Abdulbari Umar Hassan

Abdulbari Umar Hassan Crypto enthusiastic || Exploring the digital world || Peace Ambassador.

11/09/2022

‏{وَأَبْشِرُوا}🤍
‏‎﴿إِنَّ الَّذينَ قالوا رَبُّنَا اللَّهُ ثُمَّ استَقاموا تَتَنَزَّلُ عَلَيهِمُ المَلائِكَةُ أَلّا تَخافوا وَلا تَحزَنوا وَأَبشِروا بِالجَنَّةِ الَّتي كُنتُم توعَدونَ﴾ [فصلت: ٣٠]

06/09/2022

TATTAUNAWA TSAKANIN MA'AURATA..!!

Za ka zauna da abokanka kusha hira a majalisa tare da shewa da qyaqyatawa. Amma ita matarka ka girke ta a gida ba ta samun lokacinka ballantana kyakkyawar tattaunawa.

Ai daga cikin ma'anar aure: tarayya a rayuwa, debe kewa, farantawa juna rai. Kuma hakan ba zai samu ba idan ba kyakkyawar tattaunawa a tsakani.

Mata na yawan qorafi a kan yadda wasu mazaje suke kauce ma tattaunawa tsakaninsu da iyalensu. Sai mace ta rasa wanda za ta bayyana ma damuwarta. Gaskiya wannan ba daidai bane. Ya kamata maza mu gyara.

Girmamawa tare da zaben lafuzza masu kyau wajen tattaunawa na taimakawa wajen budewar zuciya ga abokin zama. Ku tattauna da iyalenku.

Jameel Muhammad Sadis

04/09/2022

RUSHEWAR GIDA BA DAGA NESA YAKE ZUWA BA.

Wani matashi ya tambayi abokinshi, ina kake aiki?

Sai yace: wuri kaza.

Abokin yace : Nawa ake baka a wata?

Yace:- 5000.

Sai abokin yace : 5000 kadai? Tayaya zaka rayu da dubu biyar?

Tun daga wannan ranar abokin ya raina aikinshi, ya nemi a qara mashi albashi, mai gidan yaqi qara mashi, shi kuma ya watsar da aikin.

A da yana aiki, yana samun 5000 a wata, amma yanzu baya aikin komai.

Wata ta tambayi qawarta wace kyauta mijinki ya baki a ranar birthday dinki?
Sai tace bai bani komai ba.
Shine qawar tace : Da gaske k**e? Anya kina da daraja a wurinshi kuwa?

Tunda ta jefa mata wannan bomb din a gida ta fita, da mijin matar nan ya dawo ya tadda ta cikin fushi, s**a hau rigima da jayayya daga qarshe ya sake ta.

Daga ina matsalar ta fara? Daga wannan kalmar da qawarta ta gaya mata.

Ance akwai wani mahaifi da yake rayuwa cikin kwanciyar hankali da iyalanshi, sai abokinshi yace mashi, ya akai danka bai ziyartarka sosai? Anya rashin lokaci ne ko ko dai baya sonka?
Tun daga wannan rana kwanciyar hankalin mahaifin ya qare, ya dawo kallon dukkan abunda danshi yakeyi a matsayin aibi da kuskure, kullum cikin damuwa da rashin godiyar kyautatawar da dandanshi yake mashi.

Tambayoyi ne da zamu iya tsammanin daidai suke, saidai suna iya rusa zamantakewa.

Meyasa baka sayi babbar waya ba?

Meyasa baka mallaki mota ba?

Tayaya zaka riqa jure halayen wannan mutumin?

Tayaya zaka bari ana yi maka wannan abun?

Muna yin wadannan tambayoyin la'alla bisa rashin sani, ko son jin labari, saidai bamu sani ba zasu iya haifar da wasu tambayoyin a zuciyar mai sauraro.

Abunda saqon ya qumsa shine : Karka zamo cikin masu rusa katangar alaqar da take ginanna.

Ka shiga gidan mutane a makance, ka fito a kurmance, babu ruwanka da aibobin cikinsa.

Ba ina wanke kaina bane a lokacin da nake isar da wannan saqon...kuma ba ina nufin ni bana kuskure bane.

