19/11/2025
Daga Tsohuwar Waya Zuwa Sabuwar Waya..
Wannan zai maka amfani sosai.
Sau tari ba kowa bane yakeda sha'awar riƙe waya kala-kala ba wani idan ya siya waya sai tayi masa sama da shekara biyu a hannunsa bai canza wata ba, sau tari kuma bawai saboda babu kuɗin canzawar bane A'a kawai saboda ya loda ma wayarsa abubuwa sosai kuma baya son ya rasasu musamman messages na wayar da sauran muhimman abubuwan da ya zuba ma wayar wanda canza wayar zaisa dole ya rasa wasu abubuwan a ciki..
To ga hanya mafi sauƙi da zakayi Transfering duk wani abu dake cikin tsohuwar wayarka zuwa sabuwar wayar da kasiya kamar irinsu: Applications, Messages, Call history, Music, Videos, Games da sauransu. Duk zasu sauka kai tsaye zuwa ga sabuwar wayar da ka canza insha Allah.
Matakin farko idan sabuwar wayar babu Xender a ciki sai katura mata xender, daganan sai kashiga cikin xender ɗin, itama haka zalika tsohowar wayar naka sai kashiga cikin xender ɗinta.
A cikin xender na sabuwar wayar naka daga gefen dama zakaga wata alama da take daga ƙarshe kusa da wata alama mai kamar alamar 'whatssp' kana dannata zata bayyanar maka da waɗannan abubuwan kamar haka:
1. Connect PC
2. Connect KaiOS
3. Scan Connect
4. Share Xender
5. Phone Copy
Sai ka danna wurin da aka rubuta "Phone Copy" kana dannawa zai buɗe maka daga cen sama zakaga wurin da aka rubuta "Import All data from your old phone to the new one." sai kayo kasa zakaga wurin da zasu tambayeka shin wannan wayar sabuwar ce ko tsohuwar?
To tunda a sabuwar ne sai ka danna wurin da kaga an rubuta "New" haka zalika itama a tsohuwar wayar sai kayi Exactly kamar yadda kayi a sabuwar amma ita idan kazo wurin sai ka dannan "Old" ma'ana tsohuwar wayar kenan..
Kana danna alamar "New" a sabuwar wayar naka ka tabbatar masu da cewa wayar itace sabuwar daganan zasu baka wani Options da zasu tambayeka shin ita tsohuwar wayar naka "Android" ce ko "Iphone" idan Android ce sai ka danna wurin android, kana dannawa zasu buɗe maka wani shafi da zasu sanar dakai cewa ka