30/10/2025
CIKA ALKAWALI:
ANA GAB DA KAMMALA AIKIN MASALLACIN GARIN DAN DASHE CIKIN IKON ALLAH DAGA MAI GIRMA SARKIN KOKO.
Akwai wata babbar nasara da ta samu al'ummar Garin Dan Dashe, dake yankin Masarautar Koko, sakamakon cikar alkawalin Mai Girma Sarkin Koko, Alhaji Mohammed Bello Koko II. Wannan nasara ita ce ta kammala aikin ginin Babban Masallacin garin, wanda al'ummar s**a fara gina shi.
Wannan gagarumin aiki ya samo asali ne daga wata ziyarar ban girma da Hakimin Garin Dan Dashe tare da Al'ummar garin s**a kaiwa Mai Girma Sarkin Koko, Alh. Mohammed Bello Koko II, a fadar sa mai daraja.
Babban makasudin ziyarar shine, g*i suwar bangirma da isar da korafin neman taimako ga Mai Girma Sarki don ya sanya hannu a kammala musu aikin wannan Masallacin da s**a fara gudanar da gininsa.
Mai Girma Sarkin Koko, Alh. Mohammed Bello Koko II, ya karɓi baƙuncin nasu cikin girmamawa da fara'a. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya yi musu alkawalin cika burin su na kammala aikin ginin wannan Sabon Masallaci, wanda al'ummar Garin Dan Dashe s**a yi fatan a kammala musu shi.
✅Cikin ikon Allah (SWT) da kuma gagarumin ƙoƙari na Sarki, Mai Girma Sarkin Koko ya cika alkawalin da ya ɗaukarwa al'ummar Garin Dan Dashe. A halin yanzu, ana gab da kammala aikin ginin wannan babban Masallaci karkashin kulawar Gidauniyar Sarkin Koko Malam Musa Foundation. Wannan Masallaci zai zama wuri mai tsarki don bautar Allah da haɗa kan al'ummar garin Dan Dashe.
Hakika, samun Mai Girma Sarkin Koko, Alh. Mohammed Bello Koko II, a matsayin Sarkin Koko, wata babbar nasara ce da Allah (SWT) ya yiwa yankin Masarautar Koko baki ɗaya. Muna roƙon Allah (SWT) ya ƙara masa jagora, da kuma taimakon sa a dukkan al'amuransa. Amin.
Muna kuma roƙon Allah (SWT) ya ƙara taimakon Mai Girma Gwamnan Jahar Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu, bisa ga jajircewar sa wajen kawo manyan ci gaba a faɗin Jahar Kebbi. Amin.
Ciroman Koko Media Team
30/10/2025