Sautus Sunnah

Sautus Sunnah Authentic Sunnah reminders, lectures, short clips & beneficial knowledge.
(2)

Domin tallafawa wannan manufa 👇🏻
Accoun Number: 6387403608
Account Name: Sautus Sunnah Media
BanK Name : Moniepoint Micro Finance
https://sautussunnah.lovable.app

27/08/2026

Duniya ba ta kai ka tada hankalinka a kanta ba, kuma in ka santa, ba ta kai ka ka bita a guje ba.

— Dr. Jameel Moh’d Sadees

Dr. Jameel Muhammad Sadis

22/08/2026

ZAMA DA ƳAN AFRIKA A FADAR SARKIN HAUSAWA NA KASAR TURAI A FARIS

21/08/2026

🔥 MU TAMBAYE KA… KA SAN WANNAN? 👀

Akwai wata aya a cikin Al-Qur’ani da mutane da yawa suke karantawa, amma ba kowa ya tsaya ya fahimci ma’anarta da sakonta ga rayuwarsa ba.

📖 Allah ﷻ Ya ce:

فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا ۝ إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا

“Lalle ne, tare da tsanani akwai sauƙi. Lalle ne, tare da tsanani akwai sauƙi.”
(Suratul Inshirah 94:5–6)

❤️ Idan kana cikin wani hali a yanzu, kada ka yanke ƙauna da rahamar Allah.

💬 Ka rubuta “ALHAMDULILLAH” a comments idan ka yarda cewa bayan wahala akwai sauƙi.

📲 Ka SHARE wannan post zuwa ga mutum ɗaya da kake ganin yana bukatar wannan tunatarwar yau.

🔔 SAUTUS SUNNAH — Domin yada kalmar Allah da Sunnah.

20/08/2026

Dalili da Hikimar Auren Gata da Gwamnatin Kano ta yi

Abdullahi Asil Marafa Yazo A Mataki Na Biyar A Musabaƙar Alƙur’ani Ta DuniyaƊan Najeriya, Gwani Muhammad Abdullahi Asil ...
19/08/2026

Abdullahi Asil Marafa Yazo A Mataki Na Biyar A Musabaƙar Alƙur’ani Ta Duniya

Ɗan Najeriya, Gwani Muhammad Abdullahi Asil Marafa daga Jihar Zamfara, ya samu matsayi na biyar 5 a Musabaƙar Alƙur’ani ta Duniya karo na 46 da ake gudanarwa a Masarautar Saudiyya.

Wannan babbar nasara ce ga Najeriya da Jihar Zamfara, musamman ganin yadda ya fafata da ƙwararrun masu karatun Alƙur’ani daga ƙasashe daban-daban.

Muna taya Gwani Muhammad Abdullahi Asil Marafa murna bisa wannan gagarumar nasara.

Allah Ya ƙara masa ilimi, basira da ɗaukaka, Ya sanya Alƙur’ani ya zama haske da hujja a gare shi.

Sautus Sunnah

Ƴar Najeriya, Maryam Ibrahim Dan Azumi, ta lashe matsayi na ɗaya (1st Position) a ɓangaren mata — 60 Hizb da Tafsiri, a ...
19/08/2026

Ƴar Najeriya, Maryam Ibrahim Dan Azumi, ta lashe matsayi na ɗaya (1st Position) a ɓangaren mata — 60 Hizb da Tafsiri, a Gasar Sarki Abdulaziz ta Ƙasa da Ƙasa ta Alƙur’ani, karo na 46, da aka gudanar a Makkah, Masarautar Saudiyya.

Gasar ta bana ta samu halartar masu fafatawa daga ƙasashe 133 na duniya, abin da ya ƙara wa wannan gagarumar nasara muhimmanci da daraja. 🇳🇬🌍🏆

Wannan nasara ta ƙara tabbatar da irin baiwar da Allah Ya h**e wa ƴaƴan Najeriya a fagen Haddar Alƙur’ani da ilimin Tafsiri.

Masha Allah! Muna taya Maryam Ibrahim Dan Azumi da Najeriya murna. 🇳🇬

19/08/2026

Matsayar Sheikh Aminu Daurawa kan takarar Muslim-Muslim a Najeriya
Babu jam'iyyar Musulunci a Najeriya, ra'ayin 'yan kasa ne su zabi wanda suke so in ji Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a yayin ziyarar da ya kawo DW Hausa a birnin Bonn na Tarayyar Jamus

19/08/2026

Duk zuchiyar da tasan Allah babu abunda take nema Kamar yardar Allah

——— Dr. Jameel Moh’d Sadees

. Sautus Sunnah@top fans Dr. Jameel Muhammad Sadis

19/08/2026

Yaya Zaka Zama Musulmin Kwarai | Ganawa da Musulmin Africa A Kasar Jamus

Ganawa ta musamman da Musulman Afirka mazauna ƙasar Jamus, a birnin Frankfurt, ƙarƙashin African Muslim Association, domin tattaunawa kan yadda za mu ƙarfafa imanimmu, kyautata halayenmu, haɗa kan al'ummarmu, da kuma zama musulmai na ƙwarai a cikin al'ummar da muke rayuwa.
Manufa: Gina al'umma mai ƙarfi, haɗin kai, kyakkyawar mu'amala, ilimi, tarbiyya da zaman lafiya

Muna taya Professor Bashir Aliyu Umar, OON, murnar naɗa shi da Bank of Ghana ya yi a matsayin Shugaban Majalisar Shawarw...
18/08/2026

Muna taya Professor Bashir Aliyu Umar, OON, murnar naɗa shi da Bank of Ghana ya yi a matsayin Shugaban Majalisar Shawarwari kan Harkokin Kuɗaden na Musulunci.

Allah ya taya riko ya baka ikon sauke wannan nauyi, ameen.

Sautus Sunnah

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sautus Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category