Kebbi news

Kebbi news Hausa news

Abu ga kaddara.😭😭Wannan shine 'posting' da Muktar yayi 'sharing' a page dinsa har aka k**ashi aka kaisa gidan g...
04/05/2025

Abu ga kaddara.😭😭

Wannan shine 'posting' da Muktar yayi 'sharing' a page dinsa har aka k**ashi aka kaisa gidan gyaran hali yau kwana biyu kenan ba'a sake shi ba. Ita kuma gidan jaridar ba'a daukar mata mataki ba saboda har yanzu rubutun na nan. Muktar nada iyali, yanada wadanda yake daukar dawainiyarsu a karkashinsa suke.

Saidai abun mamaki har yanzu babu wani mataki da aka daukar ma gidan Jaridar da tayi ainihin posting na cewa "Mai girma gwamnan Jahar Kebbi zaibar jam'iyyar APC". Ya k**ata a duba ma Muktar. Saboda munsan mai girma gwamnan Jahar Kebbi mai adalci ne. Wannan abun daya faru, da yawan jama'a na kallonsa a matsayin rashin adalci. Wanda duniya na nan tasa ido.

Saboda gidan jaridar da ta fara yin wannan posting ya k**ata a k**a ba wanda yayi sharing ba. Dukda shima bamu ce baida laifi ba.

Murjanutu Diri

Shata da RararaNi majiyi wakar Rarara ne sosai,har takai da Ina iya chankar kalmar da zai fada a gaba a cikin baitin sa....
04/05/2025

Shata da Rarara

Ni majiyi wakar Rarara ne sosai,har takai da Ina iya chankar kalmar da zai fada a gaba a cikin baitin sa.

Amma magana domin Allah hada Rarara da Shata ba abune Mai yiyuwa ba.

ibada dalilai fiye da ashirin

Shata karshe ne a waka,Amma duk wanda ke musu ya saurarin wakokin Shata ashirin kawai zai tabbatar da zance na.




Adamu Usman Aug

Gaskiya Mata Bakuda Tsoro Wallahi. 🤔Ko a Jikinta Har Wani Murmushi Take Fah.🤓😂Cewa CMRD Anas Rojo
04/05/2025

Gaskiya Mata Bakuda Tsoro Wallahi. 🤔
Ko a Jikinta Har Wani Murmushi Take Fah.🤓😂

Cewa CMRD Anas Rojo

MASU GARKUWA DA MUTANEN SUNKAI HARI JAHAR KEBBI HASBUNALLAHU WA NI'MA WAKEEL. Jama'ar Musulmi Mu taya Ƙauyen Gudale da A...
04/05/2025

MASU GARKUWA DA MUTANEN SUNKAI HARI JAHAR KEBBI

HASBUNALLAHU WA NI'MA WAKEEL.

Jama'ar Musulmi Mu taya Ƙauyen Gudale da Addu'a inda Cikin Daren Jiya Misalin Karfe biyu na dare Ne Masu Garkuwa da mutane s**a Shiga ƙauyen (BIRGIN GUDALE) Dake Cikin Jihar Kebbi a Karamar hukumar mulki ta Augie basu kashe kowa ba Amma an ɗauki ALHAJI AUDU NA GWANDU dake zama cikin wannan Garin na BIRGIN GUDALE.

MAHAMMAD TAJUDDDEN BUBUCE

Ubangiji Allah Subhanahu wata'ala Ya kawo Muna Sauƙin Wannan Masifa Ya kawo muna agajin Gaggawa.

Allah Ya Jarabçe Shi Da Țabin Hankali A Garin Da Ya Je Nema, Yanzu Haka Ana Cigiyar 'Yan UwansaYanzu haka yana garin Akw...
02/05/2025

Allah Ya Jarabçe Shi Da Țabin Hankali A Garin Da Ya Je Nema, Yanzu Haka Ana Cigiyar 'Yan Uwansa

Yanzu haka yana garin Akwanga dake jihar Nasarawa. Ya ce shi dan garin Unashine dake karamar hukumar Danko/Wasagu a masarautar Zuru a jihar Kebbi.

