28/06/2025
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Sanya Ma Sabuwar Dokar Kayan Nauyi Hannu
Ga abinda hakan ke nufi ga al’ummar Jihar Katsina
Jiya jiyan nan, Gwamna Dikko Radda ya sanya hannu a dokar da ta shafi al’ummar Jihar Katsina, musamman saye ko sayar da ƙarafa (kayan nauyi).
Wannan sabuwar doka za tayi maganin matsalolin da ke tasowa a hidimar, kamar haka: sata da ɓarnatar da kadarorin gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane da sunan kwasar bola. Musamman, mun shaida inda aka rinƙa ɓallewa da satar kayayyakin makarantu, wayoyin wutar lantarki, bututun ruwa, har ma da marafan ƙofa da taga, domin sayarwa a matsayin kayan nauyi.
Wannan doka ba tana haramta sana’ar ba ne; za ta gyara harkar ne ta hanyar tsaftacewa, ingantawa, da samar da tsare-tsaren da za su gudanar da ita domin amfanin al’ummar Jihar Katsina da ma na wajenta.
🛠️ Abinda dokar ke buƙata shi ne:
Duk wasu masu harkar za su yi rijista, kuma su samu lasisi daga Gwamnatin Jiha.
Duk wasu cinikayya da za ayi, sai an rubuta sunan mai sayarwa, abinda aka sayar, rana da lokaci, da kuma inda aka samo shi.
Duk harkar saye da sayarwa za ayi ta ne da rana a lokacin da aka ƙayyade, ba da dare ba.
Yara ƙanana 'yan ƙasa da shekara sha takwas (18) ba za su saya ko su sayar da kayan nauyi ba.
Diloli masu rijista ne kaɗai za su yi hulɗar, kuma a shagunansu ko ofisoshinsu. Ba sauran saye da sayarwa a wajen waɗannan wurare kamar gidaje da sauransu.
Ƙungiyoyin masu sana’ar kayan nauyi za su saka ido, kuma su hukunta mambobinsu.
Duk wanda aka samu da karya doka, za a ci shi tara, ko a gurfanar da shi, ko ma a dakatar da kasuwancin nasu.
👨🏽🔧 Ta yaya hakan zai shafi mutanenmu:
Idan kana yawon neman kayan nauyi, ko kana saye, ko sarrafa su:
Dole sai ka yi rijista domin cigaba da harkar.
Dole ka rinƙa rubuta abinda ka saya, da wurin wanda ka saya.
Idan kana harkar nan a halattacciyar hanya, wannan sabuwar doka za ta baka kariya da yanci.
Idan kuwa baka yi rijista ba, ko kana sayen kayan sata, toh, lokaci ya yi da za ka gyara.
🏘️ A