
20/06/2025
Yadda Zaka Zama Babban Mai Karatu: Matakai Goma Don Inganta Karatunka
(Mukullin Maƙala daga Dr. Sultan Al-Duwaiyfan)
1. Sauyin Gudun Karatu:
Gudun karatu yana bambanta bisa irin littafin da kake karantawa. Littattafan da s**a ƙunshi maqaloli ana iya karantawa da sauri, amma idan littafin yana da zurfin tunani ko ilimi, yana buƙatar ka karanta shi a hankali ko daidai. Ka tuna: muhimmanci ba wai gama littafi da sauri ba ne, amma fahimtar abin da ke ciki da amfani da shi.
2. Ka San Manufarka:
Dole ne ka san dalilin da yasa kake karatu. Shin domin nishaɗi ne ko don faɗaɗa iliminka da hangen nesanka? Wannan zai taimaka maka wajen zaɓar littattafan da zasu inganta rayuwarka da fahimtarka.
3. Kar Ka Karanta Duk Abin da Ka Gani:
Ba duk littafi, mujalla, ko imel ne kake buƙatar karantawa ba. Yawanci waɗannan abubuwan ba su da amfani sosai. Ka zabi abin da ya dace da kai, da burinka, da fannin da kake so ka ƙware a ciki.
4. Zabi Muhimman Sassa:
A cikin littafi, karanta sassan da s**a fi dacewa da abin da kake nema ko da kake son koya. Ka zama mai zaɓe wajen karatu, saboda tunaninka shine kayan aikin ka na rayuwa, da yanke shawara, da gina kanka.
5. Halin da Kake Ciki Muhimmi ne:
Lokacin da kake cikin natsuwa da annashuwa, zaka iya karanta littattafan da s**a fi ɗaukar hankali. Amma idan kana jin gajiya, ka karanta littattafan da s**a fi sauki. Wannan yana taimaka maka samun fa'ida ba tare da wahala ba.
6. Karanta Bisa Manufa:
Idan kana niyyar rubuta littafi, ko yin bincike, to ya kamata karatunka ya ta'allaka ne akan wannan batu. Yana da kyau ka sanya burin kirkirar sabbin ra’ayoyi ko hangen nesa daga abin da ka karanta.
7. Kada Ka Tsaya Karatu Sai da Dalili:
Idan ka fara karatu, kada ka dakata sai da wani dalili mai ƙarfi. Idan bayan karatu kana da tambayoyi, koma ka sake duba littafin ko ka bincika a wasu littattafan. Idan babu tambaya, to ka samu abin da kake buƙata.
8. Mayar da Hankali:
Ka tuna cewa kana da manufa a karatunka. Idan hankalinka ya rabu, ka ɗan ɗauki hutu ko ka canza littafi. Muhimmanci shi ne ka ci gaba da karatu a hanya mai amfani.
9. Inganta Muhallin Karatu:
Za ka karanta da fahimta sosai idan wuri yana da tsafta, shiru, kuma kana zaune cikin kwanciyar hankali. Wannan yana taimaka wa kwakwalwarka ta mai da hankali da jin daɗin karatu.
10. Karatu Ba Wani Hanya ce Ta Nishaɗi Kawai ba:
Wasu suna ɗaukar karatu a matsayin hobbynsu, amma gaskiyar ita ce karatu hanya ce ta rayuwa. Babban mai karatu ba ya faruwa cikin dare ɗaya. Sai da s**a yi aiki, s**a yi kuskure, s**a gyara, sannan s**a kai matsayi na girma.
A Taƙaice:
Idan kana son zama babban mai karatu, kana buƙatar fahimta, niyya, natsuwa, da yin aiki tukuru. Karatu wata hanya ce ta gina kai da bunƙasa rayuwa.
–Shikuma wannan hoton wani Magana ne daya burgeni shiyasa nayi amfani da hoton.