An turo mana da sakon ne dan a taya su cigiyar 'yan uwansa.

Dan Allah a taya mu yadawa (sharing) ko 'yan uwansa za su gani.

Ga lambar wadanda yake hannunsu za a iya tuntubar su dan neman karin bayani: 08024488015

Sojojin Amurka a Najeriya.Kowa yaga wannan shirmen but anyi shirui, Saboda soyayyar APC ko kuma tsoron kamu ko?Maganar S...
02/05/2025

Sojojin Amurka a Najeriya.

Kowa yaga wannan shirmen but anyi shirui, Saboda soyayyar APC ko kuma tsoron kamu ko?

Maganar Shugaban 'Kasar Nijar ta zama gaskiya.

Yanzu dai ga sojojin Amurkan nan sunzo.

YaaAllah duk mai kokarin jawo muna wadannan azzaluman cikin kasar mu, YaaAllah Ka fara hadashi da dukkan bala'in su.

YaaAllah Ka watse duk wani shiri da makirci da ake kokarin shirya muna, ta amfani da wawayen cikin mu, marasa imani da tunani.

Yahaya Abubakar

DA DUMI-DUMI: Shugaban kungiyar Êalibai ta Najeriya Comrade Isah Atiku ya ce Dan Shugaban Najeriya Seyi Tinubu ya sa an ...
02/05/2025

DA DUMI-DUMI: Shugaban kungiyar Êalibai ta Najeriya Comrade Isah Atiku ya ce Dan Shugaban Najeriya Seyi Tinubu ya sa an k**a shi anyi masa dukan tsiya sannan aka yi masa tsirara saboda kawai yaki amsar cin hancin Naira milyan 100 domin goyon bayan Gwamnatin Tinubu

Sannan Comrade ya ce an nemi tsige shi daga Shugabancin daliban na NANS kodayake dai Mista Seyi ya musanta zargin

Me zaku ce?

Rahoton jaridar A YAU

Muna rokon gwamnatin Jahar Kebbi data dubi girman Allah ta saki wannan bawan Allah Muktar da aka k**a a yau aka tura gid...
02/05/2025

Muna rokon gwamnatin Jahar Kebbi data dubi girman Allah ta saki wannan bawan Allah Muktar da aka k**a a yau aka tura gidan Yari. Laifin Muktar dayane, yayi 'sharing' na wani 'posting' wanda wata gidan jarida ta ruwaito na cewa " Gwamnan Jahar Kebbi zai bar jam'iyyar APC".

Sanadiyyar wannan 'posting' dinda wannan bawan Allah yayi 'sharing' a page dinsa, yau an k**ashi an gurfanar dashi kotu. Babu wani jayayya aka wuce da Muktar gidan Yari. Muktar ya fito ya bada hankuri na wannan posting dinda yayi, amma kuma ba'a duba masa ba, saida aka k**ashi aka gurfanar dashi kotu. Munsan Gwamnan Jahar Kebbi mai adalci ne, dan Allah Mai girma gwamnan Jahar Kebbi ka dubama wannan bawan Allah. Yanada iyali, yanada yan uwa.

Murjanutu Diri

CIKIN HOTUNA: Ku kalli yanda Gwabnan Jihar Kebbi Comrd Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya halarci taron ranar ma'aikata ta...
01/05/2025

CIKIN HOTUNA: Ku kalli yanda Gwabnan Jihar Kebbi Comrd Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya halarci taron ranar ma'aikata ta Duniya wanda yake gudana a filin wasa na Halliru Abdu dake cikin garin Birnin Kebbi.
Muna Addu'ar ALLAH yasa ayi taro lafiya a gama lafiya.

Imrana shehu filin sarki

Shugaban Ƙaramar Hukuman Mulkin Zuru LG, Muhammad Bala Isah Skudu, FCNA, FCCrF, Talban Zuru, Yaje Garin Tadurga Domin Ja...
30/04/2025

Shugaban Ƙaramar Hukuman Mulkin Zuru LG, Muhammad Bala Isah Skudu, FCNA, FCCrF, Talban Zuru, Yaje Garin Tadurga Domin Jajantama Al'ummar Garin Mai Ƙaho, Ya Kuma Basu Tallafin Abinci Da Sauran Kayan Masarufi, Wadan Da Yan Ta'adda S**a Shigo S**a Dauki Wasu Mutane Daga Cikin Su.

