NMB Media Concept

NMB Media Concept Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from NMB Media Concept, Media/News Company, Kaura Namoda, Kaura-Namoda.

25/08/2026

Maulud Mai tsaye Daga Zawuyyar Shehu Malam Babba Kaura Namoda jahar Zamfara

25/08/2026

Maulud 2026
Kai tsaye daga Zawuyyar Shehu Malam Babba Kaura Namoda Jahar Zamfara

25/08/2026
Almajirai huɗu na Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya da ke Kadage Sharifai a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano sun ...
17/08/2026

Almajirai huɗu na Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya da ke Kadage Sharifai a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano sun rasu bayan cin abincin da ake zargin gurɓatacce ne.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Shugaban ƙungiyar Tsangaya Media Network ta ƙasa, Alaramma Sani Musa Nuhu, ya fitar.

Sanarwar ta ce, almajiran sun rasu ne a Asibitin Malam Aminu Kano a daren Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, bayan sun ci abincin da ake zargin ya gurɓata.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an gudanar da jana’izar almajiran bayan samun umarni daga Dagaci da baturen ƴan snadan yankin.

09/08/2026

Kai tsaye daga Mu'assasatu Shehu Malam Babba Kaura Namoda wurin bikin yaye Dalibban islamiyya karo na 12 sashen karamar kulliya karo na 5 Sashen SIS karo na 2

ASHA KALLO LAFIYA

Gwamnatin Jihar Zamfara ta miƙa wa Shugaban Makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda (Rector) mutane huɗu da aka yi g...
07/08/2026

Gwamnatin Jihar Zamfara ta miƙa wa Shugaban Makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda (Rector) mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, waɗanda jami’an tsaron farin kaya na DSS s**a samu nasarar ceto wa.

An gudanar da bikin miƙa su ne a ofishin Shugaban makarantar, inda wakilan gwamnatin jihar s**a tabbatar da cewa dukkan waɗanda aka ceto suna cikin ƙoshin lafiya, tare da miƙa su ga mahukuntan makarantar domin ci gaba da kula da su.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa wannan nasara ta sake nuna irin ingantaccen haɗin gwiwar da ke tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro wajen ceto waɗanda aka sace da kuma yaƙi da matsalar rashin tsaro.

Gwamnatin ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da ba jami’an tsaro cikakken goyon baya domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda ya yabawa Gwamnatin Jihar Zamfara da jami’an DSS bisa jajircewarsu da ƙwarewar da s**a nuna wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su. Ya ce wannan mataki ya ƙara wa iyalai, ɗalibai da ma’aikatan makarantar kwarin gwiwa, tare da yin addu’ar Allah Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara da ƙasa baki ɗaya.

04/08/2026

Cikakken bayanin Yanda yanbindiga s**a tarwatsa sansanin soji da yin garkuwa da mutane Sama da 50 a Kasuwar daji cikin ƙaramar hukumar mulkin Kaura tare ta shugaban ƙaramar hukumar mulkin Com Mannir Mu'azu Haidara

01/08/2026

MAULUD SHEIKH AHMAD TIJJANI Daga Zawuyyar Shehu Malam Babba Kaura Namoda jahar Zamfara




Address

Kaura Namoda
Kaura-Namoda

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NMB Media Concept posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share