yadda ake tafiyar da shugabanci, da kuma irin rawar da ya kamata mu βyan Ζasa mu taka domin ganin alβumma ta gyaru.
Shirinmu na yau zai fara da tambaya mai sauΖi amma mai zurfi:
π Shin mu a matsayin talakawa muna ganin duk abin da ya ke faruwa a Ζasar nan, mun riga mun yi shiru da zuciya?
Akwai wasu lokuta da muke ganin kuskure a tafiyar da alβumma amma sai mu Ζyale, mu Ιauka babu abin da za mu iya yi. To amma gaskiya akwai abin da za mu iya yi:
Da farko, mu fara da gyara kanmu β mu zama nagari a muβamalar mu.
Na biyu, mu riΖa faΙa gaskiya da kwantar da hankali, ba da husuma ba.
Na uku, mu riΖa Ιaga murya cikin hikima don a ji abin da yake damunmu.
Idan shugabanni sun ji muryan talaka da gaskiya, to za a samu canji.
π‘ Muryan talaka ba kururuwa ba ce, murya ce ta gaskiya wadda idan aka saurare ta, za ta iya kawo canji mai kyau.
Ku kasance tare da mu a kowane Jumaβa domin cigaba da wannan tafiya. Wannan shi ne farkon shirinmu.
π https://www.facebook.com/profile.php?id=61577013226427