Shugaban ƙaramar hukuman mulkin zuru LG, Hon Bala Isah Gajere ya jajantama al'ummar garin tadurga waɗan da ƴan ta'adda s**a dauki wasu daga cikin mutanen su, inda hon bala isah gajere ya kai musu tallafin abinci da sauran kayan masarufi, kuma ya ƙara basu tabbacin gwamnatin jahar kebbi ƙarkashin jagorancin Cmrd Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu zata basu duk wata gudun mawa da yak**ata fannin tsaro in sha Allah.

Muna roƙon Allah ya ƙara bamu lafiya da zaman lafiya, amin.

Gobe Ta Allah Ce
By Tazan Junior
S,A Media To The Executive Chairman Zuru LG, Hon Bala Isah Gajere

Mataimaki na musamman ga Maigirma Ministan kasafin Kudi na Nigeria ya gwangwanje , mutanen masu lalura ta musamman da ab...
30/04/2025

Mataimaki na musamman ga Maigirma Ministan kasafin Kudi na Nigeria ya gwangwanje , mutanen masu lalura ta musamman da abababen hawa

Kai tsaye daga nan filin wasa na Haliru Abdu Stadium dake nan cikin garin Birnin Kebbi wurin taron rabawa masu lalura ta musanman kekunan guramu wanda BAGUDU BOYS s**a shirya tare da Hadin guiwar BEAUTIFUL GATE HANDICAPPED PEOPLE CENTER JOS

Bashar Aliyu Buhari ya dauki nauyi albarkacin mai girma Minista Sen. Abubakar Atiku Bagudu

Minista Matawalle Ya Yabawa Ma’aikatan Ma’aikatar Tsaro, Ya Sha Alwashin Baiwa Kowa Dama Yadda Ya DaceMinistan kasa a ma...
30/04/2025

Minista Matawalle Ya Yabawa Ma’aikatan Ma’aikatar Tsaro, Ya Sha Alwashin Baiwa Kowa Dama Yadda Ya Dace

Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya yaba da kwarewa da sadaukarwar ma’aikatan Ma’aikatar Tsaro, tare da sake jaddada kudirinsa na bin tsarin ba kowa dama yadda ya k**ata.

Bello Matawalle ya sanar da hakan a yayin wani taron tattaunawa da ya gudana a Abuja.

Yayin jawabin da ya gabatar a wajen taron da aka gudanar a ranar Talata a Ship House, Minista Matawalle ya bukaci manyan da kananan ma’aikata da su rika kawo korafe-korafensu kai tsaye gare shi, yana mai jaddada muhimmancin bude hanyoyin sadarwa a cikin ma’aikatar.

A wata sanarwa da Mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar, ministan ya yaba wa ma’aikatan da jajircewarsu wajen sauke nauyin da ke kansu. Haka kuma ya jinjina wa Babban Sakataren ma'aikatar Ambasada Gabriel Tanimu Aduda, bisa shirya wannan taro, inda ya bayyana shi a matsayin wata “damar kirki” ta musayar ra’ayi kai tsaye tsakanin shugabannin ma’aikatar da ma’aikatanta.

Yayin da yake bayyana tarihin rayuwarsa, Matawalle ya bayyana yadda ya fara aiki a matsayin karamin ma’aikaci a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Ƙasa har zuwa matsayin da yake kai yanzu, yana mai nuna fahimtarsa kan kalubalen da ma’aikata ke fuskanta. Ya bayyana fatarsa cewa irin wannan taro zai zama abin da za a rika gudanarwa akai-akai domin karfafa hadin kai da fahimtar juna.

Ganawar ta samu halartar babban sakataren ma'aikatar, daraktoci, mataimakan daraktoci, da manyan da kananan ma’aikatan ma'aikatar.

Address

Kebbi
Kebbi
0906765

Telephone

+2349067658418

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kebbi news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share