Radda Visionary Network Media

  • Home
  • Radda Visionary Network Media

Radda Visionary Network Media Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Radda Visionary Network Media, Media/News Company, .

Radda Visionary Network Media is a platform dedicated to showcasing progress, inspiring leadership, and amplifying voices that shape a greater Katsina State and beyond.

27/11/2025

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sanya hannu kan kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar N897.8bn, yana mai sanya jihar a matsayin ta farko a Najeriya da ta kammala kasafin cikin lokaci. Fiye da kashi 80% na kudin an karkata shi ga manyan ayyuka, ciki har da ilimi, da gine-gine, da ci gaban tattalin arziki. Gwamna Radda ya kuma ƙaddamar da sabon Fibre Network da wutar hasken rana, abin da ya kara tabbatar da sabuwar manufar cigaba a Katsina.
Dr. Dikko Umaru Radda Katsina State

25/11/2025

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana sabbin matakan da gwamnati ke ɗauka domin canza tsarin tattalin arzikin jihar, ciki har da kafa KSDMB, faɗaɗa shirin Nigeria for Women Project zuwa kananan hukumomi 34, gina tashar samar da wutar ruwa a Danja, da kulla muhimman yarjejeniya da ƙungiyoyi daga ƙasashen waje. Matakan sun fito ne a taron Katsina Economic and Investment Summit 2025 domin mayar da jihar cibiyar zuba jari da ci gaba a Najeriya. Dr. Dikko Umaru Radda

23/11/2025

Katin zabeka ba katin roba ba ne—ikonka ne, muryarka ce, hakkinka ne na zabar makoma.
Kasarmu za ta inganta ne idan muka fito mu kada kuri’a.
Kada ka bar wani ya yanke maka hukunci.
Ka fito ka zabi makomarka!
Dr. Dikko Umaru Radda

23/11/2025

Katsina ta samu gagarumar nasara!
Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya wakilci jihar a taron duniya na Ambition Africa 2025 a Paris, inda ya tattauna kan sabbin hanyoyin samar da makamashi mai dorewa, tsaro da ci gaba.
Wannan shi ne karo na farko da wani Gwamnan Jiha daga Najeriya ya halarci wannan babban taro karkashin kulawar Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron.
Katsina tana bude sabon babi – zuba jari, masana’antu, hasken rana, iska, hydro da sabbin damar ci gaban matasa.

Dr. Dikko Umaru Radda Muhammad Sani Lawal

20/11/2025

- Dalibai 2,199 za su amfana da tallafi
- Katsina ta kulla yarjejeniya da Belarus kan ilimi, tsaro da noma
- Hamza Hadi Maiwada na haskakawa a
Turai
Ku kasance tare da Radda Visionary
Network Media don karin labarai na ci gaba.

16/10/2025

“Jagoranci da Manufa. Hidima da Imani. Dr. Aminu Usman (Abu Ammar).


SANARWA GA MANEMA LABARAIRadda Visionary Network Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa da Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina; Ta Karrama K...
13/10/2025

SANARWA GA MANEMA LABARAI

Radda Visionary Network Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa da Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina; Ta Karrama Kwamanda Janar da Lambar Girmamawa

Katsina, Najeriya — 11 ga Oktoba, 2025

Ƙungiyar Radda Visionary Network ta kai ziyarar ban girma ga Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), domin ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma tattauna sabbin hanyoyin yin aiki tare wajen bunƙasa al’umma, ƙarfafa matasa, da inganta ci gaban mata a fadin Jihar Katsina.

A lokacin ziyarar, tawagar da Mohd Sani Lawal, shugaban ƙungiyar, ya jagoranta tare da Umar Jamilu, Sakataren Ƙungiya, Fatima Sabo Nalado, Mataimakiyar Shugaba, Ibrahim Babangida Aliyu Turaji, Ma’ajin Ƙungiya, da Zainab Bello Ali Mashi, Jagorar Mata ta II, tare da sauran mambobin zartarwa, sun mika Lambar Girmamawa ga Dr. Usman domin girmama irin gudunmawarsa, jagorancinsa mai hangen nesa, da jajircewarsa wajen bunƙasa al’umma da ɗaukaka tarbiyya.

