
30/06/2025
Mawallafa, ku yi farin ciki! Masu karatu, ku shirya!
Muna farin cikin sanar da ƙaddamar da manhajar wayar Kundi Bookstore — sabuwar dandamali da ke ba wa marubuta damar dora littattafansu da siyar da su kai tsaye ga masu karatu, tare da bayar da sauƙaƙen tsarin karatu a cikin manhajar kanta.
Kundi Bookstore ta magance ɗaya daga cikin manyan matsalolin da marubuta ke fuskanta — wato yada littattafansu ba bisa ka’ida ba — ta hanyar hana sauke ko raba littattafan, domin ana iya karantawa ne kawai a cikin manhajar.
❌ Babu ƙarin rubuta littafi kawai domin a raba shi ga waɗanda ba su saya ba.
✅ Marubuta za su iya wallafa aikinsu cikin sauƙi, su kuma isa ga sabbin masu karatu.
✅ Masu karatu za su iya siyan littattafai su kuma karanta su cikin aminci a cikin manhajar, ta yadda hakan zai kare haƙƙin mallakar marubuta.
Mun gina Kundi Bookstore domin ku, da tunanin ku, da tsammanin ku a zuciya. Kuma ku sani, sauran fasahohi masu ban sha’awa na zuwa nan ba da daɗewa ba — ku kasance cikin shiri!