Isah Miqdad Project Promoters

Isah Miqdad Project Promoters Official page for Isah Miqdad Project Promoters

10/08/2026

Labari cikin Video:

Na yadda Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon Isah Miqdad AD Saude ya kai ziyarar duba aikin ruwa ( Solar Powered Borehole) a garin Bum-Bum dake mazabar Shinkafi ‘B’

10/08/2026

Mai girma Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya halarci Nutrition SMART Survey Planning Meeting 2026, wanda aka gudanar a Hillside Royal Suite, Katsina.

Taron, wanda Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta Jihar Katsina ta shirya tare da haɗin gwiwar UNICEF Kano Field Office, ya mayar da hankali kan nazarin sakamakon binciken Nutrition SMART na shekarar 2025, tare da tsara dabarun inganta binciken na shekarar 2026.

10/08/2026

Kai tsaye daga Auditorium, Hillside Royal Suite, Katsina, inda ake gudanar da Taron Shirye-shiryen Nutrition SMART Survey na shekarar 2026.

Mai girma Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, na daga cikin manyan mahalarta taron, wanda ke mayar da hankali kan nazarin sakamakon Nutrition SMART Survey na 2025 da kuma tsara ingantattun dabaru domin gudanar da binciken shekarar 2026.

07/08/2026

Bidiyon:
Ciki da wajen sabon Police Outpost na Kofar Sauri, wanda Karamar Hukumar Katsina ta gina ƙarƙashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude

07/08/2026

A yau an ƙaddamar da sabon Police Outpost na Kofar Sauri, wanda Karamar Hukumar Katsina ta gina ƙarƙashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon.Isah Miqdad AD Saude, domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Faruk Lawal Jobe, ne ya jagoranci ƙaddamar da aikin tare da halartar manyan jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, shugabannin siyasa da sauran al’umma.

07/08/2026

Jawabin Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Faruk Lawal Jobe a wajen ƙaddamar da Bude Sabon Ofishin ’Yan Sanda (Police Outpost) da Gwamnatin Karamar Hukumar Katsina ta gina a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Isah Miqdad AD Saude.

07/08/2026

Jawabin Shugaban Karamar Hukumar katsina Hon. Isah Miqdad Ad Saude a wajen ƙaddamar da Bude Sabon Ofishin ’Yan Sanda (Police Outpost) da Gwamnatin Karamar Hukumar Katsina ta gina a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Isah Miqdad AD Saude.

07/08/2026

KAI TSAYE
Daga Kofar Sauri, Katsina, inda ake gudanar da bikin ƙaddamar da Bude Sabon Ofishin ’Yan Sanda (Police Outpost) da Gwamnatin Karamar Hukumar Katsina ta gina a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Isah Miqdad AD Saude

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Faruk Lawal Jobe, ne ke jagorantar ƙaddamar da wannan muhimmin aiki.

Hello Applicants!📢
02/08/2026

Hello Applicants!📢

Address

Katsina Local Government Council
Katsina
820101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Isah Miqdad Project Promoters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share