A cikin jawabin sa, Dr. Usman ya bayyana godiya mai zurfi bisa wannan karramawa, inda ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen ƙarfafa matasa da mata. Haka kuma ya amince da farin ciki ya zama Mai tallafawa (Patron) ga Radda Visionary Network, inda ya sha alwashin ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga manufofin ƙungiyar.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar, Mohd Sani Lawal, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce ƙarfafa alaƙa da Hukumar Hisbah wajen inganta zaman lafiya, ladabi da tarbiyya, da kuma haɗin kai a cikin al’umma. Ya tabbatar da cewa ƙungiyar tana da cikakken shiri na yin aiki tare da hukumomi da cibiyoyi domin inganta shirin ƙarfafa matasa, ci gaban mata, da dorewar shirye-shiryen al’umma.

Ƙungiyar Radda Visionary Network ta jaddada cewa wannan karramawa da ta bai wa Dr. Usman alama ce ta ci gaba da manufar ƙungiyar na girmama shugabanni masu gaskiya, sadaukarwa, da jajircewa wajen haɓaka ci gaban al’umma.



04/10/2025

Shugabantar matasan Katsina zuwa gobe mai haske — Hon. Abubakar Tsanni. Dr. Dikko Umaru Radda Katsina State Usman A Tsanni

SANARWA GA MANEMA LABARAIRadda Visionary NetworkA ranar talata, [30 ga Satumba, 2025], kungiyar Radda Visionary Network ...
01/10/2025

SANARWA GA MANEMA LABARAI

Radda Visionary Network
A ranar talata, [30 ga Satumba, 2025], kungiyar Radda Visionary Network ta kai ziyarar ban girma ga Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Matasa na Jihar Katsina, Honorable Abubakar Tsanni.
A yayin wannan ziyara, kungiyar ta mika masa Lambar Girmamawa ta Musamman (Award of Excellence) a matsayin yabo kan jajircewarsa wajen tallafawa matasa, ci gaban al’umma da kuma nuna jagoranci na gari.
Haka kuma, muna da karramawa da halartar Hon. Mustapha Sani Bello (Jaga), Dan Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina mai wakiltar Karamar Hukumar Mashi kuma Shugaban Kwamitin Majalisa kan Harkokin Matasa da Wasanni, wanda ya halarci wannan taro tare da Hon. Abubakar Tsanni.
A yayin tattaunawar, an mai da hankali kan manyan matsalolin da ke shafar matasa, ciki har da shirye-shiryen karfafa gwiwa ga matasa, ci gaban wasanni, da dabarun karfafa shiga matasa a harkokin mulki da hidimar al’umma.
A jawabin sa, Hon. Abubakar Tsanni ya yaba wa Radda Visionary Network bisa jajircewarta wajen hada kai da karfafa matasa, tare da alkawarin ci gaba da ba da goyon bayansa ga ayyukan kungiyar. Haka nan, Hon. Mustapha Sani Bello (Jaga) ya karfafa kungiyar da ta ci gaba da tafiya a kan turbar hadin kai, bunkasa baiwa, da gina shugabanci a tsakanin matasan Jihar Katsina.
Kungiyar Radda Visionary Network ta nuna godiya bisa kyakkyawar tarba, tare da sake jaddada kudurinta na mara baya ga manufofin gwamnati da s**a shafi bunkasa matasa da kuma tabbatar da ci gaban al’umma mai dorewa.

Sa hannu:
Radda Visionary Network

Daga gare mu duka na Radda Visionary Network, muna mika fatan alheri gare His Excellency Mallam Dikko Umar Radda, Gwamna...
10/09/2025

Daga gare mu duka na Radda Visionary Network, muna mika fatan alheri gare His Excellency Mallam Dikko Umar Radda, Gwamnan Jihar Katsina — Allah Ya albarkaci tafiyar shugabancinka da hikima, farin ciki da nasara.






























Address


820

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Radda Visionary Network Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share