30/06/2025
Darasin Rayuwa – Fitowa ta Goma Sha Takwas (18)
Godiya
Godiya tana daga cikin manyan siffofin da suke kawo nutsuwa da farin ciki a rayuwa. Idan mutum ya saba godewa Allah a kan dukkan halin da yake ciki, zuciyarsa za ta cika da kwanciyar hankali da karɓar kaddara.
Godiya ba wai kawai tana takaita ga samun arziki ko nasara ba, har ma a cikin wahala da jarabawa. Wanda yake godewa Allah a lokacin da yake cikin ƙunci, ya fi ƙarfin wanda yake kuka da korafi, domin ya fahimci cewa duk abin da ya same shi akwai alheri a cikinsa.
Idan muka dinga godewa kan ƙanana da manyan ni'imomi, za mu gane cewa rayuwarmu cike take da abubuwan da s**a cancanci jin daɗi da murna. Wannan dabi’a ta godiya tana gina zuciya mai ƙarfi, tana cire hassada da kishi, tana kuma sa mutum ya ci gaba da ƙoƙari ba tare da jin ƙasƙanci ba.
Ka yi ƙoƙarin kasancewa daga cikin masu godiya a kowane lokaci: a lokacin da ka samu, da lokacin da aka karɓa daga gare ka. Ka gode wa Allah, ka gode wa mutane, ka gode ma kanka. Wannan zai taimaka maka wajen samun ingantacciyar rayuwa.
Abubuwan da za a koya:
– Godiya tana ƙara ni'imomi, tana kawo farin ciki da samun karin ƙarfi.
– Wanda yake godewa Allah, baya kallon rayuwa ta hanyar korafi ko kuka.
– Yin godiya yana sa ka zama mutum mai kyakkyawar mu’amala da mutane da Ubangiji.
✍🏻 Al-Hāfeez Abu Hassān
30/06/2025