Tafiyar Autan rarara Dan Soja

Tafiyar Autan rarara Dan Soja Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tafiyar Autan rarara Dan Soja, Media/News Company, katsina, Katsina.

eid Mubarak oga sir Allah shi maimaita
20/03/2026

eid Mubarak oga sir Allah shi maimaita

Shugaban Gidauniyar Shehu Dabai Hon. Shehu Dabai Ya Cika Alƙawari Ta Hanyar Mika Makullin Sabuwar Mota Ga Fitaccen Mawak...
30/12/2025

Shugaban Gidauniyar Shehu Dabai Hon. Shehu Dabai Ya Cika Alƙawari Ta Hanyar Mika Makullin Sabuwar Mota Ga Fitaccen Mawakin Gwamna Dikko Radda, Dan Soja

Shugaban Shehu Dabai Foundation, Hon. Shehu Dabai, ta hannun wakilan sa ya mika makullin sabuwar mota ga fitaccen mawakin Gwamna Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, wato Dan Soja, a kofar gidan Alhaji Surajo Mai Asharalle, Kofar Kaura, cikin garin Katsina.

An dai mika wannan mota ne domin nuna yabo da girmamawa ga wakokin da Dan Soja ke yi domin tallafawa manufar Gwamna Dikko Radda da jam’iyyar APC a Katsina.

Idan ba a manta ba, a ranar 12 ga Disamba, 2025 lokacin da Gwamna Radda ya kai ziyarar aiki tare da kaddamar da aikin samar da wutar lantarki a karamar hukumar Danja, Hon. Shehu Dabai—wanda shi ne Darakta Janar na Gidauniyar Jin Kai da Tallafawa Al’umma ta Shehu Dabai Foundation—ya bayyana kyautar sabuwar motar ga Dan Soja a matsayin yabo kan rawar gani da yake taka wa.

Hon. Dabai ya ce wannan taimako “na daga cikin muhimmiyar gudummawar da gidauniyar ke bayarwa domin cigaban jam’iyya da kuma goyon bayan ayyukan Maigirma Gwamna Malam Dikko Radda.”
Ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiwatar da makamantan ayyukan jin kai matukar suna taimakawa ci gaban jihar.

Credit:
DAN SOJA AUTAN RARARA
MEDIA TEAM
Disemba 26/12/2025

27/12/2025

Address

Katsina
Katsina
2011

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tafiyar Autan rarara Dan Soja posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share