Modern journalists

  • Home
  • Modern journalists

Modern journalists Modern journalist is a new medium. zaku iya bayar da talla ga wannan shafin
(2)

Domin samun sahihai kuma ingantattun Larabarai, akan al'amurran da ke faruwa a gida Nijeriya, dama sauran Ƙasashen Ketare wasu lokuttan, gami da tallata Hajojin ku, ko kuma ra'ayin ku.

" Banzo garin Daura saboda addu'ar kwana 3 ba, domin babu inda musulunci yace a ware wasu kwanaki domin yiwa Mamaci addu...
17/07/2025

" Banzo garin Daura saboda addu'ar kwana 3 ba, domin babu inda musulunci yace a ware wasu kwanaki domin yiwa Mamaci addu'a, nazo ne domin yin ta'aziya bisa ga Babban rashin da mukai"~ Sheik Yahaya Jingir.

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin daukar sabbin Jami'ai da ta fara, har ya zuwa ranar Litinin 21 ga watan Yuli 2025...
17/07/2025

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin daukar sabbin Jami'ai da ta fara, har ya zuwa ranar Litinin 21 ga watan Yuli 2025.

Sakon ta'aziya....A madadin Shugaban Hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar Katsina (SUBEB) Dr. Kabir Magaji Gafiya ke miƙa sa...
16/07/2025

Sakon ta'aziya....

A madadin Shugaban Hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar Katsina (SUBEB) Dr. Kabir Magaji Gafiya ke miƙa sakon ta'aziya ga iyalai da yan'uwa, da sauran al'ummar Jihar Katsina, bisa ga rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Dr. Kabir Magaji ya bayyana rashin Marigayin a matsayin Babban rashi, ga al'ummar Nijeriya, dama Duniya baki ɗaya.

Kazalika, ya miƙa sakon ta'aziya ga Gwamna Malam Dikko Radda na Jihar Katsina, da sauran al'ummar Jihar Katsina baki ɗaya, yana mai addu'ar neman rahamar Ubangiji ga Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Mutuwar Buhari abin fargaba ne ga masu hankali ~ Matashi Asad Yelwa‎Ba mutuwarsa ce abin ɗaga hankali ba domin kuwa ta k...
16/07/2025

Mutuwar Buhari abin fargaba ne ga masu hankali ~ Matashi Asad Yelwa

‎Ba mutuwarsa ce abin ɗaga hankali ba domin kuwa ta kowa tana tafe, Abun fargabar shi ne, ya roke mu gafara kafin ya tafi, kuma da yawan mutane sun yafe masa, Amma mu kuma bamu da damar rokon tashi gafarar akan abin da muka yi masa, domin dole akwai.

Hakanan kuma ba zamu sake ganin shi ba sai a filin alkiyama, ga mu, ga shi a gaban ubangiji- zamu maimaita zantukanmu, da posts din mu a kan shi na gaskiya da na karya. Lokacin kuma ba a yafiya. Indai wannan bai daga maka hankali ba, ban san kuwa me zai daga shi ba, dan'uwa.

‎Hakika mutuwa darasi ce ga mai Imani. Allah ka sa mutuwa ta ci gaba da koya mana kokarin fita hakkin bayin ka kafin mu rasa damar neman yafiyar su.

Wasu daga cikin Fuskokin Shugabanni a yayin Jana'izar marigayi Muhammadu Buhari.
15/07/2025

Wasu daga cikin Fuskokin Shugabanni a yayin Jana'izar marigayi Muhammadu Buhari.

Darasi...A Da wurin zama na Hutawa, yanzu kuma wurin zaman na har abada.
15/07/2025

Darasi...

A Da wurin zama na Hutawa, yanzu kuma wurin zaman na har abada.

Shin ko me ya hana mawaki Rarara wallafa sakon ta'aziyar marigayi Buhari, har ya zuwa wannan Lokaci?
14/07/2025

Shin ko me ya hana mawaki Rarara wallafa sakon ta'aziyar marigayi Buhari, har ya zuwa wannan Lokaci?

Yanzu-yanzu...Gwamnatin tarayya ta baiwa Ma'aikata Hutun Gobe Talata 15 ga watan Yulin 2025, domin alhinin rashin tsohon...
14/07/2025

Yanzu-yanzu...

Gwamnatin tarayya ta baiwa Ma'aikata Hutun Gobe Talata 15 ga watan Yulin 2025, domin alhinin rashin tsohon Shugaban Ƙasa Mariyagi Muhammadu Buhari.

Yanzu-yanzu...Gwamnatin Katsina da takwarorinta na shiyar Arewa maso yamma, sun ayyana Gobe Talata a matsayin ranar Hutu...
14/07/2025

Yanzu-yanzu...

Gwamnatin Katsina da takwarorinta na shiyar Arewa maso yamma, sun ayyana Gobe Talata a matsayin ranar Hutu...

Ƙungiyar Gwamnonin arewa maso yamma ta bayyana Gobe Talata, a matsayin ranar hutu, domin nuna alhin rashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa da Shugaban Kungiyar Gwamna Malam Dikko Umar Radda na Jihar Katsina ya sanya wa hannu, ta bayyana a Gobe Talata ne ake sa ran gudanar da Jana'izar Marigayin a Maihaifar da ke Garin Daura.

"Ina fatan zamu yi yafiya da kuma addu'a ga Baba Buhari"~Shiek Daurawa roki ƴan Nijeriya.
14/07/2025

"Ina fatan zamu yi yafiya da kuma addu'a ga Baba Buhari"~Shiek Daurawa roki ƴan Nijeriya.

Na ɗaya daga cikin waɗan da za su fi kowa Jimamin rashin Shugaba Buhari.Ko zaku iya tuna sunan sa, da kuma matsayin sa g...
13/07/2025

Na ɗaya daga cikin waɗan da za su fi kowa Jimamin rashin Shugaba Buhari.

Ko zaku iya tuna sunan sa, da kuma matsayin sa ga Marigayin?

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Modern journalists posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Modern journalists:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share