BID HAUSA

BID HAUSA Welcome to *BID HAUSA*, the premier digital gateway for authentic Hausa‑language audio.

We bridge Northern Nigeria’s cultural heartbeat with global reach, delivering meticulously crafted programmes, crisp news, insightful interviews, and vibrant media eng

31/08/2026

Ba karamin abin kunya bane a ce an samu hukumomin boge 4 a cikin gwamnatin Tinubu, wannan gaza wa ce babba.

Hon. Sirajo Aminu Makera jigo a jam'iyyar ADC.

29/08/2026

Dalilan da za su sanya a zabi Wazirin Adamawa Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Tarayyar Najeriya a zaben 2027.

Hon. Surajo Aminu Makera, jigo a jam'iyyar ADC a Najeriya.

28/08/2026

Jawabin manajan kamfani green house katsina Alh salisu shehu wajen taron maulidi na green house ranar 12 ga watan rabiyul auwal hjr 1448

25/08/2026

Jawabi daga daraktan kamfani green house katsina Alh sani shehu namaska

25/08/2026

GREEN HOUSE KATSINA TA GUDANAR DA MAULUDIN ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)

A yau, 12 ga watan Rabi'ul Auwal, kamfanin Green House Katsina ya gudanar da taron Mauludin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (S.A.W), cikin yanayi na farin ciki, ibada da tunatarwa, ƙarƙashin jagorancin shugaban kamfanin, Alhaji Shehu Namaska.

Taron ya samu halartar ma'aikata da sauran mahalarta daban-daban, inda aka gudanar da karatun Alƙur'ani Mai Girma da Ishiriniya Diwani, tare da majalisar nasiha da tunatarwa kan muhimmancin kyawawan ɗabi'u da kyakkyawar mu'amala.

A farkon taron, Manajan kamfanin Green House Katsina, Alhaji Salisu Shehu, ya yi maraba da mahalarta taron, tare da nuna farin cikinsa da wannan dama ta haɗuwa domin tunawa da rayuwa da koyarwar Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu (S.A.W).

A jawabinsa, shugaban kamfanin Alhaji Shehu Namaska ya jaddada muhimmancin kyawawan halaye a wajen aiki, inda ya ja hankalin ma'aikatan kamfanin da su riƙa mutunta tare da kyautata mu'amala da abokan hulɗarsu.

Ya bayyana cewa, abokin hulɗa ginshiƙi ne mai muhimmanci ga ci gaban kowace sana'a da kamfani, don haka ya kamata a riƙa girmama shi, sauraron buƙatunsa da kuma mu'amala da shi cikin mutunci da gaskiya.

Haka kuma, Alhaji Shehu Namaska ya shawarci ma'aikatan da kada su tsaya kawai kan abin da suke samu a yau, sai dai su san ci gaban kansu, su koyi aiki tukuru, tanadi da kyakkyawan tsarin rayuwa domin kyautata makomarsu.

Ya ce idan mutum ya yi aiki da jajircewa, gaskiya da hangen nesa, tare da yin tanadi yadda ya kamata, nan gaba shi ma zai iya zama mai zaman kansa kuma ya samar da guraben aikin yi ga wasu.

A jawabin kammala taron, Daraktan kamfanin Green House Katsina, Alhaji Sani Shehu, ya sake jaddada manufar kamfanin ta girmama da daraja abokan hulɗarsa, yana mai cewa nasarar kamfanin ba za ta cika ba tare da amincewa da goyon bayan abokan hulɗa ba.

Ya tabbatar da cewa Green House Katsina zai ci gaba da ɗaukar abokan hulɗarsa a matsayin muhimmin ɓangare na tafiyarsa, tare da yin iya ƙoƙarinsa wajen samar da kyakkyawar hidima da mu'amala mai inganci.

Taron Mauludin ya kasance wata muhimmiyar dama ta ƙarfafa zumunci, haɗin kai, kyawawan ɗabi'u da tunawa da koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W), tare da ƙara wa ma'aikata kwarin gwiwar yin aiki cikin gaskiya, mutunci da kishin ci gaban kamfanin.

Green House Katsina — ci gaba tare da girmama abokan hulɗa da kyautata hidima.

Matakin Trump kan Kim Jong-un ya ƙara haifar da shakku kan amincin Amurka a wani muhimmin lokaci ga nahiyar Asiya.**
24/08/2026

Matakin Trump kan Kim Jong-un ya ƙara haifar da shakku kan amincin Amurka a wani muhimmin lokaci ga nahiyar Asiya.**

24/08/2026
'Yan Houthi na Yemen sun ce sun kai hari kan wani jirgin dakon mai na Saudiyya a Tekun Bahar Maliya, lamarin da ke kara ...
24/08/2026

'Yan Houthi na Yemen sun ce sun kai hari kan wani jirgin dakon mai na Saudiyya a Tekun Bahar Maliya, lamarin da ke kara tsananta rikici a yankin.

24/08/2026

Allah yakara basira AMIN

24/08/2026

Address

Sabon Titi Kwado
Katsina
820001TO820281

Opening Hours

Monday 08:00 - 00:00
Tuesday 08:00 - 00:00
Wednesday 08:00 - 00:00
Thursday 08:00 - 00:00
Friday 08:00 - 00:00
Saturday 08:00 - 00:00
Sunday 08:00 - 00:00

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BID HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share