Kawai dai nasiha ce nake aikawa zuwa garemu baki daya.

المسلم من سلم المسلمين من لسانه ويده.

HADISIN YAU NA (108) (KA KARE MUTUNCIN ƊAN'UWANKA) MANZON ALLAH (SAW) YACE:  DUK WANDA YA KARE MUTUNCIN ƊAN'UWANSA BA TA...
29/08/2022

HADISIN YAU NA (108)

(KA KARE MUTUNCIN ƊAN'UWANKA)

MANZON ALLAH (SAW) YACE: DUK WANDA YA KARE MUTUNCIN ƊAN'UWANSA BA TARE DA YA NA NAN BA, TOH, YA CANCANCI ALLAH YA ƳANTA SHI DAGA WUTA.

FA'IDA
WANNAN HADISI YANA KOYA MANA MAHIMMANCIN KULA DA KARE MUTUNCIN ƳAN'UWANMU IDAN MUKA GA ZA A CI MUTUNCIN SU, KO INA GULMARSU, KO ZA A YI MUSU SHARRI DA ƘAGE DA ƁATA MUSU SUNA HAKA SIDDAN.
DUK WANDA YA YI HAKA YA CANCANCI ALLAH TA'ALA CIKIN RAHMAR SA YA ƳANTA SHI DAGA SHIGA WUTA RANAR ALƘIYAMA.

ALLAH KA TSARE MU DA CIN MUTUNCIN ƳAN UWAMMU.

28/08/2022

SAKIN FUSKA DA MURMUSHI

MANZON RAHMA (SAW) YACE: "MURMUSHI GA ƊAN'UWANKA SADAƘA NE"

MU SAKI FUSKA MU YI FARA'A MU YI MURMUSHI, MU GAISA DA JUNA,
BA GABA
BA KIYYAYA,
BA HASSADA.
ZAI MU JI DAƊIN RAYUWA.

ALLAH YA YI MANA RAHMA DON SOYAYYAR MU GA ANNABIN RAHMA.
Sheik Aminu Ibrahim Daurawa

HADISIN YAU NA (107)MANZON ALLAH (SAW) YACE: "NASARA TANA TARE DA HAK'URISAMUN BUƊI SAI BAYAN DAMUWASAUƘI YANA ZUWA BAYA...
28/08/2022

HADISIN YAU NA (107)

MANZON ALLAH (SAW) YACE: "NASARA TANA TARE DA HAK'URI
SAMUN BUƊI SAI BAYAN DAMUWA
SAUƘI YANA ZUWA BAYAN TSANANI.

FA'IDA
WANNAN HADISI YANA KOYA MANA DABARUN ZAMAN DUNIYA, DA YADDA YA KAMATA MUTUM YA TSARAWA KANSA RAYUWA CIKIN NUTSUWA DA MAYAR DA KOMAI GA ALLAH TA'ALA.
NASARA ANA SAMUN TA IDAN AN YI HAK'URI AN JURE ANBI ƘAIDA ANYI AURE AIKI
SHIGA CIKIN DAMUWA DA TSANANI YA NA WUCEWA IDAN AN CI GABA DA ADDU'A
KOMAI TSAKANI SAUƘI YANA TAFE DA IZNIN ALLAH.

ALLAH YA BAMU LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA.

25/08/2022

"Babu wani turare da yake korar Shaiɗan, Shaiɗanu suna guduwa ne idan ana karanta Azkar".

Dr. Sani Umar R/Lemo

23/08/2022

"Yi ƙoƙari ka guji aikata duk wani abu da in ka yi shi mutanen kirki za su ce: wane bai kyauta ba"
-Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu (Hafizahul-Lah)

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ya ku taron talakawa! Shin ba na yi muku albishir ba? Lallai talakawa muminai za su shiga Alj...
20/08/2022

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ya ku taron talakawa! Shin ba na yi muku albishir ba? Lallai talakawa muminai za su shiga Aljannah kafin mawadata muminai su shiga da rabin wuni wato shekara ɗari biyar"

19/08/2022

Address

Aliero
Kebbi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdulbari Umar Hassan posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share