
27/05/2025
Idan Allah Ya Kiraka Ba Wanda Ya Isa Ya Hana
Wani matashi dan Libiya mai suna Amer yana kan hanyarsa ta zuwa aikin Hajji, sai ya fuskanci matsala dangane da sunansa yayin da ake bincike a filin jirgi. Jami’an tsaro s**a ce masa, “Za mu kokarta warware matsalar, amma sai ka jira dan lokaci.” Sauran mahajjata an kammala binciken su, s**a hau jirgi, aka rufe kofar jirgin. Bayan ɗan lokaci, an warware matsalar Amer, amma matukin jirgi ya ƙi buɗe masa kofa, jirgin ya tashi.
Jami’an tsaron s**a rarrashe shi s**a bashi haƙuri, Amma Amer ya ki barin filin jirgin, ya nace da cewa, “Na yi niyyar yin Hajji, kuma In Sha Allah zan je.”
Cikin gaggawa sai ga rahoto ya iso cewa jirgin ya samu matsala, ya dawo. Aka gyara matsalar jirgin, amma matukin ya sake kin bude kofa. Jami’in tsaro ya ce masa ya rarrashe shi yace masa “Ba a rubuta wannan tafiyar za'ayi ta da kai ba.” Sai Amer ya amsa da kwarin gwiwa, “Na yi niyyar yin Hajji, kuma In Sha Allah zan je.”
Jirgin ya sake tafiya, daga baya aka sake samun rahoto cewa ya samu wata matsala kuma ya dawo karo na biyu. A wannan lokaci ne matukin jirgin ya fahimta, ya ce, “Ba zan tashi ba idan babu Amer.” wuka ɗauke shi s**a tafi, s**a sauka lafiya.
Wannan hoto ne da matuƙa jirgin s**a ɗauka tare da Ameer.
Sharin Inside the Haramain ne ya wallafa rubutun da turanci.